Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 29   Mayu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Rayuwarmu
Mu Leka Hollywood
Malam Zurke
Mutanen Boye
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Akwai:
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Wani sashe (na mata) na mahalarta taron kaddamar da KARBALA

A yau fim ya fi wa'azi shiga zukata

In ji Malam Zakzaky a wurin kaddamar da KARBALA
Daga SANI MOH'D MAIKATANGA a Kano

AN bayyana cewa wasan kwaikwayo babbar harya ce ta shigar da sakonni a zukatan mutane, musamman ganin cewa ba sosai jama'a kan dauki wa'azi a halin yanzu ba.

Shugaban Rundunar 'Yan'uwa Musulmi a Nijeriya, Malam Ibrahim Yakub Al- Zakzaky ne ya yi wannan furucin a babban dakin taro na otal din 'Royal Tropicana', Kano, lokacin da ake kaddamar da wani fim da 'Yan'uwa Musulmi Mata (Muslim Sisters) suka shirya mai suna Karbala.

Taron kaddamawar da aka yi a ranar 13 ga Afrilu, 2002, an shirya yinsa ne a rufaffen dakin motsa jiki na 'Sani Abacha Sports Complex'' amma aka sami sabani lokacin da masu shirya taron suka sami labarin gwamnatin Jihar Kano ta shirya wani taro a wurin. "Gwamnatin dagutai ta nuna cewa za ta gabatar da wani taronta sai dai mu bari sai da yamma," inji Malam Zakzaky. Ya kara da cewa bayan an sanar da shi ne ya ce a je a kama wani wuri daban.

Cikin jawabin da ya gabatar, shahararren malamin ya ce tun farko ba fim aka yi niyyar yi ba, an nemi shawararsa ne kan abin da ya dace a yi don a samu kudin shiga maimakon a rika neman taimako daga 'Yan'uwa don gudanar da wani abu. Malam ya ce ya ba da shawarar a yi wasan kwaikwayo maimakon yawon zuwa wa'azin da ake yi; ta haka za a tunatar da 'Yan'uwa "tunda yawanci ba daukar wa'azi ake yi ba."

Dimbin jama'a, musamman 'Yan'uwa Musulmi (Muslim Brothers) magoya bayan Malam Zakzaky sun cika dakin taron da kuma harabar otal din. Duk da cewa an biya kudin shiga N100, wannan bai hana samun cinkoso ba a bangaren mata da kuma su kansu maza. Yayin kaddamar da fim din na Karbala an tara kudi a take sama da N600,000.

Daraktan fim din, Malam Bala Makosa Zariya, wanda kuma shi ne editan mujallar Nishadi, ya yi nuni da cewa an shirya wannan fim ne domin fadakar da 'Yan'uwa Musulmi da su farka". Kuma ya ce, "Ba fim ba ne irin na jahiliyya da sauran ke yi. A'a, wannan fim duk wanda ya kalle shi zai san cewa an shirya shi ne domin ci gaban Musulunci da al'ummarsa".

Ita kuwa furodusar fim din, kuma matar Malam Zakzaky, Malama Zeenat Ibrahim, a cikin jawabin da ta yi a wurin ta yaba da irin goyon bayan da maigidanta da kuma darakta Bala Makosa suka bayar. Ta kuma gode wa Mai Martaba Sarkin Gumel, Alhaji Ahmed Mohammed Sani, wanda ta ce sun sami shawarwari da taimako daga gare shi. Ta gode wa wani sarki da ta ce ke cikin Jamhuriyar Nijar, da Yariman Zazzau Alh. Mannir Ja'afaru, wanda ya taimaka da dawakai, da kuma duk wani wanda ke da hannu a cikin shirya fim din.

Tun farko bayan bude taro da addu'a an gabatar da wadanda su ne suka dauki nauyin shirya fim din na Karbala, wato kungiyar mata Musulmi da ake kira da sunan Muslim Sisters Islamic Movement of Nigeria da ke garin Zariya.

Daga cikin 'yan fim da suka halarci wurin akwai shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Mandawari, wanda ya sayi kwafen kaset daya a kan N5,000 a madadin kungiyar da yake shugabanta, Yakubu Ibrahim da kuma Rukayya Umar Santa.

Ita ma jarumar fim din, Malama Jamila, ta yi bayani inda ta ce sun sha wahala sosai wurin shirya Karbala. Ta kuma gode wa Malam Zakzaky da Malam Bala Makosa.

An tashi taron lami lafiya.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin