Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 30   Yuni 2002


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rayuwarmu
Duk Sun Yi Aure
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 



Dalilin da ya sa muka kafa Gidauniyar Balaraba
Inji Ishaq Sidi Ishaq

KWANAN nan wani gungun masu harkar shirya finafinan Hausa suka taru suka kafa kwamiti domin tunawa da jarumar 'yan fim din nan wadda Allah ya yi wa rasuwa a hadarin mota kwana daya bayan an daura mata aure, wato Balaraba Mohammed. Mun ji cewa nan ba da dadewa ba za a yi gagarumin taron kaddamar da Gidauniyar Tunawa da Balaraba inda ake sa ran tara kudi ko wani taimako don bai wa magadan marigayiyar. Shugaban kwamitin shi ne shahararren dan wasan nan kuma darakta, ISHAQ SIDI ISHAQ.

Ba sai an nanata ba, rasuwar Balaraba ta gigita jama'a a cikin kasar nan da waje, ta jawo matukar tausayawa daga gare su tare da kara fahimtar karfin ikon Ubangiji (SWT).

Wadanda suka kafa wannan kwamitin ba wasu ba ne illa mutanen da suka yi aiki tare da marigayiyar. Kamar yadda shugaban kwamitin ya fada, manufarsu ita ce su nuna cewa 'yan fim su rika agaza wa junansu a duk lokacin da wani ya shiga wani mawuyacin yanayi.

A cikin wannan hirar da Ishaq ya yi da wakilinmu a Kano, ya bayyana manufar kwamitin, da ra'ayoyinsa kan yadda yake ganin ya dace 'yan fim su tashi tsaye wajen karrama kansu da kansu, ba sai wani ya ce masu su tashi su yi abu kaza ba. Bismilla: FIM: Za mu so jin manufar kafa wannan gidauniya mai suna Gidauniyar Tunawa da Balaraba.

Ishaq Sidi Ishaq
Ishaq Sidi Ishaq, Shugaban Gidauniyar Tunawa da Balaraba
ISHAQ: Manufar wannan gidauniya ba zai wuce karrama ta da muke so mu yi ba. Ba wai kawai ita kadai ba, muna fatan abin ya dore; yanzu duk wani dan fim da wani abu ya same shi, sai a bi irin wannan hanya ko wata don a tallafa masa ko iyalan da ya bari idan mutawa ya yi .

FIM: Me kuke son tarawa?

ISHAQ: Akwai taimako da muke so mutane su bayar da za a harhada domin a bai wa su magadan marigayiyar. Muna ganin idan mun yi haka karramata muka yi; kuma bayan karramawa, yana nuna cewa Balaraba a koda yaushe tana cikin zuciyarmu. Akwai mutane da yawa suna neman kyaras ta yaya za su ba da tasu gudunmawar ta hanyar wannan gagarumin abu da muke son yi, sun rasa yaddaza su yi. Akwai masu bugo waya suna son su bayar da nasu agajin, da masu zuwa da kafa suna tambaya.

Mutuwa dai tana kan kowa. Idan misali mun ce da mutum ya mutu mun manta da shi, to a gaskiya ba ma kyautata wa junanmu. Akwai abubuwa da yawa da ya kamata 'yan fim su yi su kyautata wa junansu. Mu muna ganin tunda mutuwar Balaraba din nan ba wanda ba ta taba ba, wannan abin ya yi mana kaimi, muka ce mu fara daga kanta.

Gaskiya kuma, in dai kamar yadda na fada ba zamu so kanmu ba, fisabilillahi mu masu harkar fim akwai abubuwa da yawa da ke tasowa amma ba ma sa hannu a ciki. Ina ka taba jin an ce yau ga shi ana gina wani masallaci 'yan fim sun je sun ba da tasu gudunmawa?

FIM: Wasu na korafin cewa ai can baya wasu 'yan fim sun mutu, to me ya sa ba za ku yi masu gidauniya ba ko ku hada su cikin wannan?

ISHAQ: Kamar yadda nake son fadi ni dai ba zan manta ba idan wasu sun manta, gaskiya an taba yin haka. Lokacin da abokinmu, dan'uwanmu Aminu Hassan Yakasai ya rasu, ka san yana daya daga cikin daraktoci manya, da Allah ya karbi ransa an yi masa irin wannan gidauniyar. Ban san dai takamaiman abin da aka tara ba, an dai tara kudi kusan N7,000 da wani abu. Ka ga kenan ba za a ce ba a taba yin irin wannan ba, an yi abin nan kuma ba mamaki iyalinsu aka taimaka mawa da su.

Mu muna ganin yanzu da Balaraba ta rasu ya kamata a ce an dada yin irin wanda aka yi wa su Aminu Hassan. In ka duba ka ga akwai iyayenmu a wannan harkar, kamar Allah ya jikan rai Doron Mage, lokacin da ya rasu ba na jin an yi wani abu. Haka lokacin da U.S.A. Galadima ya rasu. Sai muka ce bai kamata irin wannan na faruwa ba, mu zauna shiru sam ba ma motsi. Ka ga Danhaki yana bukatar taimako, akwai lokacin da yake cikin matsala ta ciwon idonsa. Saboda haka ya kamata ko menene zai taso a daina bari abin yana yin nisa. Lokacin da abin yake da zafi sai mu nuna damuwarmu a kan al'amarin, mu yi tunanin abin da za mu yi.

FIM: Wasu cewa suke ai wannan aiki da kuka dora wa kanku ba naku ba ne, aikin kungiyoyin masu shirin fim ne.

ISHAQ: To a kan wannan gaskiya idan aka ce za a biye irin wannan gutsuri-tsoma, ba inda za a je domin domin, kamar yadda na fada, mu din nan mu muka sa kanmu. Ka ga kamar ni, ni ne Sakataren Kungiyan Daraktoci sa'annan memba ne ni a Kungiyar Kurodusoshi, haka ni dan Kungiyar 'Yan Wasa ne, ni ba wata kungiya nake wakilta ba cikin Kwamitin Gidauniyar Tunawa da Balaraba, duk abin da aka yi, abin da za a ce shi ne 'yan fim ne suka yi. Mu ne muka yi tunanin fito da wannan hanya ta taimakon juna.

FIM: Wasu kuma cewa suke yi addu'a ce kawai ta kamata a yi mata.

ISHAQ: Abin da na sani shi ne duk duniya ba inda ba a yin haka. Idan ana tsayawa kan irin wannan finafinan, to misali wadanda Balaraba ta yi wa finafinai da ba su fito ba, to sai su ma su fasa fito da fim din tun da ta mutu? Ai za a yi shekaru kusan talatin ana moran fim dinta; ka gane abin da nake nufi? Ba Balaraba kadai ba, duk mutumin da ya mutu aka yi wa iyayensa irin wannan wallahi ba za su taba mantawa da mu 'yan fim ba, kuma ba za a rika yin tababar shigar mata a fim din ba. To duk abin da za a yi na alheri bai kamata wasu su fito su ce kaza da kaza ba. Mu dai mun kudiri niyyar za mu yi abin nan kuma Allah ya ga zuciyarmu.

FIM: Wane kira za ka yi wa 'yan fim da sauran jama'a kan wannan gidauniya?

ISHAQ: Kiran da zan yi ga mutanenmu da kuma 'yan kallonmu masoyanmu shi ne, muna neman hadin kai da goyon baya kuma su ba da tasu gudunmawar. Mu fito mu rika taimaka wa junanmu ga aure ko suna ko kan iyalan wanda ya rasu.

FIM: Wannan kwamiti wa ya dauki nauyinsa? Domin tilas sai an kashe kudade kafin ya kai ga cin nasara.

ISHAQ: Babu wani mai daukar nauyi domin mu muka sa kanmu, taimako muke bayarwa. Mu ke kashe kudaden zirga-zirgarmu da buga takardu da sauransu. Kowa da aljihunsa yake yi, domin mu muka sa kanmu.

FIM: A karshe daga kan Balaraba kun gama aikinku sai ku rushe kanku ko za ku zama kwamitin dindindin?

ISHAQ: To mu dai kaimi shi ne na Balaraba da ya taso, amma nan gaba wasu kungiyoyi ko gungun mutane idan irin haka ta faru sai su yi tunanin su ma su yi irin wannan. Amma ba mun kafa wannan kwamiti ya zama na dindindin ba. Wannan abu ne da muke ganin ya shafe mu shi ya sa muke son mu fara daga kan Allah-jikan-rai Balaraba Mohammed.

'Mutuwar Balaraba ta rikita ni'

ALLAHU Akbar! Allahu Akbar! Na girgiza, na rikice, hankalina yai matukar tashi, yadda har nai shakku da sahihancin labarin da na samu da Magariba, bayan na dawo daga wajen galar da aka shirya don taya su murnar auren, cewa wai BALARABA TAI HADARI HAR TA RASU!"

Haka furodusan fim din Kacibus kashi na 1 da na 2, Malam Ado Kullun-Kullun, ya fada wa mujallar Fim a cikin gigita, lokacin da yake juyayin rasuwar 'yar wasa Balaraba Mohammed wadda Allah ya yi wa rasuwa kwana daya bayan an daura mata aure da jarumi Shu'aibu Lawan (Kumurci).

Ado ya ci gaba da bayyana yadda bakin al'amarin ya riske shi, yana cewa, "Allahu Akbar! take sai na rinka hango hoton da muka yi da ita a location fim din Kacibus 2. Sai na tuno hirar da muka yi da ita ta karshe a ranar Talata da yamma dududu bai fi saura awowi dari ta bar duniya ba, take cewa da ni, 'Ba ni da wani buri da ya wace in an yi bikinmu ranar Litinin in kwanta a dakin mijina in huta, domin duk jikina a gajiye yake saboda wannan zirga-zigar.' Sai na ce, 'Ai duk gajiyar da kika yi Balaraba hutun kwana uku kacal ya wadatar da ke daga duk wata gajiya'. Muka yi ta hira a mota a kan hanyarmu ta dawowa daga location din na Kacibus 2. Allah Akbar! Kana taka Allah na tasa!"

Da Fim ta tambaye shi game da halayen marigayiyar, sai furodusan ya ce, "Balaraba tana da matukar kirki, sannan tana da cika alkawari, domin in aka sa lokacin fita location tana kusan riga kowa fara zuwa. Kuma mun yi zaman lafiya da ita har muka gama Kacibus 1&2 ba mu samu wata gagarumar matsala da ita ba." Ya kara da cewa, "Babban abin da ya fi burge ni da ita shi ne in tana hulda da mutane ba za ta taba bambancewa tsakanin mai shi da mara shi ba."

Daga karshe Ado Kullun-Kullun ya ce, "Ina mika ta'aziyyata ga mijinta Shu'aibu Lawan, iyayenta, 'yan'uwanta da tsohon shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Auwalu I. Marshal, da sabon shugaban, Ibrahim Mandawari, da kuma sauran 'yan wasa maza da mata da duk al'ummar Musulmi".

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin