|
Har yanzu Maryam Umar Aliyu matar aure ce!
Inji Mahaifinta, kuma zai karar su Abida a Nijar!
Maryam
|
Daga BASHIR YAHUZA a Katsina
WANI attajiri dan kasuwa dan asalin kasar Nijar mazaunin Katsina, Alhaji Umaru Aliyu, ya bara kan bilinbituwar da 'yarsa yarinyar nan Maryam ta shiga. Ya zargi wasu fitattun 'yan fim da ke Kano da cewa su ne suka hure mata kunne suka gudu da ita, sa'annan kuma suka cusa ta cikin sana'ar fim.
Idan ba ku manta ba, a Fim ta watan Mayu 2002 (shafi na 44) muka fara ba ku labarin Maryam Umar Aliyu a wani labari mai taken, "Maryam: Allura Cikin Ruwa..." A labarin ne muka bambance ta da jarumar shirin Mushaqqa, wato Maryam Aliyu. Har ila yau, a hirarta da Fim, Maryam Umar Aliyu, wadda yanzu shekarunta 15 da haihuwa, ta ce ba wani ne ya kawo ta ya saka ta a harkar fim ba. "Ni na kawo kaina saboda ina sha'awa". Amma da aka tambaye ta wanda ta fara haduwa da shi, sai ta ce, "Baban Gaje na fara samu, ya ce sai na kawo iyayena. Babana ya ce to idan ina so in yi fim sai na zauna a Katsina. Ni da babata muka ce a'a." To, bayan buga labarin ne Alhaji Umaru ya nuna takaicinsa game da halin da Maryam ke ciki, a wata ganawa da ya yi da wakilinmu a Katsina kwanan baya. Ya bayyaana cewa har zuwa yanzu Maryam tana da igiyar aure, don wai mijinta bai sake ta ba. Ga abin da ya ce da bakinsa, "Yadda abin yake shi ne, lokacin da Maryam ta dawo gidana da sunan yaji, mahaifiyarta ta sanar da ni, ni kuma na tsare ta domin tunanin matakin da zan dauka. A kan haka Abida ta zo har nan Katsina ta tafi da Maryam zuwa Kano. Ina cikin nemanta ne sai kawai na sami labarin cewa wai ta fara shirin wasan fim."
A kan haka wakilinmu ya tambaye shi cewa to wane mataki ya dauka kan Abida? Sai ya kada baki ya ce, "Na sha wahala kafin in gano asalin yadda aka gudu da Maryam, amma daga bisani sai al'amarin ya dauki wani salo, inda wani saurayi Musbahu Ahmed wai ya fito cewa yana son in ba shi ita aure. A kan haka na kai su kara a ofishin 'yansanda a Kano. An rubuta kara sai aka ba da belinsu da cewa idan an gano Maryam za a warware maganar." Shin ko ya gano Maryam din? Alhaji Umaru ya shaida wa wakilinmu cewa abin ma ya sake janza salo, domin a halin yanzu nemanta yake ruwa a jallo, amma wai ta bace ko kasa ko sama, kuma zargi yake cewa an boye ta ne da gangan. Kuma ga shi ya sami labarin cewa Abida ta yi aure. A kan haka ya ce a shirye yake ya yi shari'a da duk wanda ya sanya Maryam a fim. Kuma ya ce a halin yanzu kan hanyarsa yake kenan ta zuwa Nijar. A can zai shigar da kara don a shiryo takardu na musamman don gurfanar da wadanda yake kara ta hanyar diflomasiyya. Ya ce lauyansa ne ya ba shi wannan shawara don kasancewarsa ba dan kasa ba. Ya ce wannan mataki da zai dauka shi zai zamo sahihi, wanda kuma zai biya masa bukata.
Daga karshe sai ya ce, "Ina rokon duk wanda ya ga Maryam ya taimaka mani don in maida ta gida, don a halin yanzu ban san inda take ba."
Ga alama dai, kamar yadda muka fadi a labarinmu na farko a kan Maryam, za a jima ana jin duriyarta a fagen shirin fim. To, har yanzu labarin na Maryam Umar Aliyu bai kare ba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|