Jama'a mu yi wa Shu'aibu Kumurci addu'a
In ji Tsigai
"Rannan duniya tai motsi
Ran rasuwar Ciroman Gwambe"
-
SHATA, a wakar "Allah Jikan Ciroman Gwambe"
LABARIN rasuwar su Balaraba ya riski jama'a a cikin tsananin al'ajabi.
Kusan kowa ya gigita da ya ji cewa wai Balaraba Mohammed, wadda aka daura wa aure jiya-jiyan nan, ta mutu. Abin da kowa ke cewa shi ne, "Anya da gaske ne?" Mai yin tambaya ga aboki ko makwabcinsa ya yi, mai buga tarho zuwa ga wanda ya san yana da labari - kamar ofishin mujallar Fim - ya buga. Abin da ya biyo baya shi ne gigita. 'Yar wasa Rukayya Umar Santa, wadda ta zo Kaduna domin abu biyu - auren Balaraba da kuma kammala daukar fim din Maina na mai dauko hoton kati Nasiru Mohammed - suma ta yi da ta ji bakin labarin. Har an nufi asibiti da ita, ta farfado. A Kaduna da Kano inda 'yan fim suka fi yawa, kamar an yi ruwa an dauke. Duk wanda ka gani sai ka ji ya ce, "Wai Balaraba ta rasu! Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!"
To, dukkan mai rai mamaci ne. Kowa yana da abin cewa a kan wannanal'amari, musaman kan Balaraba, wacce ita ce 'yan fim suka fi sani a cikin wadanda Allah ya dauki ransu. Su kansu masu kallon finafinai, sun bugo waya, wasu sun zo da kansu, suna cewa don Allah a sa su a cikin labarin masu yi wa mamatan addu'ar Allah ya gafarta masu. Amma ba zai yiwu mu kawo ra'ayoyin kowa da kowa ba. Don haka a nan ga mutane kalilan da muka rubuta ra'ayoyinsu: DARDA'U SAMINU ZARIYA:
DARDA'U ne direban bas da aka yi shatarsa ya debi 'yan biki domin tafiya da su Kano daga Kaduna. A cewarsa, wasu maza ne suka tare shi ya zo wucewa a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya, wadda take kusa da gidan bikin, suka ce masa don Allah ya zo zai kai wasu 'yan biki Kano. Domin kagararsu da a yi tafiyar ko ciniki aikin ba a yi da shi ba, illa kawai aka ce masa babu abin da zai gagara; shi kuma za yarda. Ga karin bayanin da ya yi mana:
"Bayan da muka bar Kaduna, ni nake gabansa (shi direban da ya dau su Balaraba). A daidai Jaji sai suka wuce mu. Dukkansu suna daga mana hannu. Sun dan ba mu tazara saboda yanayin motarsu ba daya ba ce da tawa. Da muka tadda su sun yi hadarin, wasu cikin motar tawa suna cewa kada in tsaya, amma sai na tsaya. Duk ba mu san cewa su ne suka yi hadarin ba.
"Mun bar Kaduna karfe 2:46. Hadarin kuwa ya faru kusan karfe 4. Direban (su Balaraba) yaro ne. A lokacin da hadarin ya faru mutum biyu suka mutu nan take. Kuma ni na kwaso mutum hudu a motata zuwa Kaduna: ita Balaraba, yayanta, wata mata da ta yi rauni da kuma direban nasu wadanda dukkansu suna da rai a wannan lokaci. Sai kuma gawar yaro da aka sanya cikin motar har ila yau."
BAFFA AHMED (CINNAKA):
CINNAKA yana cikin motar bas wadda ta dauki sauran 'yan bikin lokacin za a kai amarya Kano. Ga bayaninsa:
"Ba ni kadai ba, kuma ba 'yan wasa kawai ba,wannan mutuwa ta girgiza kowa kwarai da gaske. Har aka kwana ba ni cikin hayyacina, sakamakon wannan mutuwa ta Balaraba da 'yan'uwanta. Allah ya gafarta mata, ya kyauta tamu in ta zo."
USAINA GOMBE (TSIGAI):
"Alhamdu Lillahi. Ni kaina na yi kukan da ban taba yin irinsa ba a duniya, a gaskiya. Amma sai na tuna Ubangijin da ya yi ta ya fi mu son ta. A gaskiya ban da mu kan mu da muke juyayin rasuwar wannan 'yar'uwar tamu muna tausaya wa shi mijin nata, Shu'aibu, wanda mun san a masu harkokin fim ba a taba yin soyayya kamar tashi da Balaraba ba. Muna rokon jama'a su yi masa addu'a domin gudun kada ya kamu da hawan jini ko ciwon zuciya. Mun yaba da irin karshen rayuwar Balaraba; akwai abin koyi. Kuma Allah ya sa mu a danshinta."
HAMISU LAMIDO IYAN-TAMA:
"Duk abin da Allah ya tsara wa dana'adam babu wanda ya isa ya kankare masa shi. Shi angon da Allah ya ba shi auren wannan yarinya kuma ya karba, Allah Ubangiji ya sa hakan shi ne mafi alheri a gare ta, ya kuma ba shi hakuri da juriyar rashinta. Da fatan Allah zai masa sauyin da zai zam alheri a gare shi.
"A lokacin da na samu sakon rasuwar ni da Bashir Mudi Yakasai, daga Hajiya Balaraba (Ramat) ta waya, ce mata na yi don Allah ta daina shiga cikin masu yada ji-ta-ji-ta, don an sha yada irin wadannan sharrurrukan a kan mu 'yan wasan fim. Ta tabbatar mani da wannan labari, amma ban yarda ba sai da na bugo waya Kaduna na ji tabbacin labarin daga bakin shugaban kamfannin Koli wanda ya ce a lokacin da muke magana da shi ma daga asibitin yake. Nan gaba daya muka yi tsit, masu kuka suna yi, duk an yi tagumi. A gaskiya, tun da labarin ya tabbata a gare mu, duk harkokin fim ya tsaya a Kano. Ni kuwa a kamfanina ma na tsayar da komai har sai an yi sadakar uku. A take na ce dukkan ma'aikatana kowa ya tashi. Bayan na koma gida, barcin da nake zaton zan samu a gidan wallahi ban samu ba saboda yadda na yi ta ganin gilmawar ita wannan baiwar Allah a zuciyata, musamman saboda wata hira da na yi da ita kwana biyar kafin auren har na sa ta ta yi mani wata talla na sabon shirina da zan yi Buri. Na sa kaset din ina kallo sai na ji kuka ya zo mani. Allah ya ba mu hakurin jure rashinsu a Film Industry ita da Darakta Aminu Hassan Yakasai, ya kuma jikansu da gafara."
ADAMU BELLO ABILITY, shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar kaduna:
"Wannan rasuwa ta Balaraba rasuwa ce mai ban tausayi. Abin bai shige ni sosai ba sai da na je na ga motar a inda suka yi hadarin, sannan na dawo na gana da iyayenta na yi masu ta'aziyya. Muna masu fatar alheri tare da fatar sun cika da imani. Mu kuma da iyayenta da masoyanta baki daya ina mai ba mu hakurin? Alh. Hamisu Lamido Iyan-Tama, Shugaban Furodusoshin Arewa, yana tattaunawa da wakilinmu a gidan mamatan, lokacin da ya je ta'aziyyarashinta tare da 'yan'uwa nata da suka rasu tare."
SAMINU MOHAMMED MAHMUD:
Alhamdu Lillahi, mu Musulmi Allah ya yi mu da juriya wajen tawakkali. In ban da tawakkalin to, da sai mu ce akwai wani abu. Allah shi ne mafi sanin dalilin da ya sa ya aukar da wannan mutuwa kan Balaraba a wannan lokaci. A gaskiya fisabilillahi ni na kasa barci saboda juyayin rasuwar wannan yarinya. Saboda akwai ta da wasu kyawawan dabi'u a yayin da kake aiki ta ita, wadanda in ka tuna da su tilas ka kasa duk wani aiki da kake yi a yayin da ka ji labarin wannan rasuwa. Aiki da Balaraba bai da matsala, musamman a sha'anin kudi, tunda kusan ba don kudi take yi ba. A lokacin da muka samu labarin, muna shooting (na fim din Maina). A take wata yarinya cikinmu ta fadi ta suma. Ni kaina na rude har na fita daga hayyacina a daidai lokacin. Abin da nake roko ga iyayenmu, wato iyayenta da shi mijin, da kuma mu kanmu, shi ne dauwama, tunda shi kansa ma Manzon Allah da ya yi masa rasuwa, aka yi bayani cikin Kur'ani aka ce mutuwarsa ma ita ce ta fi rayuwarsa alheri. Ita ma (Balaraba) muna fatan Allah sa wannan mutuwar tata shi ne ya fiye mata alheri fiye da ci gaba da rayuwarta.
MALAM ISA BELLO (JA)
Gaskiya mun yi babban rashi, don ko mutuwar su Aminu Hassan ba ta girgiza ni kamar yadda ta wannan baiwar Allah ta yi ba. Allah ya jikanta, Allah ya jikanta.
ZAINAB BAITA, No. 243 Court Road, Kano
Na yi bakin ciki kwarai domin ni a gaskiya sai da na zo nan (oishin Fim) da kuka tabbatar min sa'annan na yarda. Ni a da ban yarda ba. Allah ya jikanta, Allah ya sa ta huta.
AHMAD ABDULLAHI SUKAIRAJU, Kasuwar Wambai, Kano
Na tausaya wa Kumurci fiye da yadda kake tsammani. A wurin bikin da mujallar Fim ta karrama mawaka na fara ganinsa. Kuma abin sha'awa, tare na gan su da Balaraba. Daga wannan rana ban kara ganinsu ba. Da ma can ni Kumurci ne dan wasana. Wannan rashi har da ni aka yi wa shi domin nawa ne yai rashi. Allah ya ba shi hakuri kuma Allah ya jikan Balaraba.
FATIMA ABDULHALIM (Romon Rogo)
Ina cikin gidan Hajiya Umma Ali sai Mandawari ya bugo waya ya sanar da ita. Nan take gaba dayanmu muka rikice da kuka. Kuma da na je gida na shaida wa mahaifiyata cewa Balaraba ta rasu, wallahi yanke jiki ta yi ta fadi. Har yanzu cikin damuwa nake, ko abinci ba na iya ci sosai.
ALH USAINI HAJIN FAFA, furodusan shirin Nabila
Allah Ubangiji shi ya san abin da ya ke so da bawansa. Muna wurin gala da Kumurci da Sani Mai Iska, sai aka ce an bugo waya daga Koli a Kaduna. Muka tafi ofishina. Ni na dauki waya aka fada min rasuwa. Nan take jiri ya kama ni. Sani ya tambaye ni abin da ya faru, na kasa fada masa. Na ba shi waya aka fada masa daga can, sai dai Sani ya fada wa jama'a. Wasu daga cikin mata har suma suka rika yi. Allah ya jikan Balaraba, ya kuma gafarta mata, ya sa ta cika da imani. Shi kuma Shu'aibu Allah ya ba shi hakurin rashin da ya yi da dukkanin iyayenta da sauran 'yan shirin fim din baki daya.
HAUWAR LENSCOPE MEDIA
Abin da zan ce da wannan rasuwa ta Balaraba, abu ne wanda ya girgiza mu, kai, har ma wadanda ba harkar suke yi ba. Ba za a taba mantawa da wannan rashi ba. Ina mika ta'aziyyata ga mahaifan Balaraba da Shu'aibu Lawan da duk wani dan wasa. Allah ya gafarta mata, amin summa amin.
MOHAMMED MUHAMMAD LANKASTA, MAIDUGURI
Ni dai tun tuni ina so in halarci wannan daurin aure, amma Allah bai yi ba. Kwatsam, sai mutane suka rika zuwa suna tambayata, "Wai da gaske Balaraba ta rasu?" Da ma zan zo fitar da wani fim dina mai suna Amana Ce, sai kawai na taho domin tabbatarwa. Shi ne na zo nan Hajin Fafa. Allah ya jikanta. An yi rashi babba.
SHAFI'U LAWAL ABUBAKAR DA AMINU ABUBAKAR DA AMINU DALHAT ADAMU DA ABUBAKAR SULEIMAN 'TAILOR', KADUNA
Munai maku ta'aziyyar Balaraba. Allah ya jikanta da rahama, amin. Kuma shi Shu'aibu, Allah ya ba shi juriyar rashinta.
ABUBAKAR YAKUBU SARKI DODO, Shugaban kungiyar 'Asikolaye Youth Devt. Association',Nnamdi Azikiwe Way Bypass, Kaduna
Ina ta'aziyya ga uban wannan yarinya mai farin jini, da mijinta da kuma sauran 'yan wasa. Ba shakka wannan mutuwa ce wacce ta girgiza al'umma, domin ita Balaraba Allah ya taimake ta ta yi aure a kan gaba, wato lokacin da mutane ke jin ta a jikinsu. Mutane sun san Balaraba tana da mutunci da hangen nesa. Kuma tanuna mana cewa soyayyarta ga Kumurci soyayya ce ta gaskiya, ba ta kudi ba. Allah ya jikanta, yarahamsheta, amin.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin