|
Duniyata ba ta gigita ba -Halima Adamu
Amarya Halima Adamu tana ba Angonta kosan soyayya
|
Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA a Kano
Hotuna daga BALA MOH'D BACHIRAWA
IDAN akwai wata 'yar wasan fim wadda batun aurenta ya jawo ka-ce-na-ce da tausayawa, to shahararriyar jaruma Halima Adamu Yahaya ce. Lokacin da ta aure Alhaji Sa'idu Hashim (Malam Wane), wani kansila a Kano, al'amarin ya burge jama'a. To sai kuma auren ya mutu bayan watanni, ta fito da ciki. Wannan kuma ya jawo surutai. To yanzu kuma sai ga shi ta kara yin wani auren a lokacin da ko yaye danta Al-Amin ba ta yi ba. Wannan kuma ya burge mutane sosai, ya nuna cewa lallai dai Halima ba kin yin aure take ba.
Bayan fitowar Halima daga gidan Alhaji Sa'idu Hashim, ta yi finafinai da dama. Kadan daga cikinsu akwai Jinina, Miras, Mushaqqa, Jituwa da Mashi. Jituwa shi ne fim din ta na karshe kafin ta yi wannan auren.
Kwanaki biyu rak ne tsakanin auren Abida mohammed da na Halima. An daura na Halima a ranar Jumma'a 31 ga Mayu, 2002, a kofar gidan mahaifinta da ke Kwanar Gabari cikin birnin Kano. Wannan aure, wanda shi ne na uku da ta yi a rayuwarta (ta taba yin wani kafin ta shiga harkar fim), an daura shi da misalin karfe 5:00 na yamma, kuma dimbin 'yan fim sun halarta.
A wannan karon, angon na jarumar ta Kara Da Kiyashi wani matashi ne mai suna Kwamared Abdullahi Maikano Rimin Gado, wanda ma'aikaci ne a Karamar Hukumar Rimin Gado cikin Jihar Kano; hasali ma shi ne shugaban kungiyar kwadago (NLC) a karamar hukumar.
Daga cikin wadanda suka halarci daurin auren akwai Alhaji A.A. Kurawa, wanda shi ne daraktan Sashen Habaka Shirin Fim na Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, da kuma tsohon Sakataren Kungiyar Dillalan Kaset ta Jihar Kano, Alhaji Ahmed Mohammed Amge. Sauran sun hada da Aminu A. Shariff (Momo), Hafizu Bello, Jibrin S. Fagge, Mika'il bin Hassan (Gidigo), Mudassir Haladu (Young Producer), Ali Rabi'u Ali, da Bala Mohammed Bachirawa.
Kwanaki kadan kafin a daura auren, Halima ta tattauna da mujallar Fim. A lokacin, amaryar ta ce tunda ita ba sabon shigar aure ba ce, ba wata doguwar magana za ta yi ba. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Fim: Halima muna taya ki murna. Muna so mu ji yadda kuka hadu da Abdullahi Maikano.
HALIMA: Kana ji? Ni yanzu wannan auren ba wai sabon aure ne ba. Maganar yadda muka hadu duk ba ta taso ba. Allah dai ya hada mu, ko ma dai a ina ne. Kuma Allah ya tabbatar da hukuncinsa, shikenan.
Ga shi angon naki ma'aikaci ne a karamar hukuma. Shin a can za ki zauna ko a Kano zai aje ki?
HALIMA: Insha a Allahu a Rimin Gado zan zauna. Amma wasu na cewa (duniya) ta juya min ba kyau daga birni na koma kauye. To in a so in gaya masu a matsayina na 'ya mace, duniyata ni ba ta gigita ba don na tafi aure kauye. Saboda na yi imani duk 'ya macen da ta isa 'ya mace ce kuma har take jin aure ne ya haife ta, duk inda aka dauke ta aka kai ta za ta zauna.
Ni a nawa tunanin, birnin mace shi ne dakin mijinta. Saboda haka duk inda aka kai ni zan iya zama. Ba dai saboda kauna ba ne? Ai ba garinsu nake so ba, dan cikin garin nake so. Saboda haka dole in so zama a ciki.
Me za ki ce wa sauran 'yan fim wadanda za ki bari maza da mata?
HALIMA: Ka ga da ana ta cewa 'yan fim ba sa aure, to ga shi ana ta yi. Idan ba a yi ba Allah ne bai kawo ba. Idan Allah ya kaddara za ka yi abu, to idan lokacin ya zo sai ka yi shi. Ka ga kamar ni, wallahi wallahi ban taba tsammanin wannan shekarar zan yi aure ba. Tunda ka ga shayarwa nake (na dana Al-Amin). To ga shi yarona shekarata daya da haihuwarsa wanda ba ma na sa ran zan yi aure a wannan lokacin.
Ga shi za ki yi aure lokacin da yarinyar da kika kawo shirin fim, Maryam Umar, ba ta da lafiya, don an ce har ma an mayar da ita garinsu. Me za ki ce dangane da rashin lafiyar da aka ce tana damunta?
HALIMA: Wallahi ni ban ma san ba ta da lafiya ba. Rabon da in ga Maryam na fi wata shida. Ka ga kuwa ba zan san abin da take ciki ba. Wasu na ganin ga abin da muke ciki da ita, ba za su iya zuwa su ce min ga ta ba ta da lafiya ko wani abu ba. Wallahi ni ban ma sani ba. Amma Allah ya ba ta lafiya.
Wane kira za ki yi ga 'yan fim?
HALIMA: Don Allah, don Allah, don wanda ya kagi auren nan, wanda kuma ya halatta shi a yi, don Manzon Allah (S.A.W.), ni dai da ni da Abida, don Allah duk wanda ba zai bi mu da addu'a ta alheri ba, to yai shiru. Gaskiya akasarin abubuwan da suke samun 'yan fim akwai bakin mutane.
Me za ki cewa masu mujallun Fim da Bidiyo inda kika dan yi aiki na gajeren lokaci?
HALIMA: Ba abin da zan ce sai madalla na gode. Don ko ba komai a dauko ka a saka a wani abu wata karin daukaka ce da Ubangiji Allah ya yi maka, kuma alheri ne. Amma wani abu daya shi ne mujallar Fim da Bidiyo sun ji kunya ba karama ba (a ce) har kuka yi fim dinku kuka gama ba ku gayyaci Halima ba! Shi ne kawai abin kunyar da kuka yi (dariya).
Halima, mun gode.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|