Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 46   Junairu 2004
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Burina in yi kida ba a Kano kawai ba

- ADAM USER

Daga SANI MOHAMMED MAIKATANGA

ADAM User yana daga cikin manyan makadan wakokin finafinan Hausa a wannan zamanin. Yana aikinsa ne a fitaccen situdiyon nan mai suna 'Sulpha Musical Studio' da ke Zoo Road, Kano. Hasali ma dai wasu na kiransa 'A kori-Aleebaba', ba don komai ba sai don nuna amincewea da kwarewarsa.

Sunansa dai Adam A. Zango, to amma an fi saninsa da User. Sana'ar fim ce ta kawo shi Kano. "Abin da ma ya kawo ni ba shi na samu kaina a ciki ba, domin niyyata da in shiga harkar fitowa a fim, sai kuma ban samu ba. Sai mai gidana da ya kawo ni garin, Salisu Mu'azu, ya ce in fara koyon kida tunda ban samu wannan abin da nake so ba."

Adamu User
Adamu User a bakin aikinsa

An haifi Adam a garin Zangon Kataf cikin Jihar Kaduna. Matsayin karatunsa na boko sakandare, wanda ya gama a cikin 2000, amma ya ce yana son ya ci gaba.

Use ya fahimce fadar nan da Hausawa ke yi, cewa duk inda abincin mutum yake a nan zai same shi. "Wani lokaci kana wata hanyar amma ba a nan abincinka yake ba," inji shi. Don haka zuwansa Kano sai ya dukufa koyon kidan fiyano a karkashin gwanin kidan nan da ya bar kamfanin 'Sulpha', wato A. Dengu. Ya dauki tsawon shekara daya yana koyo kafin hannunsa ya fada.

Shin yaya yake ji yanzu a rayuwarsa yadda yake yi wa finafinai kida, sabanin abin da ya yi niyyar yi a farkon shigowarsa industiri? Sai User ya amsa, "Gaskiya na gode wa Allah saboda a yanzu babu wani mawaki da ba zan iya aiki da shi ba, kuma su ma suna jin dadin aiki da ni, kuma ni ma haka."

Kowane fasihi yakan fuskanci wahaloli iri-iri a fagensa. Adam ma yakan fuskanci wahala wajen fitar da kida da irin launin da mutum yake bukatar wakarsa. Adam User ya ce: "Alhamdu lillahi, duk wannan iyawa ne, in ka iya ka yi komai, amma kuma za ka ga wasu suna daukar waka abu ne mai sauki, sai sun zo gadan-gadan wai za su yi waka sai ka gama yin kidan za a fara sai ka ji macen ta yi muryarta daban shi ma tashi daban sun kasa hawan kidan. Kuma in a ka ji wakar sai a ce laifin makidin ne. Saboda haka dole sai ka tsaya ka gyara, saboda ka saba da aiki da mawakan da suka iya wakar kuma sun san aikinsu."

Adam User ya bayyana mana yadda aka yi A. Dengu ya bar 'Sulpha Studio'. A cewarsa, "Ya bar nan ne saboda ci-gaba, tunda yanzu shi inda yake yin kida yana yi ne da 'mini-computer' kenan, mu kuma nan muna yi da 'keyboard' ne kuma yana Jos yanzu."

User ya ce duk da yake yana da kusan kowane mawaki, ammma kuma ya fi yawan aiki da Yakubu Muhammad. "Saboda haka na fi jin dadin aiki da shi," inji shi.

Kowane dan fim yana da wani buri a wannan sana'a. Burin Adam User shi ne ya ga ya daukaka ta bangaren kidansa, "ya zamanto har waje ana kirana in yi kida ba Kano kawai ba, kuma a ce ina fita tare da mawaka muna aiki."

Daga lokacin da ya fara wannan sana'a zuwa yanzu bai san yawan finafinan da ya yi wa kida a wakokinsu ba. Ya ce, "Ban san adadinsu ba amma barin maigidana daga nan na buga wakokin da suka kai akalla dubu hamsin."

Shin ya taba samun wani alheri daga wani da ya buga masa waka a kan irin alherin da ya samu a wannan wakar? Sai ya ce babu. "Daga wanda ya rera waka da kidana da kuma mai kamfanin da aka yi wa wakar duk ba wanda ya taba zuwa ya ban wani abu, wai ya ce ko ya ji dadin kidan da nai masa. Babu wanda ya taba yi min haka."

To a misali idan yanzu abin a ce an daina yin waka a finafinan Hausa me Adam zai koma yi?

"Ai ba kidan kawai na tsaya ba," inji shi. "Muna yin talla, tunda ina aiki har da komfuta, domin har daga wani garin ana zuwa wajena muna yin jingle da su kuma ina yi wa masu English music kida kuma kusan kullum sai na yi aiki da su. Don an daina waka a wasan Hausa ba ni da wata matsala; aikina zai tafi sosai."

Ya furta ra'ayinsa kan kalaman batsa da wasu mawakan ke yi. Adam User ya ce, "E, wadannan irin kalamai da ake magana ina jinsu amma kuma shi mai wakar zai gaya maka cewa shi ga abin da yake nufi sabanin abin da kai ka yi tunani. Saboda haka ko ni in an yi irin wannan sai na tambayi mutum abin da ake nufi a nan, in tambayi mutum sai ya fahimtar da ni."

Dangantakar User da sauran abokan aikinsa dai lafiya lau, duk da yake Allah ya daukaka shi. "Gaskiya muna zaman lafiya da kowa, kamar su Aleebaba, Apollos da kuma Konzuma wadanda duk a harkar na same su. Babu mai dauka ta da wata niyya kuma ni ma ba na bakin ciki da su domin duk a gabana suke."

A karshe ya shawarci abokan sana'ar tasa makada, ya ce, "Abin da ake amfani da shi a waka wajen kida kamar busa ko wata ganga, yadda za ka ji abin da aka ji a wannan wakar shi za a ji a waccan. Shawarata a nan, a yi kokari a rika canzawa. In kari ya zo na Hausa ko da ya zo da irin wancan a rika kokari a dan canza wani abu."

To Adam User, da fatan sun ji.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin