Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 31   Yuli 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Kasimu Yero ya zama

Sarkin 'yan wasa
Gyara kimtsi!Sarki Kasimu Yero
Daga Shafi'u Magaji USMAN a Kaduna

A RANAR Asabar, 8 ga Yuni, 2002 aka nada shahararren dan wasan kwaikwayo din nan Alhaji Kasimu Yero a matsayin sarkin dukkan masu finafinan Hausa na Nijeriya. An yi masa nadin ne a lokacin da ake bikin bai wa wasu shahararru kuma tsofaffin masu wasan kwaikwayo na Arewa lambobin yabo na musamman bisa la'akari da dimbin gudunmawar da suka bayar ga wannan harka. Alhaji Yusuf Ladan, Dan Iyan Zazzau kuma Hakimin Kabala, Kaduna, shi ne ya yi nadin a gaban dimbin jama'a.

Shi dai wannan nadi ya kasance daya daga cikin abubuwan da aka shirya yi ne a bikin wata kungiya mai suna 'Wisdom Promotion Project' a Kaduna da hadin gwiwar hukumar hukumar NTA Kaduna domin karrama su tsofaffin 'yan wasan wadanda yawancinsu sun samu sama da shekaru 30 suna wannan harka. Wadanda aka karrama sun hada da Alhaji Usman Baba Pategi (Samanja), Alhaji Haruna Danjuma (Mutuwa Dole), Alhaji Umaru Danjuma (Kasagi), Alhaji Jafaru Bagudu (hakimin Bomo), Alhaji Sambo Idris Sambo (Hakimin Funtuwa), Alhaji Mustapha (Basabce), Alhaji Yusuf Bagaye (Sarkin Alhazai), Malam Shehu Jibrin (Golobo), Danwanzam Sakkwato, Alhaji Daudu Galadanchi (Kuliya), Malam Abdullahi Shu'aibu (Karkuzu), Alhaji Muhammadu Akawu da Hajiya Mairiga Aliyu.

Sauran kuma su ne Alhaji Ibrahim Abba Gana (Waziri na cikin Magana Jari Ce), Hajiya Rashida Bello, Alhaji Ibrahim Buba (Musa na cikin Magana Jari Ce), Hajiya Rabi Tanko, Hajiya Tabature Dandume, Hajiya Hajara Ibrahim, Alhaji Najume Mohammed (Idon Mujiya), Alhaji Umaru Mohammed Kontagora (Sankira), Alhaji Sani Gwarzo (Tumbuleke), Hajiya Ladin Cima, da Hajiya Rabi Adamu (Bodora).

Akwai kuma wasu hazikan bayin Allah da suka ba da gudunmuwa mai dimbin yawa a harkar wasan kwaikwayo kafin rasuwarsu wadanda su ma aka tuna da su a wannan taro. Wadannan mutane kuwa su ne Alhaji Umaru Ladan Zariya, Hajiya Dala Isa Bakori, Alhaji Uba Gaya (Buguzun) da Hajiya Harira Kaciya.

Ban da wadanda suka kwanta damar, kusan duk wadanda aka karrama sun samu halartar taron, wanda Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kaduna kuma tsohon dan wasan kwaikwayo, Alhaji Muhammad Rabi'u Bako (Gundumi Fasa Kwanya), ya shugabanta. A jawabin kwamishinan, ya yaba wa tsofoffin 'yan wasan tare da bayyana manufar gwamnatin Jihar Kaduna kan yadda take bai wa wasan kwaikwayo muhimmanci a harkokinta.

Da dama cikin tsofaffin 'yan wasan da suka yi jawabai a wurin su bayyana matukar takaicin yadda har yanzu gwamnatocin kasar nan ba su fahimci muhimmancin 'yan fim a harkokinsu ba bare har su tallafa masu. Don haka suka jaddada kiraye-kiraye na neman sa hannun gwamnati a wannan harka yadda ya kamata.

Kafin a kammala taron sai da shi kansa Sarkin 'Yan Wasa Kasimu Yero ya nada wasu da za su rufa masa baya (fadawa). Akwai Malam Yusuf Barau (Magajin Kasimu a Kaduna), Alhaji Ibrahim Mohammaed Mandawari (Magajin Kasimu a Kano), Malam Musa Mohammed Abdullahi (Garkuwan Sarkin Alhazai), A'isha Musa (Garkuwar Tabature Dandume), Malam Musa Yahaya Kwado (Magajin Tumbuleke), Malam Sani Idris Kauru Moda (Magajin Kasagi), Malama Tani Umar (Garkuwar Rashida Bello), da Yahuza A. Ilu (Magajin Salisu Mai Ganaka).

A yayin da yake zantawa da mujallar Fim, Alhaji Kasimu Yero ya koka kan yadda ake yawaita sanya wakokin da ba su dace da al'adunmu ba a cikin finafinan Hausa. Kuma ya yi kira ga matasa da suke cikin wannan sana'a da su yi gwargwadon karfi da kwarewarsu wajen ganin su kara bunkasa sana'ar.

Dab da kammala taron an kaddamar da wata kalanda ta wasu cikin tsofoffin 'yan wasan. Alhaji Maikudi Tela, shugaban Kungiyar Katsinawa da Daurawa Mazauna Kaduna, shi ya kaddamar da kalandar kan kudi N100,000.00. Sai gwamnatin Jihar Kaduna da ta Karamar Hukumar Birnin Gwari ta ba da N50,000 kowace. Akalla an samu kimanin N300,000.00 a wajen kaddammar da kalandar.

Taron, wanda bai samu halartar dimbin jama'ar da aka yi zaton za su cika filin wasan ba, an aiwatar da shi cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wani yamutsi ba.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin