Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 42   Agusta 2003
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

'Macutan Daraktoci Sun Cika Industiri Suna Bata Mana Aiki'

Inji Saifullahi Tukur Yola

SAIFULLAHI Tukur Yola ba mutumin Adamawa ba ne. Mutumin Kano ne, dan unguwar Yola ta cikin Birni. A halin yanzu yana daga cikin matasan daraktocin finafinan Hausa da aka sanya wa ido saboda hangen irin basira da Allah ya yi musu. Akwai finafinai da yawa wadanda wannan hazikin darakta ya shirya wadanda ake jin yin irinsu zai iya sauya akalar finafinanmu na Hausa. Daya daga cikinsu shi ne Hairani, wanda ya fito dauke da labarin rikicin wani gida inda suruka ba ta kaunar matar danta, suka hada kai da matar wan dan nata suka dinga musguna wa yarinyar. Wani fim din na Saifullah shi ne Judah, wanda ake ganin babu shakka sai ya fi Hairani karbuwa da gawurta.

Daraktan, wanda dalibin jami'a ne a yanzu, ya tattauna da wakilinmu kan abubuwan da yake ganin suna bata aikin daraktocin finafinan Hausa, da irin gyaran da yake so a yi kafin harkar fim ta samu ci-gaban da ake bukata. Saifullahi ya yi maganganunsa kai tsaye ba tare da jin shakka ko tsoron kowa ba. Bismilla:

FIM: Menene matsayin ilminka?

SAIFULLAHI: Matsayin ilimina a yanzu shi ne difloma a Shari'a and Civil Law, amma yanzu ina karatun digiri a B.U.K.

FIM: Gaskiya ne duk daraktocin fim din Hausa karanta suka yi?

SAIFULLAHI: Ba haka ba ne, hasali ma duk daraktocin Hausa ba wanda ya karanta; baiwa ce kawai, wanda da yawa kuma daga cikinsu karambani ne, don ba abin da suka fahimta a daraktin suke yi. Wannan shi ya sa yawancin 'yan wasa su ma sai ka ji sun ce sun zama daraktoci, domin sun ga daraktocin namu ba wai abu suke a darektin din nasu ba, daga Action sai Cut, ba sa koyar da wani abu ga dan wasa. Sai kuma cuta da daraktocin suka sa a gaba; Allah Allah ake wani furodusa ya zo mai dan tsoka-tsoka a cuce shi. In ya ce yana son yin fim, fim din da bai wuce ya ci N200,000 ba, sai a caje shi N500,000 ko miliyan daya, kuma ba za a tsaya a yi masa aikin fisabilillahi ba. Shi ya sa za ka ga in furodusa ya sha da kyar aka gama fim din, to ba ya sake marmarin yin wani fim din. Dalilin haka ne shi ma sai ya ce ya zama daraktan kansa, don shi bai ga wani abu a daraktin din ba. Da Allah zai hada shi da darakta na sosai ya ga aikin daraktan, to da in aka ce ya zo ya yi aikin daraktin shi da kansa ya san an hada shi da aikin da ba nasa ba. Kuma kamar yadda na ce baiwa ce darektin a wajen wadansu, hakika haka ne, akwai masu nasibi a harkar, sai su ma suna bata rawarsu da wasu abubuwa da bai kamata ba. Kai dai Allah ya kiyaye!

FIM: Yaushe ka fara aikin daraktin? Kuma finafinai nawa ka yi darektin?

SAIFULLAHI: E to, gaskiya ni tun ina makarantar sakandaren kwana nake darektin a 1985, don muna da kungiyar dirama ta makaranta wadda ni ne daraktanta; ni nake rubuto labari sau da yawa kuma na zo na yi daraktin dinsa a dandamali (stage), a lokacin kuma mun sha wakiltar makaranta a gurare da yawa, mu je mu yi wasa, wanda wannan ya sa mun samu kyaututtuka da dama kuma duk da wadannan labarai da nake rubuta na yi daraktin. Kuma na yi kungiyar dirama mai suna 'Barewa Dramatical Group' da ke Gadon-Kaya. Nan ma na yi darakta a cikinta wanda mun yi wasa cikinta irin na stage.

Sai dai a irin wadannan finafinai namu na yanzu na bidiyo, to sai in ce maka shi na fara shi ne a shekarar 2001, saboda na ga wadansu wadanda ba su san meye ma darektin ba duk suna aikin suna nema su bata harkar, shi ya sa na ce to bari in dauki makamaina in yake su. Na fara ne da wani fim mai suna Nan Gani Nan Bari wanda wata tangarda ta sa fim din ya tsaya ba a karasa shi ba. Amma a yanzu ina da finafinai, wadansu suna kan hanyar fitowa; wasu su ne Kujiba-Kujiba, Hairani, Judah, Yazayi, Ganji Gaga, Na Ji Na Gani. Kuma ina godiya ga Allah da ya sa wadansu daga cikin finafinan da na gama za su fita, kamar Judah, da Hairani da Kujiba-Kujiba. Dan'azimi Baba ne ya rubuta su, kuma shi ya yi min furodusa, domin kuwa shi wannan bawan Allah in na ce muku shi ne uban 'yan fim din Hausa gaba daya ba za ku musa mun ba, saboda kaifin basirarsa da hikima wadda Allah ya ba shi, wanda tun da aka fara fim din Hausa yake ba da gudunmuwarsa kuma har yanzu bai gaza ba, wanda ya kirkiri abubuwa da dama a harkar, irin su waka a fim da kidan fiyano kansa, da dai sauransu. Sannan har yanzu ba a samu wanda ya kamo shi a rubuta labari mai ma'ana ba. Kuma ga shi mai shiryawa, mai daukar nauyi, kuma ga shi darakta. To don haka nake alfahari da wadannan finafinai da ya yi mani, ni kuma na yi daraktin. Allah ya kara mana irinsu, ya kuma sa mutanenmu su rika koyi da su.

FIM: Yaya kake ganin makomar finafinan Hausa nan gaba kadan?

SAIFULLAHI: Babu inda za ta, in ba an tsaya an yi gyara ba. Domin finafinanmu a yanzu suna da matsaloli wadanda in dai ba mu gyara su ba, to harkar ma mutuwa za ta yi, Allah ya kiyaye. Wadannan matsaloli suna da yawa, irin su satar basira; misali, sai ka ga mun dauko labari irin na Indiya mun yi, wanda ba irin al'adarmu daya da su ba. Sai ka ga fim din ba tsari. Kuma idan ka yi tunani sai ka ga yaushe muka fara fim din, da har kwakwalwarmu za ta toshe a ce ba mu da labarin kanmu sai mun dauko fim din Indiya mun juya shi? Bayan su Indiya din nan sun fi shekara dari suna yi, wanda idan ka duba sai ka ga a cikin finafinansu na wadannan shekarun ,wanda suka saci basirar Turawa ko wasu ba su fi a kirga su ba, amma duk sauran basirarsu ce. To don me mu ba za mu rika yin kokarin kanmu ba, sai mun saci nasu? Ta kai ta kawo yanzu a Hausa hatta waka ba za mu iya yin kokarin kanmu ba, sai dai mu juya wakar Indiya mu sa a fim dinmu. Wannan abin kunya ne sosai in muka yi tunani. Domin mu ma muna so finafinanmu su shiga kasashen duniya, kamar yadda nasu suke shiga. To in ya fita aka ji ko aka ga irin wadannan wakoki nasu, ba mu ji kunya ba? Abu na biyu shi ne rashin yin amfani da abubuwa masu kyau. Ba mu son kashe kudi a finafinanmu. Ko fosta wadda za a lika ba mu yin manya, sai dai mu yi na maleji. Kai dai kawai a ga sunan fim dinka, da dai sauransu, wanda in muka duba abokan harkarmu na Kudu, ba haka suke yin nasu ba. Su saboda kashe kudi da suke yi sun fi mu ci gaba nesa ba kusa ba, har gwamnatin Nijeriya tana mara masu baya fiye da mu. To abubuwan dai suna da yawa, Allah dai ya gyara mana.

FIM: Me za ka iya cewa a kan yadda daraktocin finafinan Hausa suke aiwatar da ayyukansu, musamman na Kano?

SAIFULLAHI: Su gyara ayyakansu, don irin aikinsu kusan iri daya ne, kullum ba ci gaba, kuma su sa Allah a zukatansu, su cire cuta daga ransu, su kuma cire ganda da algus a cikin ayyukansu. Don haka ni ba zan iya cewa komai a kan yadda suke aiwatar da ayyukansu ba, don ba aikin suke ba.

FIM: To me za ka ce da jama'ar gari 'yan kallo?

SAIFULLAHI: Su sa ido su ga finafinaina da za su fito nan ba da dadewa ba. Allah ya sa a yi kallo lafiya. Kuma in da akwai shawarwari da za a ba mu to muna maraba da su. Salamu alaikum.

FIM: Mun gode.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin