Musulunci bai kafu ba sai ta hanyar wasan kwaikwayo
Inji Shaikh Yusuf Ali
Daga Wakilinmu a Kano
A KOKARINSA na nuna muhimmanci da halascin wasan kwaikwayo a cikin addinin Musulunci, fitaccen malamin nan mazaunin Kano mai suna Sheikh Yusuf Ali, ya ce duk wani mutum da zai fito ya ce bai dace a yi wasan kwaikwayo ba, to wannan mutum bai fahimci Musulunci ba ko kuma yana da wata manufa daban.
Malamn ya yi wannnan kalamin ne a lokacin da wasu shugabannin kungiyoyin shirya finafinan Hausa suka kai masa ziyarar "neman fatawa da shawarwari" a gidansa da ke Tudun Maliki kusa da gidan adana dabbobin daji (Zoo) da ke Kano a ran 29 ga Maris, 2002.
"Adinin Musuluncin wanda muke yi bai kafu ba, bai karbu ba, har sai da akai wasan kwaikwayo a kansa gaba dayansa," inji Shehin malamin. Daga nan ya fara buga misalai da wasu kissosi, cikin har da kissar wani mala'ika da ya yi shigar mutum ya jaraba wani kuturu, makaho da kuma wani mai kora. Sai kuma wata wadda malamin ya ce Allah ya bada umarni wani mala'ika ya yi shigar mutane ya jaraba wani alkali. Ya kuma kawo ta Annabi Idris (A.S.) da mala'ika.
To wadannan misalai da ya kawo ya ce abu ne kamar wasa amma ya zama gaskiya. Da ya gama bayar da misalan sai ya furta cewa, "In ba a ce Allah ne darakta ba, to wa za a ce?"
Da ya koma kan matsalolin finafinanmu kuwa, Sheikh Yusuf ya ce akan samu mishkiloli a wasu finafinan, musamman ta yadda ake fadar wani abu mummuna "ko don jahili ko don son kai." A nan sai ya yi kira ga masu shirya fim da su rika zaburar da Musulmi kan abubuwan da za su kara karfin gwiwa kan addini.
A kan batun nishadantarwa kuwa, malamin ya ce ko a Saudiyya ana yin wasan kwaikwayo, ya kuma ce akwai wasu abubuwa da Musulunci ya kau da kansa. "A rika kawo mummunan abu a cikin fim don a guje shi, kyawawa kuwa don a koye su,"inji shi. "Shi addinin Musulunci ba daga salla sai azumi ya tsaya ba."
Daga nan kuma ya yi tuni da cewa, "Malaman da suka tattara Hadisan nan irin su Bukhari, idan suka yi bincike suka gaji, za ka ga sun tashi suna tikar rawa, nishadinsu ya dawo, jin dadinsu ya dawo." Wannnan bayani ne da ya yi ya ce kada a yi wata tantama za a iya samunsa a cikin wani littafi mai suna Assunnah Qablas Sadawi na Habib Hujjaj.
Da malamin ya dawo kan 'yan fim sai su ma ya ce, "Mai halwa da sallar dare idan kuka tsara fim da kyakkyawar niyya sai kun fi shi samun lada, ranar lahira sai kun riga shi shiga Aljanna!"
Wadanda suka kai wannan ziyara a wurin malamin sun hada da shugaban kungiyar MOPPAN a arewacin kasar nan, Abdulkarim Mohammed, da shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Ibrahim Mandawari, da shugaban Kungiyar Daraktoci ta Jihar Kao, Tijjani Ibraheem, da kuma Bashir Nayaya (Danmagori). A ziyarar ba a gayyaci 'yan jarida ba sai daga wata sabuwar mujalla da ba ta fara fitowa ba a lokacin, amma a wurin gabatarwa Danmagori ya furta cewa tuni har mujallar ta sami karbuwa.
Tun da farko sai da maziyartan suka bayyana wa shehin cewa suna neman hadin kai sakamakon rashin fahimtar juna da suke fuskanta daga hukuma, masu kallo da kuma wasu daga cikin malamai. Sun kuma yi korafi kan yadda 'yan Hisba ke " kawo cikas" ga 'yan fim a a wasu lokuta.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin