Karshen tika-tika, tik! Shukakkar soyayyar nan da ta dade tsakanin fitaccen jarumi kuma furodusa, Ali Nuhu, da rabin ransa Maimuna Mohammed, kakar girbinta ta yi. Yanzu haka an kammala duk wasu shirye-shiryen yin auren, an kuma sa ranar daurin auren, wato ranar Asabar 15 ga wannan watan na Maris, 2003. A Zariya za a daura auren, inda iyayen amaryar suke zaune.
Wakilanmu sun gano cewa farkon soyayyar Ali da Maimuna shi ne lokacin daukar shirin fim din Wasila na 1, lokacin da suka hadu a gidan dan kwallon kafar nan Tijjani Babangida inda aka dauki wakar fim din mai taken"Jamilu Jamiluna", sanadiyyar raka kanwarta Habiba da ta yi wajen nata saurayin, wato furodusan shirin, Yakubu Lere, wadanda su ma an daura aurensu kwanan baya.
An sha yin tsegunguma game da masoyan biyu cewa shi Ali ba zai aure ta ba, musamman lokacin da suka taba samun wani sabani a tsakaninsu. Wani wanda ba ya son a bayyana sunansa ya ce sabanin ya faru ne sanadiyyar wata rasuwa da aka taba yi a gidan su amaryar, amma Ali bai samu damar zuwa ta'aziyya ba, wanda hakan a cewarsa, ya sa wasu daga cikin dangin amaryar suka nuna bacin ransu, tare da daukar alwashin ba za su ba shi 'yarsu ba. Wata majiyar kuma ta ce wasu 'yan je-ka-na-iya ne suka nemi tabarbarar da maganar auren, saboda sun nemi su yi wa Ali jagora kan maganar amma ya nuna ai shi ma namiji ne, ba sai anyi masa iso ba.
Duk da cewa masoyan biyu sukan boye wa duniya irin soyayyar da suke yi, amma da abin ya tsananta dole ta fito fili. Saboda tsananin son da suke yi wa juna, majiyarmu ta gano cewa a ko da yaushe, suna sane da duk abin da kowannensu yake ciki, duk da kasancewar shi angon a Kano yake, ita kuma a Kaduna.
Wani dan wasa cewa ya yi akwai ma lokacin da Ali ya ce ya fasa auren saboda yawan surutan mutane.
To duk ma dai abin da ya taba faruwa a baya, yanzu ya zama tarihi, tunda maganar aure ta tabbata.
Ali Nuhu mutum ne mai yawan masoya, musamman 'yanmata. "Da ma ruwan ido ya hana shi yin aure tun tuni," inji wani dan wasa. "Yanzu kuwa ai ta kare. Saura mu ga na Ahmed S. Nuhu-shi ma idan ya gama nasa ruwan idon."
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin