|
Kasuwar finafinai za ta mutu?
'Yan fim sun shiga halin ha'ula'i saboda durkushewar kasuwar finafinai. Ga hanyoyin da suke ganin za a bi a gyara harkar wadda yanzu take kakarin mutuwa.
KAMAR yadda Ra'ayin wannan mujallar na wannan watan ya nuna (a shafi na 2) a daidai halin da ake ciki yanzu kasuwar finafinai ta karye. Wasu sun ce ta fara makyarkyatar mutuwa. Ciniki kam ya ragu. Furodusoshi da dama sun durkushe. Yawancin 'manyansu' sun jingine harkar shirya fim, suna cewa sai yadda hali ya yi. Wasu kuma sun fito baro-baro sun ce sun daina yin fim din ma baki daya tunda babu riba. Wani ya bar garin. Wata 'yar wasan ta daina fitowa. Masu ayyuka kamar su waka ko editin, duk aikinsu ya ragu. Wasu sun fara tunanin neman sabon aikin yi ko sana'a. Da yawan 'yan fim suna zaman kashe wando tunda an rage yin fim. Yawancin masu shirya fim a yanzu baki ne wadanda ba su san dawan garin ba. Su ma bakin, duk wanda ya shirya fim sai ka ji ya ce, "Dan ba kara!" Da ma Hausawa sun ce haihuwa daya horo ne! Daga su sai kuma wanda wani ya ba shi kwangila ya shirya masa fim. Sai kuma mai gasa ido rufe da wani. Sai 'yan 'tunda-Wane-ma-ya-yi-fim-ni-ma-sai-na-yi'.
Shin me janyo wannan hali na ha'ula'i? Kuma me ya kamata a yi a magance shi?
Mujallar Fim ta shafe watanni uku tana yin bincike a kan al'amarin. Ta zabi wadansu 'yan fim, daga kan 'yan wasa da furodusoshi har zuwa kan marubutan labaran fim da dillalan kaset, ta tattauna da su a kan al'amarin. Tambayar da wakilanmu SANI MOH'D MAIKATANGA da IRO MAMMAN kan yi wa mutum ita ce: Me ya jawo kazancewar kasuwar finafinai kuma menene magani? Wakilan ba su tambayi masu kallon fim ba domin kusan a ce su ba su san abin da ke faruwa ba. Amsoshin da suka samu sun bambanta, domin kowa akwai yadda yake kallon abin. Duk da haka, za a iya tsame amsoshin baki daya a jera su a warka daya. Idan ana son a yi gyara, sai a gyara; idan kuma haka ake son a ci gaba da zama, shi ma ga fili nan ga doki nan.
Bismilla:
Balaraba Ramat Yakubu
|
BALARABA RAMAT YAKUBU
Marubuciya kuma furodusa
HAJIYA Balaraba, wadda a yanzu ta yi finafinai guda biyu, ...Sai A Lahira 1&2 da Ina Sonsa Haka 1&2, ita ce Sakataren Kungiyar Furodusoshi Mata ta Jihar Kano. A cewarta, ita dai ba ga wani abu na ci-gaba a wannan harka ba. "In ma har akwai wani ci-gaba, to na mai hakar rijiya ne," inji ta, "domin a kullum idan wata matsala ta taso za ka ga an taru an tattauna kamar da gaske, amma da zarar an bar wajen shikenan ba wani abu daya da za a yi a kai har sai wata matsalar ta kara tasowa. To ka ga babu wani ci-gaba da za a ce ana samu. In dai har ba mu gyara wasu matsaloli da suka sha gabanmu ba wanda kuma kowa ya san su ne suke damun 'yan fim, to ba za a ci gaba ba. Matsalolin su ne kamar irin su: 1. Yawan shigowar sabbin furodusoshi; 2. kasa gyara kasuwar finafinan; 3. rashin samun wata hanyar saida fim; 4. rashin hadin kan shugabanni; da kuma 5. zama a kan labari daya na soyayya.
"Idan har aka tsaya aka duba wadannan aka gyara su, to wallahi wannan harka za ta je inda ba ma zato. Amma ni yanzu batun fim ba abin da zan ce tunda na san duk wanda yake da bunu a gindi ba ya gudummuwar wuta, domin na yi manyan finafinai biyu, amma kasuwa tana ta yi min rawar banjo. Ina tunanin watakila zan kwashe kayana daga wajen 'dan kwalisa' (wato Ishaq Sidi Ishaq) in koma wajen Dan Ibro (wato Rabilu Musa) domin kasuwar da 'yan kasuwan da masu kallon finafinan ba su san menene tashin hankalin furodusa in ya fitar da fim ba. Don haka ina nan ina gaya wa Dan Ibro: Allah ya ja da ran camama!"
Sulaiman Sa'eed
|
SULEIMAN SA'EED
Darakta kuma dan wasa
TAURARUWAR Suleiman Sa'eed tana haskawa yanzu a fagen ba da umarni da kuma yin wasa. Shi ne darakta kuma jarumin shirin Maula.
Wasu na kuka da cewa wasu daraktoci sukan nace a kan cewa tilas su ne za su fito a matsayin jarumin fim din da aka ba su aikin shiryawa. A ganin masu wannan ra'ayin, wannan yana kashe kwarjinin fim. Daya daga cikin sukar da aka yi wa daraktan musamman a kan fim dinsa da ya fito da shi a fagen shirin fim na Kano, wato Maula, wanda Hindatu Bashir ta shirya, shi ne wai Suleiman da Hindatu sun cika fim din da 'yan Jos saboda su ma suna da asali da Jos. An manta da yadda 'yan Kano suke cika fim dinsu da Kanawa. Shi Suleiman ba haka yake ganin abin ba. A kan wadannan korafe-korafe guda biyu, ya ce, "Kamar yadda nake fitowa a cikin finafinan da na yi darektin ko kuwa na zamanto ni ne kusan mai jan fim din, wannan ba laifina ba ne; masu fim din su ne suke nuna suna son in fito shi ya sa nake fitowa. Amma ni ba na son in rika fitowa. Kuma kan batun Maula da ake surutun wai 'yan Jos sun mamaye fim din, wannan ai duk surutu ne tunda 'yan Jos a ciki ba su fi biyar ba, sauran duk 'yan Kano ne. Sannan an yi amfani da action (gumurzu) a fim din ne domin in za ka yi fim kar ka bari dan kallo ya san yadda karshen fim din zai kasance, to an yi haka ne domin a dagula wa mai kallo hankali."
Me daraktan zai ce a kan batun da ake yi wai finafinan Jos da na Kano sun bambanta, har wasu na cewa na Jos sun fi tsaruwa? Ya amsa: "Batun finafinan 'yan Jos da 'yan Kano, a gaskiya kowa yana iya kokarinsa daidai iyawarsa...
"Sannan batun ci-gaba a harkar fim yanzu ko kuma wani batun tafiya da zamani duk wannan wani abu ne da yake son hadin kan shugabanni da kuma samun shawarwari a tsakaninmu, sannan duk wani batun yin amfani da special effects da emotion ko action a cikin fim shi ma ba wai yin ba ne, a'a, samun kayan aiki mai kyau shi ne - tun daga kyamara zuwa su komfuta din da ake amfani da su wajen yin wadannan effects din. Sannan shi kuma mai fim din ya fitar da kudi domin ya yi abu mai kyau a fim dinsa. In har da kudin da za a kashe fim ya yi kyau to insha Allahu za a samu ci-gaba mai amfani."
ABBA LAWAN DANEJI
Mai kamfanin hada hotunan fim na CBC, Kano
ALHAJI Abba Lawan Daneji shi ne Mai Unguwar Daneji cikin birnin Kano. A fagen shirin fim an fi saninsa a fannin tsara fosta, yanzu kuma a fannin editin, wato hada hotunan bidiyo na fim, da tsara siddabaru (special effects). Shi ne ya yi siddabarun cikin fim din Salma-Salma Duduf inda aljana take daukar mutum a tafin hannunta, da shirin Aisha 2 inda Ibro yake artabu da wani dodo, da kuma shirin Lawisa inda mutum yake tafiya babu kai. A kullum Abba Lawan yana tunanin yadda zai yi ya inganta wannan fasaha tasa ta yin siddabaru a finafinan Hausa. Shin ko yana ganin harkar fim a nan gaba sai da irin wadannan siddabarun da ake yi da komfuta sannan ta ci gaba? Ya ce, "A gaskiya wannan harka tana kasa tana dabo. Saboda abin da ake samu a da ba a samu yanzu, kowa na kuka da kasuwar saboda ta bi ta cunkushe, kuma wannan yana takaita ma mutum wajen abin da zai kashe saboda komai ana yinsa ne don riba. Sannan kuma a zo ba a samu ribar ba. Saboda yanayin kasuwar ka ga zai yi wuya mutum ya je ya kashe kudinsa wajen yin siddabaru masu al'ajabi da ban mamaki domin suna neman a kashe kudi sosai, amma idan har a ce za mu daure mu yi labari mai kyau da inganci. Haka kuma bangaren yin wannan siddabaru muna da abubuwan da mu kanmu sai mun tsaya sosai in za mu yi. Da farko za ka ba mu labarin fim din ko yadda kake son siddabarun ya zama a cikin fim din, sannan mu kuma mu gaya ma in ka je wajen daukar shirin yadda za ka dauke shi yadda in mun zo ba za mu sha wahala ba. Shi ne kamar fim din Aisha 2 inda Ibro yake yin waka wannan dodon yake zuwa. A nan ma mun samu 'yar matsala saboda an samu kuskure wajen daukar shirin. Kamar a cikin ita wannan na'ura mai kwakwalwa muna da wasu programmes wadanda muka fi yin amfani da su yanzu, wato Adobe Effects da kuma Studio Max. A yanzu wadannan su ne programmes din da muke amfani da su kamar yadda aka shirya fim din Salma Salma Duduf inda za ka ga mutum a kan tafin hannu. Wannan duk ana daukar komai daban ne ita kuma matar mun dauko shoot dinta ne a wani daji daban inda muka sa mata wani farin kyalle a bayanta. Haka tafin hannun nata shi ma muka dauka daban sannan muka zo situdiyo muka hada su kamar lokaci daya aka yi su. Ni ma yanzu akwai wani da muke yi domin koyar da harufa da karatu da hada zantuka da zai taimake su a makarantunsu, kamar yadda shi Bala Anas ke kokarin yin fim na katun wanda ban san kan me zai yi shi ba."
TIJJANI IBRAHEEM BALA
Fitaccen darakta
TIJJANI dai shi ne shugaban Kungiyar Masu Bada Umarni a Finafinai ta Jihar Kano. Sadaukarwarsa ga aikin shirya fim da kuma dimbin gudunmuwar da ya bayar ga harkar sun sa ana girmama shi a fagen shirin fim. Duk da haka, da yake duniya mai sauyi ce, yawaitar sababbin daraktoci wadanda suna ganin su ma sun kawo karfi ta taimaka wajen kallon raini da wasu suka fara yi wa shi kansa Oga, wato Tijjani Ibraheem. Wasu suna sukarsa da cewa yawancin finafinansa labaran soyayya ne a cikinsu, sa'annan tsarin ba da umarninsa duk daya ne. Sa'annan ana sukarsa da cewa wai idan zai yi fim tilas ne sai ya sa wasu 'yan wasa, wadanda suka hada da Ali Nuhu, Ahmed S. Nuhu, Maryam Aliyu da kuma wasu mata uku wadanda yanzu matan aure ne, wato Fati Mohammed, Maijidda Abdulkadir da Abida Mohammed. Wasu sun danganta raguwar armashin finafinan Hausa ga abin da suka kira "wannan rashin tafiya da zamani" da suke ganin wai shi Tijjani yana yi, da dai sauran surutai. Ga alama, wadannan kalamai da ake yadawa a bayan fage sukan koma kunnen shahararren daraktan, domin a hirarsa da Fim, ya yi tsokaci kan abin da ya kira "gulmace-gulmace" da "munafinci" da kuma rashin girmama na-gaba.
Tijjani yana da masaniya sosai a harkar shirya fim da sayar da shi. Babu mamaki ganin ya kawo jerin matsaloli masu yawa wadanda yake ganin su ne ummulhaba'isin kuncin da ake ciki a harkar fim. Ga abin da yake cewa: "Wannan harka ba za ta samun wani ci-gaba ba in dai har ba mu bar yin gulma da munafinci a tsakaninmu ba. Za ka ga mutum ya zo yana ta yi maka fadanci, (amma) da zarar ya bar wajenka sai ya fara zaginka. Ko kuma ka ga ana bin wajen yin editin domin a ga waye yake editin, in an gani sai a je ana surutu a waje; ko kuma a je wajen su 'yan kasuwar ana cewa, 'Wallahi fim din wane bai yi kyau ba, kar ku karbi jaket da yawa!' To ka ga irin haka ai bai kamata ba. Kuma in har za a ci gaba da haka ba yadda za a samu ci-gaba. Sannan kuma babu girmama shugabanni; an maida su 'yan iska bacin kuma su ne suka kafa wannan harka suka sha wahala amma sun zama juji.
"Kuma maganar fim na soyayya da ake cewa ina yawan yi, ai ba wai soyayyar ba ce kawai a ciki. Kuma ai in ka kula, yawancin masu kallo na gida su ne mata, kuma sun fi son labarai irin wadannan na bangaren soyayyar. Tunda su 'yan sinima su kuma sun fi son bangaren rigima da makamancinsu. Kuma ni yanzu na fara irin wadannan finafinan.
"Sannnan duk wani fim da zan yi, muddin Ali yana nan, dole sai na sa shi a fim dina. Kuma shi Ali ina sa shi a fim ne saboda dacewa da inda na sa shi. Sannan kuma Ali ya san girman na-gaba. Kuma ina nan ina shirya wani fim wanda zai bai wa mutane mamaki matuka, kuma Ali ne a ciki. Kuma wai da ake cewa a sauya finafinan zuwa action (gumurzu) da sauransu, duk wannan ba su ba ne in har ana da mutum zai fita ya yi duk wannan ba wahala ba ne, a tsaya a ba kowa hakkinsa shi ne.
"Kuma su kansu sababbin furodusoshi da daraktoci, in har ba za su hada kansu ba, to wallahi ba inda za su je. Sai an samu fahimtar juna da kuma bin na-gaba, da kuma daina yin munafinci da gulma."
HAFIZU BELLO
Darakta
HAFIZU, wanda wasu ke kira 'Sir Hafizu Bello,' yana daga cikin 'yan fim kalilan da suke kokarin ganin sun tafi tare da zamani. Musamman ma dai ya rungumi sabuwar hanyar sadarwa ta intanet, inda yakan lelleka sakoki da yawa don ganin yadda harkar fim ke tafiya a sassa daban-daban na duniya. Burinsa ne ya kai finafinan Hausa koli can inda na Indiya da na Turawa suka kai. Sabon fim dinsa, Ruhi, shi ne alama ta yadda Hafizu yake kokarin ganin kawo sauyi ta hanyar rungumar hikimar da aka zuba a cikin na'urar komfuta.
Ya yake ganin harkar fim a nan gaba? Sai ya amsa: "A gaskiya akwai alamun abubuwan ci-gaba a wannan harka fa. Idan ka kula yanzu kowa ya fara ganewa. Domin shi mai kallo kullum yana son ya rika ganin sabon abu. Sannan kuma furodusoshi ma suna da wata matsala wacce ita ma idan aka gyara ta za a kara samun ci-gaba sosai; ita ce yadda za ka ga furodusa ya kawo labarinsa in aka ce ga yadda ya kamata fim din ya zamanto sai ya ce ai shi haka yake son labarinsa, sannan kuma ya ba da sunayen 'yan wasa da kanshi ko da ma mutum ya dace ko bai dace ba. To ka ga shi kuwa labari yana son ka ba shi wanda ya dace da shi, ba wai ka bi son ranka ba. Ka ga kamar yadda 'yan lokutan nan finafinan da suka fito sun dan samu wani sauyi, irin su Ibro Awilo; Ibro ya fito da wata siga daban, sannan Buri na Iyan-Tama shi ma ga shi an gan shi cikin wani irin yanayi daban; haka ma Rawani, ya zo da wani irin labari daban. Ka ga ai furodusoshin sun fara ganewa. Yadda abin zai tafi da kyau kenan.
"Sannan kuma fim ba shi da jumula guda daya aka sani, kowa da irin tashi. Ta haka ne za a ci gaba. Kuma ba wai don ka yi fim daya ko biyu ba ya karbu kuma ka ce za ka yi fim kamar Mujadala 3 da Wasila 3, wannan duk shirme ne. Sannan akwai wani kudiri da furodusoshi da daraktoci ke da shi, kamar a international market (kasuwannin kasashen waje), suna da target kusan goma, amma mu a nan kudirinmu biyu ne kawai: daga na sinima sai na home video. Za ka ga wani ya yi home video, wani don sinima. Ka kula a fim dina Jumurda na yi amfani da duka target din biyu, na yi kwafe din sinima daban sannan na yi na home video daban.
"Ya kamata furodusoshi da daraktoci su rika duba labari mai inganci da fa'ida ga masu kallo kafin ma a yi shirin daukar fim din, sannnan da kuma neman shawara daga masananmu."
MAJE EL-HAJEEJ HOTORO
Marubuci kuma furodusa
MAJE yana daga cikin marubutan littattafan hikaya wadanda suka yi fice a wannan zamanin. Ga masu karanta littattafai, sunansa ruwan-dare ne. Karbuwar irin labaransa ta sa furodusoshi suna sayensu su maida su fim. Sun hada da labaran finafinai kamar Sirrinsu, Shakka Babu, da Ruhi. Shi kansa Maje ya rubuta labarin fim dinsa na farko, wato Juyayi, wanda bai fito ba tukuna. Har ila yau, Maje marubuci ne a mujallar Bidiyo inda yakan yi tsokaci kan harkar fim na Hausa. To shin ya yake ganin ya dace a yi don gyara sana'ar fim wadda ta shiga cikin halin ha'ula'i?
Sai ya ce, "Duk wani abu da zan ce game da ciyar da wannan harka ta fim gaba ba ta wuce su furodusoshinmu su sauya akalar finafinansu ba. Domin in aka ce za a rika yin abu daya kullum, dole ne ya gundiri dan kallo, ya ji ma duk abin ya fita daga ransa. Ya kamata furodusoshi su kirkiri labari sabanin tunanin mai kallo wanda shi da kansa zai ce, 'Kai, yanzu wannan 'yan fim din Hausa ne suka yi shi?'
"Haka kuma ina alfahari da yadda aka fara juya littattafaina zuwa fim, irin su Sirrinsu, Shakka Babu, Ruhi wanda sunansa Al'ajabi amma yanzu Hafizu ya maida sunan Ruhi, wadanda duk wanda ke karanta littattafan Hausa ya san yadda suke dauke da wasu irin siddabaru kuma ba ya ta'allaka ba ne kan soyayya kawai. Akwai wasu abubuwa masu fa'idantarwa a ciki. Sannan kuma in har mutum zai yi irin wadannan finafinai to ya tabbatar ya samu kayan aiki masu kyau tun daga ita kanta kyamara din har na'ura mai kwakwalwa, sannan kuma ya samu daraktan da ya san yadda zai sarrafa siddabarun a komfuta din."
IBRAHIM HASSAN ADAMU
Dan kasuwar finafinai
IBRAHIM Hassan Adamu da ne ga hamshakin dan kasuwar nan mai sayar da kasakasai, wato Alhaji Hassan Adamu na bayan Bata, Kano. Ban da kasuwancin kasakasai, shi kansa furodusa ne wanda ya shirya finafinai masu yawa. A matsayinsa na dillalin kaset, mutane irin su Ibrahim suna daga cikin wadanda masu shirya finafinai suke suka a kan cewa halayyarsu ta bayar da gudunmuwa ga durkushewar kasuwar finafinan Hausa. Zargin da furodusoshi ke yi wa 'yan kasuwar shi ne wai suna yi masu mugunta wajen tallata finafinansu, suna rike masu kudade suna ba su da gutsin-gutsin ko da kuwa sun gama sayar da jaket din mutum.
Shin yaya Alhaji Ibrahim yake kallon abin a nasa bangaren? Ga bayaninsa:
"Idan komai ya yi tsanani, to maganinsa Allah. To alal hakika wannan harka tamu ta finafinan Hausa tana cikin wani hali mai tsanani wanda kuma idan har ba a tashi an hada hannu an daina duk wani gutsiri-tsoma ba, to wallahi ba inda za mu je. Amma in har aka samu gyara wadannan bangarori guda uku kamar da farko mu kanmu dillalan sannan su furodusoshin da kuma su 'yan wasan, sannan kuma shi kansa mai ba da umarni a wajen gabatar da shiri, to za a gyara. Kamar da farko, mu dillalan in har aka ce an samu wata matsala daga wurinmu, to ka ga dole shi ma furodusa ya sha wahala kafin kudinsa su fita. Alal misali, kai ne dillali, ka ba da bashi ga wani, ya zo bai ba da kudinsa ba, sannan kuma ya tafi wajen dan'uwanka furodusa ya ci gaba da harka da shi bacin kuma shi wancan ya san cewa tare kuke cinikayya, bai yi bincike a kan dawowarsa wajensa ba, kawai sai su ci gaba da harkarsu, kai kuma ko oho. Shi kuma furodusa ya zo karbar kudi an ce bai samu ba, ka ga babu ci-gaba kenan. In har bashi zai hau kan dillalan, to dole a samu koma-baya a harkar. Ya kamata dillalanmu mu tashi mu hada hannu a kan wannan don Allah.
"Sannan su kuma furodusoshi, ya kamata su hada kansu; a daina gulmace-gulmace - don ita ce ta ke kara dakushe wannan harkar. A hada kai a fito da tsari mai kyau. Sannan kuma su rika neman shawara daga mu dillalan kan wane irin tsarin finafinai ya kamata a rika yi, domin mu muka san irin finafinan da jama'a ke bukata. Da haka insha Allahu zuwa wani lokaci za a samu cimma burin habaka harkar.
"Haka su 'yan wasa, ya kamata su rage kudin da suke karba a fitowa daya. Domin yanzu in ka kula da wuya ka ga mutum ya yi fim ya saida kwalinsa na sama da dubu dari, daga nan sai ka ga su furodusoshin sun koma yin finafinan da ba su da tasiri ko wani fadakarwa.
"Har ila yau su ma daraktoci akwai tasu gudunmuwar ma, babba kuwa, saboda su ke shirya yadda fim din zai kasance. Shi ma darakta ya kamata ya rika taimakon executive producer wajen yin kasafin kudin da za a kashe a shirya fim din ta yadda ba za a kashe wasu kudade da yawa ba; sannan kuma ya bai wa mai fim din shawarwarin yadda fim ya kamata ya rika kasancewa domin su rika tafiya daidai da tarbiyyarmu da al'adunmu.
"Jama'ar gari suna son fim mai ma'ana da fadakarwa, ba kawai sai 'ina sonka, kina sona' ba. Kamar yadda finafinan HRB suke yi yana burge ni, domin gaskiya yana da labarai masu kyau, irin su Tawakkali, Furuci, ga su Mashi da sauransu irin su na da can - Ki Yarda Da Ni, ko yanzu na buga guda dubu sai na sayar. Ka ga ai irin wadannan su ne irin finafinan Malam Bahaushe. Sannan yanzu ma cunkushewar kasuwar finafinai ta yi yawa; suna fita barkatai. Ya kamata a duba a gyara don Allah."
A.A. RASHEED
Dan kasuwar finafinan Hausa
A.A. RASHEED yana daya daga cikin manyan dillalan finafinai da ke Kaduna. Shagonsa yana cikin babbar tashar mota ta Kawo. A nasa bangaren, ya bukaci furodusoshi da su yi gyara a kan matsalar shirya fim mai kashi na daya da na biyu in dai suna son kasuwar finafinai ta gyaru. Ya ce su 'yan kasuwar kaset suna samun koke-koke daga 'yan kallo game da finafinan da ake sakin na daya amma sai a kwashe kimanin wata shida ko ma shekara na biyun bai fito ba.
Alhaji A. Rasheed ya kara da cewa duk fim din da aka saki na 1 na biyun ya makale, to babu shakka darasin da furodusan fim din ke son koyarwa zai zama marar amfani kuma asara ce ga mai saye ya kalla. Ya bada shawarar cewa duk furodusan da ba ya da halin shirya fim mai na daya da na biyu a lokaci daya to ya hakura da abin da Allah ya hore masa ya shirya na daidai karfinsa.
Har ila yau dillalin ya kara jawo hankalin furodusoshi da cewa su yi taka-tsantsan wajen shirya fim mai na 1 da na 2 domin a cewarsa da yawa ana samun finafinan da na dayan kawai ke da abin a zo a gani, na biyun kuwa duk shirme ne. Ya ce wannan ya nuna baro-baro cewa wasu furodusoshi ba su tuntubar kwararru idan suka tashi shirya fim. Dan kasuwar ya ce hakan shi yake kawo cikas a kan wasu finafinan a samu rashin ciniki a kansu.
Daga karshe A.A. Rasheed ya shawarci furodusoshi da su kara inganta sana'arsu. Ya ce yawan shirya finafinai barkatai ba shi ne ba shi ne kwarewa ba, amma furodusa ya tsaya tsaf ya shirya kwakkwaran fim ko da guda daya kawai a shekara. Sannan ya yi fatan Allah ya kara hada kan furodusoshi da kuma su 'yan kasuwa yadda za su amfani juna da kyakkyawar fahimta.
MARYAM MASHAHAMA
Furodusa
MARYAM Mohammed Danfulani (Mashahama) fitacciyar 'yar wasan fim ce kuma furodusa. Ita ce shugabar kamfanin 'Mashahamatic Production,' Kano, wanda ya shirya finafinai uku - Bayan Wuya..., Ajali, da kuma Yayyafi, wanda bai fito ba tukuna. Da yake ita Maryam ta saka kafa a bangarori daban-daban na shirin fim, ta san matsalolin kasuwancin finafinan Hausa. Ita a nata ganin, wani dalili da ya jawo faduwar kasuwa, wani abu ne wanda yawancin 'yan fim ba su so su yi magana a kansa, wannan ko shi ne yawan kokarin durkusar da juna da furodusoshi suke yi. Ban da gumlce-gulmace da cin naman juna, wasu manyan furodusoshi, a cewar Maryam, sukan shiga malamai da bokaye su ce suna so a hana fim din wane ya sayu a kasuwa. "Sai mutum ya ce wa malami 'ina so a hana fim din wane yin tasiri a gun jama'a.' To, da yake shi ma wancan wane din zai yi kokarin ganin bayan dan'uwansa, sai ka ga an zo an yi ragas: wato wannan furodusan ya durkusar da wancan ta hanyar asiri, shi ma wancan din ya durkusar da wannan. Sai duk a taru a yi haihuwar guzuma - da kwance, uwa kwance," inji ta.
Maryam ta ce in dai an son a ci gaba a wannan harkar, to gaskiya sai an hada kai an daina kyashin juna. "Kowa dai yana yin wannan abin ne don ci-gaban kansa, to saboda me za ka so ka ga koma-bayan dan'uwanka?"
NASIRU GARBA DAN-FUNTUWA
Furodusa / Mai daukar hoto
NASIRU Garba Dan-Funtuwa ne furodusan fim din Maina, wanda bai fito ba tukuna. An fi saninsa a matsayin mai daukar hoton kati a fagen shirin fim na Kaduna.
Ra'ayin Nasiru kan wannan al'amari shi ne gaskiya yanzu jama'a suna fama da rashin kudi. Ya ce, "In ka lura, yawancin masu sayen kaset ma'aikata ne. Amma yau wajen wata hudu ba a biya su albashi ba. Wani ma yana kukan ko abinci babu a gidanshi."
Ya kuma dora laifi kan masu bidiyo kulob wadanda a da ba su ba da aron kaset din Hausa sai na Indiya da na Amerika. "In ba haka ba, ya za a ce kaset ya fito yau amma an kasa saida kaset dubu biyar?" inji shi. Na uku 'yan kasuwa ba su biyan furodusoshi kudinsu yadda ya kamata. Na hudu kuma yanzu furodusoshi sun yi yawa. "Kowa furodusa ne... Kullum shooting ake, wata sa'a ma labaran iri daya ne."
Mafita, a ganinsa, ita ce furodusoshi su rika hadewa suna shirya fim guda daya maimakon kowa ya je ya yi nasa. Ya ce ko a Indiya da Amerika haka ake yi. "Idan yau manyan furodusoshi su goma suka yi fim guda daya, da wuya a ba su wahala a kasuwa, ba kamar yadda muke yi yanzu ba - ka ga furodusoshi goma sun yi fim goma," inji Nasiru.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|