BABALLE Hayatu yana daga cikin matasan 'yan wasa wadanda tauraruwarsu ke haske yanzu a fagen shirin fim a Kano. Tun daga fitowarsa ta farko a cikin Abin Sirri Ne a cikin 1996 ana ta damawa da shi a fagen shirin fim. Ya fito a finafinai sun fi gaban a kirga su. Kadan daga cikinsu su ne:Furuci, Tawakkali, Mashi, Mujadala, Sakiya, Sakamako, Biyayya, da kuma Murdiya.
Sunan Baballe na ainihi dai Abubakar Hayatu. Mutanen gidansu ne suka sanya masa Baballe domin Abubakar sunan baban mahaifinsa ne. An haife shi a Yakasai, Kano, a cikin 1974. Ya fara karatu a 'Giginyu Primary School' daga 1980 - 86, sa'annan ya wuce Makarantar Sakandare ta Kawaji a Kano, inda da ya kammala sai ya shiga KCAS ta Kano daga 1996. Daga nan ne ya wuce Jami'ar Bayero inda a halin yanzu yake karatu na digiri a kimiyyar siyasa, wato Political Science.
A hirar da muka yi da shi, Baballe ya yi magana a kan yadda ya shiga harkar fim da yadda shi da su Ali Nuhu suke zama hankaka maida-dan-wani-naka da finafinan Indiya, da yadda 'yan makarantarsu a Jami'ar Bayero suke kallonsa a yanzu, da kuma yadda rasuwar mahaifiyarsa a kwanan baya ta shafi yadda yake kallon rayuwa a yanzu. Bismilla:
Fim: Daga wane lokaci ne ka fara yin wasan Hausa?
BABALLE: Na fara yin wasan Hausa a 1996 lokacin da na fara fitowa a cikin fim din Abin Sirri Ne. shi ne fim dina na farko da kamfanin 'HRB Enterprises' suka ba ni dama na dan fara lekowa.
Fim: Kafin sannan an san ka a yawancin fim a matsayin mai rubuta tsarin labarin fim (screenplay). To ya aka yi ka iya wannan abu?
BABALLE: To ka san kowa da irin basirar da Allah ya ba shi. Kuma a gaskiya Ali Nuhu na daya daga cikin mutanen da suka ba ni kwarin gwiwa domin in jaraba wannan basira da Allah ya ba ni.
Fim: Wadansu idan suka kwaikwayi wani fim na kasar waje ko an ce masu kwaikwayo ne suka yi za ka ga sun hakikance sun ce karya ne. Amma shi Ali Nuhu yakan fito fili ya ce shi fim din Indiya ne yacanza wa fasali ya maida shi na Hausa. To Baballe za mu so mu ji yadda kake yin wannan canje-canje domin a finafinan FKD mukan ga kai ne marubucin labarin kuma kai ke yin 'screen play'.
BABALLE: Idan ka duba kusan al'darmu da ta Indiya bambancin kwalliya ne. Wani zubin ba ni kadai ne ke zaunawa ba. Mukan zauna da ni da Ali Nuhu mu taru mu duba abubuwan da ya kamata a canza, yadda in Malam Bahaushe ya kalla zai ce, "E, wannan al'adarmu ce," ba ya ce "Allah-wadai wannan ba al'adarmu ba ce" ba. Duk yadda dai aka san za a sanya abu ya dawo ta bangaren al'adarmu, shi ake bi, wanda muke kuma bai saba wa al'adarmu ko addininmu ba, ana barinsa haka.
Fim: Wasu da yawa sun nakaki finafinan Indiya tun kafin su shiga harkar na Hausa. Mun san Rabi'u Ibrahim mai HRB da suna Rabi'u Indiya tun tuni. Shin kai ta hanyar shiga sinima ne ka san finafinan Indiya?
BABALLE: Idan na ce maka ta dalilin sinima ne na yi karya. Ni dai na san ina kallon fim din Indiya amma a gida nake kallo. Duk fim din da na gani nake bukata na tashi na gani a gidanmu ne. Tun daga tsofaffin finafina Indiya na da, mun tashi mun tarar da su a gida muna kallo har muka kai an daina sayo mana muna sayowa da kanmu. Gaskiya ni ban cika zuwa sinima ba. A dalilin finafinan Hausa shi ne nakan shiga sinima. Sai dai karance-karancen mujallunsu sosai ina yi.
Fim: Me ya sa ka fi fitowa a matsayin dan mai kudi ko dan birni?
BABALLE: Ai kuwa na fito a matsayin dan kauye misali a Tawakkali, Hamayya da Sharadi.
Fim: Mu muna yi maka kallon zalwajahaini, wato mai fuska biyu. Ga ka dan HRB, kuma ga ka dan FKD.
BABALLE: Ni dan ko'ina ne, da HRB da FKD da HB. Saboda su ne kashin bayana industry. To dalilin wadannan wuraren guda uku na fara sanin harkar fim.
Fim: A cikin Mujadala kun fito a matsayin mugaye har wasu masoyan Ali Rabi'u Ali suka gargade shi da ya daina fitowa da irin sigar da ya fito da ita a cikin Mujadala...
BABALLE: Ai kai in dai cikakken akto ne, to duk bangaren da aka sa ka sai ka karba ka gwada. Dan wasa an san shi da tarar aradu. Idan ka yi abu ko a karbe ka ko a ki karbarka.
Fim: Wace irin rayuwa kake fuskanta a makaranta a matsayinka na dan wasan fim?
BABALLE: A makaranta kusan kowa idonsa na kanmu. Wallahi zan fada maka a yau idan aka kafa sakamakon jarabawa kowa so yake ya je ya ga nawa, don ya ga abin da na ci maimakon ya je ya duba nasa. Wasu kuwa har da 'yanmata suna cewa suna sha'awar wasan Hausa. Ni dai duk wanda ya zo wurina fata nake in ga mun rabu lafiya da shi.
Fim: Kana cikin ganiyar fim ne ka rasa mahaifiyarka watannin baya. To wane bambanci ne ka samu kanka a ciki yanzu da babu ita?
BABALLE: Ka san rashin mahaifi ko mahaifiya ba abu ne karami ba. Tabbas na samu ci-gaba da karin daukaka bayan rasuwar mahaifiyata wanda na so a ce da ranta ta ga wasu abubuwa nawa saboda tana ba ni karfin gwiwa kan wannnan sana'a da nake yi. Wani lokaci ma ita ke tashina da asuba ta ce min, "Yau ai sai ka tashi tunda za ka je lokeshin wuri kaza." Ni yanzu sai dai in kara yi mata addu'ar Allah ya rahamshe ta, ya gafarta mata. Ranar da za ta rasu tana kwance ba ta da lafiya na ce ina da fim a wani wuri ba na so su yi asarar kudinsu idan ban je ba. Ta ce in tafi ta yafe min amma in turo mata kanenta. Kafin in je in dawo daga fim ta rasu. Ba na nan aka kai ta amma daukacin 'yan fim kaf babu wanda bai je ba. Ka ga sai na ji tamkar ina wurin saboda jama'ata masu kaunata sun je a madadina.
Fim: Ina da ina ka je zuwa yin fim a kasar nan?
BABALLE: Ta bangaren harkar fim a nan dai Arewa iyakacina Kaduna, Bauchi, Sokoto, Katsina, da Maiduguri.
Fim: Daga cikin wasunku masu bin finafinan Indiya sau da dafa, an ce wai akwai masu fahimtar yaren Indiya. Shin gaskiya ne wasunku suna ji?
BABALLE: E akwai.
Fim: Kamar su wa kenan?
BABALLE: Ka ga Ali Nuhu yana ji, Rabi'u Ibrahim HRB yana ji... Kadan kenan.
Fim: Ban da kai?
BABALLE: (Dariya) Ai kadan ka ce in lissafa maka, ba ka ce in sa da kaina ba! In kana bukata to sai in kara da sunana.
Fim: Wane ne gwaninka cikin jaruman Indiya?
BABALLE: E to, a maza dai ba ni da gwani, a mata akwai Sridevi, Karisma Kapoor, da Kareena.
Fim: A matsayinka na mai bin finafinan Indiya sau da kafa...
BABALLE (ya katse): Tsaya malam! Ni fa yanzu finafinan Hausa na sa a gaba…
Fim: To kana gadara da na Hausa kan na Indiya.
BABALLLE: Ai ba ma gadara ba, gadardar zan ce, don kuwa a matsayinmu na Hausawa kayan aikin da muke da shi ai muna kokari sosai.
Fim: Mun gode.
BABALLLE: Ni ma na gode.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin