Hira da Abubakar (Bunari), Wan Balaraba, kan abubuwan da ta yi kafin rasuwarta
Wasu mutane a Kano sun ce idan har Balaraba ta bari aka daura mata auren nan, to sai buzunta!
ABUBAKAR MOHAMMED (wanda aka fi sani da Bunari) shi ne yayan Balaraba wanda take bi mawa wajen haihuwa, shi kuma yana bi wa marigayi Abubakar da marigayiya Jummai. Dan shekara 22 da haihuwa, a da shi ne zai bi motar su Balaraba zuwa Kano, amma abin ikon Allah sai yayansa Riskuwa ya riga shi ya hau aka tafi. Wayyo! A yau shi ne babba a gidan, wato ya tashi daga matsayin da na uku zuwa na daya.
A hirar da ya yi da Fim kwana biyu bayan an yi rashin, ya bayyana wasu al'amura wadanda mahaifinsu ma ya gaya wa wakilinmu su kwana daya bayan mutuwar. Daga cikin wadannan abubuwa har da kalaman da Balaraba ta rika furtawa awowi kadan kafin ta rasu, da wasu al'amura da suka faru tun kafin ranar daurin auren. Misali, ya bayyana (kamar yadda ubansu Malam Muhammadu ya shaida mana baki da baki) cewa akwai wasu mutane uku da suka tarbi Balaraba a Kano, suka ce mata idan har ta bari aka daura auren, to ba za ta kai labari ba. Wannan barazanar ta tsoratar da Balaraba har ta tashi a ranar daurin auren tana neman kada a daura auren.
An ce waka dai a bakin mai ita ta fi dadi, don haka ga Abubakar da bayanin abubuwan da ya iya tunowa sun faru a wannan mawuyacin yanayi:
Fim: Malam Abubakar, muna maka ta'aziyyar wannan babban rashi. Kuma za mu so mu ji abin da za ka ce dangane da wannan rashin namu baki daya.
ABUBAKAR: E to, ni dai addu'a ce zan ma kanwata Balaraba, saboda wannan babban abin juyayi ne a gare mu m u 'yan'uwanta, yadda Allah ya amshi abinsa. Kuma abin farin ciki ne a gare mu kasancewar kafin ta tashi tafiyar nan sai da mu 'yan'uwanta tare da iyayen namu baki daya ta zo ta roke mu gafara, kuma muka yafe mata. Sannan ta je ta shiga wannan mota har suka je suka yi hadari suka rasu. Muna masu fata ita da yar tamu Jummai da kanen mijinta (direban motar) da Isyaku wanda kane ne a wajenmu, Allah ya jefa su a gidan Aljanna.
Za ka iya tuna magana ta karshe ko wani al'amari na karshe da ka yi da ita a ranar kafin tafiyarsu?
ABUBAKAR: A daren da za su tafi tare muka kwana da ita muna hira har sai da aka yi kiran sallar asubahi sannan muka rabu da ita ta je ta kwanta. Bayan nan sai ta gaya mani cewa a kujerar motar da za su tafi ni zan zauna gaba, in kuwa ba haka ba to ba za ta tafi ba. Allah cikin ikonsa a lokacin da za su yi tafiyar sai aka neme ni ba a gan ni ba, sai babban yayanmu Abdullahi Mohammed (Riskuwa) ya zama makwafina, suka tafi.
Shin akwai wasu alamomin da ta nuna akan abin da ya faru gabanin faruwarsa?
Abubakar: E. A lokacin da Balaraba ta dawo daga Kano a ranar Laraba cikin shirye-shiryen bikin, ta same mu tana gaya mana cewa an tare ta a Kano an ce duk tsiyarta in ta bari aka daura auren nan, karkarinta a duniya ta yi kwana uku. Ta gaya mana wannan magana zahiri.
Ta gaya maku mutanen da suka tare ta din? Tsofafi ne ko matasa, maza ko kuma mata?
Abubakar: A zahirin gaskiya ba ta gaya mana ko su wanene ba, kuma ba ta yi mana kwatancen kowa ba, amma ta gaya mana.
Lokacin ta gaya maku, akwai wani mataki da kuka dauka?
Abubakar: Ka san komai nufin Allah ne. Da, da ita da mahaifiyarmu sun ce a daga bikin, sai mahaifin namu ya ce yadda ya sanar wa jama'a, duk duniya sun ji, abin kunya ne a ce don za a daura wa Balaraba aure wasu sun ce za ta rasa ranta, wannan ba wani abu ba ne tunda hanyar sunna ce. Shi ya sa ya matsa aka daura auren. Amma bayan an daura auren sai ya ce a bari sai bayan sati biyu a dauke ta su tafi. Shi ne sai mijin nata Shu'aibu ya zo ya roke shi a kan su bar ta ta je Gala kawai za a yi kafin ranar tarewar. Shi ne sai suka zo daga ita har yayar tamu suka roke mu gafara, muka gafarta masu.
To a yanzu kuna da sha'awa ko tunanin ku dauki wani mataki dangane da wannan magana da ta auku?
Abubakar: E, to, tunaninmu dai mun san cewa Balaraba dai ta cika ne ta hanyar biyayya ga sunnar Manzo (S.A.W.). Saboda haka duk wanda ma ya yi wani abu, Allah ya yi shi kuma ya yi Balaraba, Allah zai nuna masa irin nasa sakamakon.
Kafin daurin auren iyayenku da sauran danginku kun yi wani taro musamman kan wannan magana?
Abubakar: Kwarai da gaske, mun zauna. Don a lokacin da ta zo tana hira sai muka ba ta hakuri muka ce don makiya tana da su. Mun zauna mun tattauna muka ga dai kawai a daura mata auren.
A ranar daurin auren ba ta nuna rashin amincewarta na daura auren ba?
Abubakar: A'a, ai tunda mahaifinmu ya ce za a dauran, har aka gama bikin ba wani abu da ta nuna na rashin amincewarta. Ai gaba dayanmu kowa cikin farin ciki, ba ma wanda ya saka tunanin an ma fadi wannan magana.
Shin kun tuntubi shi Shu'aibu kan wannan magana, ko shi ya zo ya yi maku wata maganar gabanin daurin auren?
Abubakar: A gaskiya shi Shu'aibu ban sani ba ko ya yi magana da iyayenmu kan wannan al'amari, amma ni ba mu yi da shi ba.
Za ka iya tuna kalmar karshe tsakaninka da ita?
Abubakar: Zan iya tunawa, a lokacin da ta tashi za su tafi, sai na ce mata, "Balaraba za ki tafi kenan?" Sai ta ce e za su tafi, saboda haka sai na zo nan Kano. Sai na ce mata to shikenan sai na zo.
Akwai wata magana ta karshe da ka ji ta furta tsakanin ta da iyayenku?
Abubakar: A zahirin gaskiya ban ji maganar da suka yi ba, saboda lokacin ana ta hidimar biki kuma ka san ni ba zan shiga cikinsu a kowane lokaci ba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin