Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Darakta Adamu Halilu ya riga mu gidan gaskiya

... yana da shekaru 66

Daga SHAFI'U MAGAJI USMAN a Kaduna

Allah ya ji kansa
Alh. Adamu Halilu (a tsakiya rike da kwagiri) lokacin da aka karrama shi a Gidan Arewa abara. Daga damansa, Daraktan Gidan Arewa ne, Dk. Hamid Bobboyi

ALLAHU Akbar! Da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi, 1 da Satumba 2002 ne Allah cikin ikonsa ya yi wa shahararren daraktan nan Alhaji Adamu Halilin rasuwa. Ya rasu a gidansa da ke lamba 19, Kagoro Close, Sabon Garin Tudun Wada, Kaduna, bayan wata jinya mai tsawo da ya yi fama da ita. Marigayin, wanda muka taba yi wa lakabi da "baban daraktocin finafinai" a fitowarmu ta watan Agusta, 2000, ba bako ba ne ga makarantanmu, musamman 'yan fim na da da na yanzun.

Mai shekaru 66 kafin rasuwarsa, Alhaji Adamu Halilu ne dan Arewa na farko da ya fara zuwa Turai ya karanto aikin fim cikin shekarun 1950. Ya kuma rike manyan mukamai a karkashin wannan aikin, wadanda suka hada da Babban Darakta na Sashen Majigi na Gwamnatin Tarayya (Federal Film Unit) da kuma Manajan Darakta na farko a Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (Nigerian Film Corporation).

Marigayin ya ba da gudunmuwa ga harkar fim da za a iya cewa babu kamarsa a kasa baki daya wajen shiryawa, ba da umarni da kuma jagorantar manyan hukumomin gwamnati kan wannan aiki. Shi ne kadai talikin da ko dai ya shirya ko ya ba da umarni ko ya yi duka biyun wajen aiwatar da finafinai akalla 80 na Turanci da Hausa a karkashin gwamnatocin da suka gabata. Sun hada da Shaihu Umar, Black Heritage, Kanta of Kebbi, Baban Larai, Moment of Truth, da sauransu. Shirin Baban Larai shi ne fim na farko da aka shirya da Hausa.

Haifaffen garin Garkida da ke cikin Jihar Borno, Alhaji Adamu Halihu ya karbi lambobin yabo masu yawan gaske daga hukumomin gwamnati na kasar nan sakamakon irin gagarumin gudunmuwar da ya bada a harkar fim na tsawon shekaru akalla 40. Lambar yabo ta baya-bayan nan da ya karba ta hannun tsohon shugaba kasa Janar Buhari ita ce wadda Cibiyar Adana Kayan Tarihi ta Arewa (Arewa House) ta Jami'ar Ahmadu Bello, Zariya, ta ba shi a lokacin rufe bikin baje kolin finafinai da littattafai da kayayyakin al'adun gargajiya da fasaha da ya gudana cikin watan Maris, 2001 a Kaduna.

Daraktan ya mutu da burin shirya ingantattun finafinan tarihi da suka shafi rayuwar Sarauniya Amina ta Zazzau, Sarki Bagauda na Kano, Mai Idris Alooma na Borno, da Jihadin Shaihu Usman Danfodiyo.

Ya rasu ya bar mace daya, 'ya'ya 11 da jikoki shida. Dimbin jama'a da wakilan hukumomin gwamnati da masu zaman kansu sun je gaisuwar ta'aziyya ga iyalan mamacin. A cikinsu akwai Nigerian Film Corporation (NFC), National Council for Women Societies (NCWS), wasu membobin MOPPAN, Sadiq A. T/Balewa, matar gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Asma'u Makarfi, tsohon shugaban Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya Mista Brendam Shehu, da tsohon Minista Maccido Dalhatu.

Har ila yau akwai irin su Ambasada Mahmud Yahaya, Alhaji Musa Bello, Alhaji Yusuf Hamisu Abubakar, Hajiya Laila Dogonyaro, Hajiya Maisarari Chanchangi, wasu matan tsofaffin gwamnoni da suka hada da matar Dabo Lere, matar Buba Marwa, matar tsohon gwamnan Bauchi Mshelia, da matar Hamza Zayyad wadanda suka tafi tun da farko-farko. Akwai manyan mutane da kungiyoyi da dama wadanda ba mu ambato ba saboda yawansu kuma har ya zuwa lokacin rubuta wannnan rahoton kungiyoyi da al'ummar kasa ba su daina kai gaisuwar ta'aziyyar ba ga iyalan shi marigayi Alhaji Adamu Halilu. Allah ya jikansa, amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin