'Yan 'Nigerian films' sun hau turbar shirya fim na batsa muraran!
Daga IRO MAMMAN,
a Kaduna
ALLAH wadan naka ya lalace! Haka Hausawa ke cewa idan sun ga wani abin assha. To, haka wakilinmu ya gani kwanan nan a fagen shirya finafinai na Kudu (wadanda ake kira Nigerian Films). Wata sara ce ta shigo harkar finafinan Kudu din a cikin 'yan watannin baya, kuma abin yana ta karuwa. Wannan ko shi ne shirya finafinai masu nuna tsiraicin mata. Tun ana yi da tsoro-tsoro, har yanzu abin ya zama gasa a tsakanin 'yan wasa, furodusoshi da daraktoci.
Wannan mugun al'amari yana ta kara kazanta ne saboda su kansu shugabannin shirya finafinan su ne suke aikata shi, tare da hadin kan manyan 'yan wasan Kudu. Da yake an fi damuwa da tsiraicin mata, shahararrun 'yan wasa mata su ne kan gaba wajen nuna tsiraici. Sun hada da Cossy Orjiakor, Shan George, Eucharia Anunobi, Barbara Odoh, Sandra Achums, Omolade Ekeinde, da Bimbo Akintola. Kowacensu takan nuna wani sashe na jikinta. Bakin yawan nuno tsiraici kwatankwacin tashen da 'yar wasa za ta yi a shirin fim. A yanzu, babu kamar jarumar shirin nan mai suna Outkast, wato Shan George, wajen aikata wannan ta'asar.
Wata mujalla da ake bugawa a Legas ta yi nazarin al'amarin, ta ce babban dalilin da ya haifar da gasar nuna tsiraicin shi ne wai saboda kasuwancin mutum ya dore a halin matsin da aka shiga yanzu, inda masu sayen fim suka ragu. Da ma can ana kuka da finafinan kan yadda suka ta'allaka bisa nuna bori, da tsafi, da zubar da jini, da sihiri, da sauransu. Yanzu ta kai wasu na cewa ba su iya kallon fim din Kudu a gaban 'ya'yansu, sa'annan suna tsoron abin da 'ya'yansu ke kallo idan su ba su nan. A cewar mamallakin gidan talbijin na DITV da ke Kaduna, Alhaji Khalifa Baba-Ahmed, "Yawancin finafinan ba su dace a nuna su ga jama'a ba. Su ma masu saye don su kalla a gida, ya dace su nuna wa 'ya'yansu abin da ya dace su kalla."
Wani bincike ya tabbatar da cewa idan aka tafi a haka, to babu shakka nan ba da dadewa ba furodusoshi 'yan Nijeriya za su fara shirya finafinan batsa muraran (blue films) suna sayarwa a kasuwanninmu. Binciken, wanda mujallar Fim ta yi, ya gano cewa har ma an shirya wani fim na batsa ana sayarwa a asirce (an kai wani wakilinmu wani gida a Kaduna inda aka sa masa fim din ya kalla don tabbatarwa bayan ya furta shakku kan labarin da aka fara ba shi). Wannan tunanin ya zama daidai idan aka yi la'akari da kalamai da halayyar wasu daga cikin masu shirya finafinan na Kudu. Kwanan baya, gidan talbijin din nan mai zaman kansa da ke Legas, A.I.T., ya yi hira da wasu gaggan 'yan fim na Kudu, inda suka bayyana cewa a bayyane suke su yi fim din tsiraici idan har za a biya su da tsoka. An yi hirar a shirin "Showbiz Café" wanda Moji Damisa-Jemegbe ke gabatarwa.
A shirin, hatsabibiyar 'yar wasan nan wadda ta fi kowace mace bayyana tsiraicinta a fim, Shan George, ta ba da amsa ga Moji Damisa-Jemegbe kan wata tambaya da ta yi mata a kan ko za ta iya yin wasa a 'blue film.' Cewa ta yi, "If the pay is good, I don't mind starring in an x-rated film," wato "Idan za a biya ni kudi da tsoka, to ba zan damu ba in yi wasa a fim na tsiraici tsantsa," wato inda za a rika nuno tabarya a turmi.
Da yake shirin gidan talbijin din ana yinsa mako-mako ne a kan 'yan fim da sauran nau'o'in masu sana'ar nishadantarwa kamar makada da mawaka, a mako na gaba an yi hira da daya takadarar 'yar wasan, wato shahararriyar 'yar wasa Sandra Achums. Ita ma ta furta kalamai irin na Shan George din, cewa za ta iya yin wasan tsiraici idan aka biya ta da kyau. Har ma ta yi suka a kan masu yin Allah-wadai da ita da Shan George a kan fim din Outkast wanda suka yi. Ta ce maimakon a zage ta, kamata ya yi mutane su yaba mata saboda karfin halin da ta nuna na yin irin wannan fim din.
Fim din Outkast yana daga cikin finafinan da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta hana sayar da shi a Jihar Kano.
Abin da ke damun masu lura da harkokin finafinan Kudu shi ne yadda masu shirya finafinan suka samu daurin gindi daga iyalansu da masu kallonsu. Misali, shahararriyar 'yar wasan nan Omolade Ekeinde ta samu goyon baya daga wurin mijinta Kyaftin Ekeinde ta yi wasa a fim din nan mai suna Prostitute, inda ta fito a matsayin karuwa. A cewar mijin, shi bai ga wani laifi a wasan da ta yi ba, sai ma gwada basira da ta yi a sana'arta.
Kyaftin Ekeinde yana magana ne a wata hira da aka yi da shi a wani shiri na gidan talbijin na A.I.T. mai suna "The Pillar." Ya ce sai da suka tattauna da matarsa a kan fim din kuma shi ne ya ba ta izinin ta yi wasa irin wannan. Har ma ya ce hoton da matarsa ta sa a fostar fim din wanda ke nuna tsiraicinta muraran yana burge shi matuka. Hasali ma, "Idan ka shiga dakin kwananmu, za ka ga na kafa hoton a bango saboda yana matukar jan hankalina da tayar mini da hankali," inji shi.
Mazaje 'yan Kudu da dama suna son 'yar wasa Cossy Orjiakor, wadda ta fi kowace 'yar wasa nuna tsiraici (Ba mu iya buga hotonta cikin wannan mujallar don ku gan ta, domin kuwa a timbir take!); ta yi kaurin suna wajen bayyana manya-manyan mamunanta a fim da kuma a fosta. Mata ne kadai suke yin tir da nuna tsiraicinta da take yi, suka ce tana zubar wa da mata mutunci.
Ita ko Cossy, kememe ta yi, tana cewa in dai ganin tsiraicinta ne ake kuka da shi, to kadan ma aka gani. Ga wasu kalamai na tsiwa da ta furta kwanan baya a mujallu:
1. "Yanzu fa ba kayana gaba daya na cire ba. To ya zuwa lokacin da zan tube zindir, zan ga abin da mutane za su ce."
2. "A gaskiya, ba na son komai wurin namiji a yanzu. Lokacin da zan so namiji kila sai na zo son samun jariri nau na kaina, daga nan zan dauki kwangilar namiji na wani dan lokaci kadan (don ya biya min bukatar hakan). Da zaran na sami ciki, zan kori namijin in ci gaba da rayuwata ni kadai in je in haihu."
3. "Ba ruwan kowa da tsiraicin da nake nunawa. Idan mutum ya damu to ya je, ko ta je, ta buga kanta a bango, daga nan ta sha Panadol."
4. "Ni ba mhaukaciya ba ce. Ina da manyan mamuna masu kyan gani kuma zan nuna abina domin duk wanda ke so ya kalla."
5. "Ba na yin zina da kowa yanzu. Tunda ba ni da saurayi, don me zan yi tunanin yin jima'i?"
6. "Duk abin da nake yi yanzu, ina bauta wa Allah. Ina yin addu'o'i kuma ina ganin sakamako mai kyau daga addu'o'ina."
Kada ka dauka cewa ashewo ne suka rikide suka zama 'yan fim. Kusan kowace ta yi karatun zamani mai zurfi. Ita dai Cossy Orjiakor, tana da digiri wanda ta samu daga Jami'ar Nijeriya ta Nsukka a 'yan shekarun baya. Shedanar da take yi ta sa 'yan mujallun finafinan Kudu da furodusoshi da daraktocin finafinai suna yi mata caa, kowa yana son ta tube gabanta ya nuna wa jama'. Ya zuwa yanzu, an buga hotonta tsirara a bangon akalla mujallu takwas na Kudu. A cikin 'yan kwanakin nan, furodusoshin finafinan kade-kade suna farautarta saboda wata rawar shedana da ta yi a fim din rawa na Obesere.
An yi la'akari da cewa akwai wani nau'i na yaudara ma a harkar. A kokarinsu na cin ribar kasuwa sosai, masu shirya finafinan sukan yaudari jama'a wajen nuna mata cikin tsiraici a jikin hoton fosta ko kwalin fim, amma idan mutum ya saya sai ya ga cewa abin da ke jikin hoton babu shi sosai a fim din. Sun lura cewa akwai shedanun masu kallon fim wadanda kan sayi fim don kurum su ga tsiraici a ciki; buga hoton mace tsirara zai iya kwadaita wa mai saye cewa akwai tsiraicin sosai a ciki.
An ba da misali da fim din Outkast. Fostar wannan fim dai tana dauke da hoton takadara Shan George. A fostar, an nuna hantsar ta Shan George sosai; tana sanye da karamin kamfai wanda bai boye ko da gashin al'aurarta ba.
"Da yake Shan George kyakkyawar mace ce mai sifa mai jan hankali, mazajen Nijeriya da dama sun kasa kin sayen fim din na Outkast, don kurum su ga tsiraicinta a fim din," inji mujallar.
Amma a fim din babu wurin da aka nuno tsiraicin da aka nuna a fostar. Duk da yake akwai an nuna wurare da yawa inda Shan take aikata zina da wasu mazaje, babu inda nonuwanta da cinyoyinta suka fito karara kamar yadda akwa kwadaita a fostar fim din. Wannan, inji mujallar, '419' ne aka yi wa mazaje, wato damfara.
Wani fim din mai nuna tsiraici, wanda a shi din ma an yi damfara, shi ne Prostitute, wanda ke ba da labarin jaruma Omolade Ekeinde a matsayin karuwa. Fostar fim din tana dauke da hoton Omolade ta daura wani guntun zane wanda ya fito da al'aurarta sosai. Hannayenta da kafadunta a bude suke, haka kuma saman mamunanta.
Wannan fostar ta tayar da muhawara a fagen shirin fim na Kudu, wanda ya tattaru a unguwar Idumota ta Legas, da kuma garin Anacha, musamman ganin cewa ita wannan 'yar wasan tana da miji har da 'ya'ya uku. Fostar ta sa maza da yawa sun sayi fim din don su ga tsiraicin na Omolade, amma a karshe sai suka ga ashe duk yaudara ce. A fim din, babu inda aka nuno ta tana rungume-rungume, ballantana jima'i. Wuraren da aka yi rungume-rungume din babu ita a ciki. Daraktan fim din ya yi amfani da wata macen daban wadda suka yi kama da Omolade, ta yi wasan tsiraicin da ake so ita Omolade din ta yi. Amma duk wanda ya kalli fim din zai gane cewa ba Omolade ba ce, domin ita waccan ta fi ta baki.
Yaudarar ba ta tsaya ga yi wa masu kallo ba; hatta gwamnati masu shirya finafinan sukan yaudare ta a kan abin da suka shirya. Yadda suke yi shi ne idan Hkumar Tace Finafinai ta umurce su su cire wani bangare na fim wanda ya saba wa doka, sai kawai su manta da ita, su fitar da abinsu yadda suke so. Kwanan nan sai da Hukumar Tace Finafinai ta Kasa (NFVCB) ta sa 'yan sanda a Legas suka kai farmaki ga wasu kamfanoni biyu da ke shirya finafinan batsa. Kamfanonin su ne 'Don Shama Production' saboda sun shirya fim din Shattered Homes, da kamfanin 'Total Experience' tare da na 'Grand Touch Pictures' saboda fim dinsu mai suna Night Out (Girls On Sale). A cewar jami'in yada labarai na hukumar tace finafinan, Mista Ferdinand Abua, ya zama dole a sa ''yan sanda su yi kamun domin su wadannan furodusoshin sun saba wa dokar kasa da ta hana nuna tsiraici a fim, kuma an gargade su kafin su saki finafinan.
Ya kara da cewa hukumar ba ta bai wa furodusoshin shirin Shattered Homes izini ba suka yi gaban kansu kurum suka saki finafinan a kasuwa. Furodusoshin sun sanya hatimin hukumar na jabu a jikin kwalin kaset dinsu bayan an fada masu su je su cire wuraren da hukuma ba ta amince da su ba a finafinan kafin a ba su takardar izini.
A kan shirin Night Out, an hana shi izinin fitowa ne domin akwai kurakurai a cikinsa, amma sai masu fim din suka finjire kawai suka fara sayar da fim din bayan sun makala masa hati,min karya. Mujallar Fim ta gano cewa furodusoshi da dama suna aikata wannan laifin, cikinsu har da masu shirya finafinan Hausa.
"Shin har ina furodusoshin finafinan Kudu za su kai wajen aikata wannan yaudarar? Wannan babbar tambaya ce da ta mamaye zukatan yawancin mutane masu nazarin harkar fim." Haka wani ya tambaya.
Hukumar Tace Finafinai ta Kasa ta bayyana damuwa matuka a kan yadda ake ta samun karuwar matasa mata da ke fitowa kusan tsirara a finafinai, duk da yake sun san cewa hukumar ba ta amince da nuna tsiraici da sauran nau'o'i na ashariya ba. Jami'in yada labaran ya yi kira ga duk wani mai hannu a shirin fim ya sani cewa babban laifi ne mutum ya sayar da ko ya nuna finafinai marasa izinin hukuma, sa'annan ya shawarci dillalan kaset su rika tabbatar da cewa fim yana da izini kafin su sayar da shi.
Wani furodusa ya bayyana damuwa matuka a kan wannan al'amarin, inda ya ce lokaci ya yi da za a hana ci gaba da wannan mugunyar al'ada. "A ganina, duk laifin na Hukumar Tace Finafinai ta Kasa ce da ke Abuja, domin su ne suke kallon fim su ba shi satifiket din amincewa kafin ya fito. Me zai hana su sa baki?"
Akwai damuwa kan cewa wannan bakar al'ada za ta iya shafar sauran bangarorin kasa. Ko dai wani hatsabibin furodusa na Hausa ya shirya fim mai bayyana tsiraici, ko kuma wata 'yar wasan Hausa ta je Legas ta yi fim din don a ba ta makudan kudi. Wannan tsoron ne ya sa Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano ta tashi tsaye wajen magance shigowar finafinai irin su Outkast da Prostitute a kasar Hausa. To amma duk da yake an hana shigarsu Kano, har yanzu a boye ana sai da su a Sabon Gari da sauran wurare, ballantana uwa-uba sauran jihohin Arewa. "Tilas ne a tashi tsaye a yi maganin wannan abu tun kafin ya kai makura ko kuma ya kwace a kasa tarbo shi," a cewar wani fitaccen dan kasuwa a Kaduna.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin