Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 45   Disamba 2003
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Usaina: Soyayyar Mijinta Ta Maida Ita Zabiya

Daga WAKILINMU

WASU 'yan shekarau kadan da suka wuce, fitaccen daraktan nan da ke Jos, Magaji Mijinyawa, yana zaune a wani falo na furodusa Sani Muhammad Sani, shi kuma furodusan yana cikin uwardaki sa'annan uwargidansa Usaina tana safa da marwa tsakanin kicin da sauran bangaren gidan domin ta ga mijinta da amininsa sun samu maganin yunwa. Tana yi tana rera wakoki daban-daban. Magaji ya kame a kan kujera kamar gunki yana sauraren wakokin. Ya kasa motsawa. Can sai ya yi wuf! ya tashi tsaye ya kwala wa mai gidan kira. Ita kanta Usaina sai da ta tsaya cak! a cikin tafiyarta. Sani ya fito da sauri, ya dauka wani abu ne ya faru.

Daga nan tunanin barin matarsa ta yi wakokin finafinansa ya shiga zuciyar Sani. Amma abin mamaki duk da cewa Magaji ne ya kawo tunanin, shi Magaji bai bai wa Usaina waka ta yi masa a cikin fim ba ko da guda daya ce, sai dai kullum ya samo karin waka sai su ukun su zauna su yi ta yi a gidan.

To, kowane fasihi yana da mai neman tauye shi. Usaina ta sha gamuwa da kulle-kullen mahassada wadanda suka dinga kushe muryarta saboda manakisa. Duk da haka, da yake Hausawa sun ce idan rana ta fito tafin hannu ba ya kare ta, Usaina ta samu daukaka, domin fa ta rera dimbin wakokin fim. Har ga shi a yau an wayi gari Farida Adams, 'yar wasa a Jos, tana cewa, "Da zan samu yadda nake so a harkar fim da sai na ce babu muryar mawakiyar da zan hau a cikin fim sai ta Usaina."

A lokacin da za a yi wani fim mai suna "Dan Jos," furodusan ya ce shi muryar Usaina yake so a fim din. Sai kuwa mahassada suka shiga aikinsu, suka matsa masa a kan cewa kada ta yi wakar, wanda hakan bai rasa nasaba da artabun da mijinta Sani Muhammad Sani yake yi da wasu daga cikinsu. A karshe dai cewa furodusan ya yi idan dai ba ita za ta yi wakokin ba sai dai ya yi fim din babu waka. Ya hakikice musu. Amma duk da haka sai da wasu mazugan suka yi munafinci a lokacin da Sadi Sidi Sharifai ya iso Jos domin yin wakokin, kulle-kullensu suka yi nasara, a karshe dai ba da ita aka yi wakokin ba.

Usaina Muhammad Sani 'yar shekaru 26 ce. Ita ce uwargidan furodusa, darakta, kuma marubuci Sani Muhammad Sani. 'Ya'yansu hudu cikin makarantar 'Jos Markazul Tarbiyyatul Islam,' Jos. Usaina, wadda ta yi aji uku a GSS Jos ta bari, ba ta yi kama da shekarunta ba; idan ka gan ta sai ka dauka 'yar shekaru goma sha ce!

To amma menene asalin abin da ya jawo hankalinta a kan yin wakokin? "Yawancin wakokin da na rubuta aka yi su a cikin finafinai asalinsu na yi su ne domin mijina saboda sonsa da nake yi ya sa nakan zauna in rubuta wakoki da sunansa in fitar masu da kari in rera masa yana jin dadi. Wani lokaci ma idan da kananan kuraje a fuskarsa ina fasa su ina yi masa".

Misali da ta bayar daga cikin irin wadannan wakokin shi ne na fim din Hamza-Habib wanda ta yi kamar haka: "Sani, Sani, Sani kaunarka nake, wanda in kalle ka sai in ji wani dadi, idan na dube ka sai in ji wani haske.." Sai ta juya a fim ya zama "Darling, Darling…"

Usaina ba ta fara yin wakokin finafinai ba har sai da ta yi aure. Amma a lokacin da tana budurwa takan rubuta wakokin Mauludi, wakokin yabon Annabi, ba ma na makarantarsu kawai ba har na wasu makarantun. Akan zo a neme ta ta rubuta ta fidda kari ko ta rubuta.

"Amma kuma nakan yi idan a gidan biki ne a wannan lokacin, ko a cikin kawayena nakan rera wakoki ne a kan Sani Muhammad Sani," inji ta. "Ko da ni da kawayena muna rera wakoki, tawa kam a kan Sani nake yi."

Ta yi dariya ta ce, "Zan gaya maku dalilin wannan. Kamar, ni a mafarki na ga Sani, a nan muka hadu, da na gan shi a zahiri sai da na cika da mamaki, na kasa komai a ranar, ga shi kuma a unguwarmu yake. Ashe Allah zai sa shi ne mijina!"

A dalilin wakoki a gidan biki na 'yan'uwanta da take yi ya sa iyayenta suka hana ta yin waka, suna tsoron kada ta zama marokiya. "Kuma ba ba ni kudi ake yi ba fa. Ina yin su domin raha ne, domin 'yan'uwana na son in yi masu su ji dadi."

Wacce irin hanya Usaina take ganin za a iya bi domin samun wakoki ingantattu?

"Hanya ta farko ita ce mu daina gaggawar yin su domin mu gama mu shiga kasuwa," inji ta. Ta kara da cewa, "Shi fa mutumin da yake wannan harkar kamata ya yi ya natsu, ya fitar da kansa daga cikin wadanda za mu iya kira 'yan kasuwa, ya zama mai kishin fim. Domin shi dan kasuwa damuwarsa a yi a gama kudi ya shigo hannu, ba wai inganta abin ba. Indiyan nan fa da muke ta yabonsu bayan tsabagen kudin da suke kashewa, suna bai wa komai hakkinsa: darektan kida daban, mai rubutawa waka daban, wani lokaci ma mai fitar da kari daban, masu kida kuwa sun wuce a yi maganar mutum daya a kan keyboard, masu bushe-bushe daban, masu ganga daban masu rerawa daban; komai ma'aikacinsa ne zai yi. Sannan a dawo comfuta a yi ta faman harhada kidan da tace shi. Don me ba za su yi wa mutane fintikau ba?"

Usaina ta ce sai mun kasance masu juriya, dauriya da hakuri kafin mu fara hango kafarsu ma balle mu kamo su. Sannan mun tambaye ta ko me za ta iya ce wa mafiyoyin da suka yi mata bukulu a lokacin daukar wakokin "Dan Jos"? Sai ta ce, "Fada da abin da Allah ya ba wani, fada da kaddarar Ubangiji ne, fada kuma da kaddara ta Ubangiji fada ne da Allah. Su ci gaba da yi domin ba da ni suke yi ba da Wanda ya ba ni muryar ne, Wanda kuma ya ba ni basirar. Sannan kuma idan kana son ci-gaba ka nemi mahassada amma fa ba ka nema da bakin hali ba, ka neme su da kyawawan halaye to za ka ci gaba."

Zabiyar ta ce ita ba ta taba sanin cewa ta isa ba a cikin mawaka, sai da ta samu mahasaada. Sau da yawa 'yanmata sukan bi ta situdiyo ko gida domin kawantaka saboda jin dadin muryarta da suke yi. Shi kuma mijinta ya ce idan yana sauraron muryarta a kaset, musamman ma dai idan ya yi tafiya takan ba shi tausayi ne har ma ya ji yana son komawa gida.

Da kuma muka tambaye ta menene take yawan tunawa a cikin rayuwarta wanda ba za ta taba mantawa da shi ba, sai ta amsa, "Mijina. Domin akwai wata irin rayuwa da yake yi wadda ba kowa ne ke yin ta ba. Na san yana da zafin rai idan an taba shi amma kuma shi ba zai taba wani ba. Duk da muna rawa ni da yarana - rawa ta barkwanci fa - yana shigowa idan yara ne suke waka sai ya kama yin rawar. To wannan abu ne da ya sa muke son shi har ba ma so ya fita a gidan. Da ya dawo kuma sai ka ga mun ruga da gudu mun rungume shi. To irin wadannan abubuwan ne suka sa ba zan taba mantawa da shi ba har abada. Amma kuma fa idan ka gan shi sai ka dauka ba zai iya yin hakan ba." Ga masu son ci gabanta kuma ta ce, "Alhamdu lillahi na gode masu su ma. Allah kuma ya ba su daukakar da ba su taba tunanin za su samu ba. Allah kuma ya ba su zaman lafiya da iyalansu, idan kuma ba su da iyalan Allah ya ba su ko mace ko namiji. Haka ma wadanda suke tsoron in samu dama zan fi wadanda suke kuma Allah ya bar mu tare."

Usaina Muhammad
Usaina Muhammad

An haifi Adam a garin Zangon Kataf cikin Jihar Kaduna. Matsayin karatunsa na boko sakandare, wanda ya gama a cikin 2000, amma ya ce yana son ya ci gaba.

Use ya fahimce fadar nan da Hausawa ke yi, cewa duk inda abincin mutum yake a nan zai same shi. "Wani lokaci kana wata hanyar amma ba a nan abincinka yake ba," inji shi. Don haka zuwansa Kano sai ya dukufa koyon kidan fiyano a karkashin gwanin kidan nan da ya bar kamfanin 'Sulpha', wato A. Dengu. Ya dauki tsawon shekara daya yana koyo kafin hannunsa ya fada.

Shin yaya yake ji yanzu a rayuwarsa yadda yake yi wa finafinai kida, sabanin abin da ya yi niyyar yi a farkon shigowarsa industiri? Sai User ya amsa, "Gaskiya na gode wa Allah saboda a yanzu babu wani mawaki da ba zan iya aiki da shi ba, kuma su ma suna jin dadin aiki da ni, kuma ni ma haka."

Kowane fasihi yakan fuskanci wahaloli iri-iri a fagensa. Adam ma yakan fuskanci wahala wajen fitar da kida da irin launin da mutum yake bukatar wakarsa. Adam User ya ce: "Alhamdu lillahi, duk wannan iyawa ne, in ka iya ka yi komai, amma kuma za ka ga wasu suna daukar waka abu ne mai sauki, sai sun zo gadan-gadan wai za su yi waka sai ka gama yin kidan za a fara sai ka ji macen ta yi muryarta daban shi ma tashi daban sun kasa hawan kidan. Kuma in a ka ji wakar sai a ce laifin makidin ne. Saboda haka dole sai ka tsaya ka gyara, saboda ka saba da aiki da mawakan da suka iya wakar kuma sun san aikinsu."

Adam User ya bayyana mana yadda aka yi A. Dengu ya bar 'Sulpha Studio'. A cewarsa, "Ya bar nan ne saboda ci-gaba, tunda yanzu shi inda yake yin kida yana yi ne da 'mini-computer' kenan, mu kuma nan muna yi da 'keyboard' ne kuma yana Jos yanzu."

User ya ce duk da yake yana da kusan kowane mawaki, ammma kuma ya fi yawan aiki da Yakubu Muhammad. "Saboda haka na fi jin dadin aiki da shi," inji shi.

Kowane dan fim yana da wani buri a wannan sana'a. Burin Adam User shi ne ya ga ya daukaka ta bangaren kidansa, "ya zamanto har waje ana kirana in yi kida ba Kano kawai ba, kuma a ce ina fita tare da mawaka muna aiki."

Daga lokacin da ya fara wannan sana'a zuwa yanzu bai san yawan finafinan da ya yi wa kida a wakokinsu ba. Ya ce, "Ban san adadinsu ba amma barin maigidana daga nan na buga wakokin da suka kai akalla dubu hamsin."

Shin ya taba samun wani alheri daga wani da ya buga masa waka a kan irin alherin da ya samu a wannan wakar? Sai ya ce babu. "Daga wanda ya rera waka da kidana da kuma mai kamfanin da aka yi wa wakar duk ba wanda ya taba zuwa ya ban wani abu, wai ya ce ko ya ji dadin kidan da nai masa. Babu wanda ya taba yi min haka."

To a misali idan yanzu abin a ce an daina yin waka a finafinan Hausa me Adam zai koma yi?

"Ai ba kidan kawai na tsaya ba," inji shi. "Muna yin talla, tunda ina aiki har da komfuta, domin har daga wani garin ana zuwa wajena muna yin jingle da su kuma ina yi wa masu English music kida kuma kusan kullum sai na yi aiki da su. Don an daina waka a wasan Hausa ba ni da wata matsala; aikina zai tafi sosai."

Ya furta ra'ayinsa kan kalaman batsa da wasu mawakan ke yi. Adam User ya ce, "E, wadannan irin kalamai da ake magana ina jinsu amma kuma shi mai wakar zai gaya maka cewa shi ga abin da yake nufi sabanin abin da kai ka yi tunani. Saboda haka ko ni in an yi irin wannan sai na tambayi mutum abin da ake nufi a nan, in tambayi mutum sai ya fahimtar da ni."

Dangantakar User da sauran abokan aikinsa dai lafiya lau, duk da yake Allah ya daukaka shi. "Gaskiya muna zaman lafiya da kowa, kamar su Aleebaba, Apollos da kuma Konzuma wadanda duk a harkar na same su. Babu mai dauka ta da wata niyya kuma ni ma ba na bakin ciki da su domin duk a gabana suke."

A karshe ya shawarci abokan sana'ar tasa makada, ya ce, "Abin da ake amfani da shi a waka wajen kida kamar busa ko wata ganga, yadda za ka ji abin da aka ji a wannan wakar shi za a ji a waccan. Shawarata a nan, a yi kokari a rika canzawa. In kari ya zo na Hausa ko da ya zo da irin wancan a rika kokari a dan canza wani abu."

To Adam User, da fatan sun ji.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin