Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 32   Agusta 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
MU LEKA HOLLYWOOD
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Karshen tika-tika tik!

A'isha Musa ta yi miji

Wasan karshe
Wasa ya kare: a'isha tare da Baban Mulika suna cashewa a wani atisaye na bikin al'adun gargajiya a Kaduna

Daga SHAFI'U MAGAJI USMAN a Kaduna

DA misalin karfe 2:55 daidai na ranar Jumma'a, 26 ga Yuli, 2002 aka daura auren shahararriyar 'yar wasan nan da ke Kaduna mai suna A'isha Musa (Shamsiyya) da wani tsohon kwararren dan kwallon kafa mai suna Ali Nayara, wanda ya yi zamaninsa cikin shekarun 1980-1990. Daurin auren ya samu halartar dimbin jama'a, musamman 'yan fim da suka hada da A.A. Kurawa da Shehu Hassan Kano daga Kano, Usman Baba Pategi (Samanja), Abdullahi Maikano Usman, Ashiru Sani Bazanga, Yusuf Barau, Magaji Suleiman, Adamu Bello Ability, Galin Money, Musa Mohammed Abdullahi, Yahuza Ilu da sauransu daga garuruwa daban-daban wadanda ba za mu iya ambato sunayensu ba saboda yawansu.

Shi dai wannan daurin aure ya biyo bayan dadaddiyar soyayyar da ma'auratan suka yi ne har aka rika jefa rade-radin cewar A'isha da Ali yaudarar juna kawai suke yi, amma ba aure za su yi ba. Har zuwa lokacin da aka tsayar da ranar auren, jama'a da dama sun jefa shakku kan yiwuwarsa, musamman ganin cewa akwai wasu matsaloli da ka iya dakile tabbatar auren. Daya daga cikinsu, a cewar wata kwakkwarar majiya, ita ce mahaifiyar A'isha ba ta son a yi auren.

Wakilinmu da ya yi ta kai- kawo zuwa gidan su A'isha a unguwar Kabala Costain cikin kwana bakwai gabanin ranar auren, ya so ya ji dalilin mahaifiyar amaryar kan kiyayyarta da wannan auren. Amma da ya hango irin matsalolin da ke kunshe cikin neman biyan bukatar tasa, sai ya hakura tilas.

Wakilinmu ya so jin gaskiyar wannan magana daga bakin ita kanta A'isha, wadda ake kira Kaduna a gidansu. Ya yi ta fama da ita ta yarda ta yi hira da wannan mujallar amma a koyaushe sai ta nuna aiki ya yi mata yawa, wai ya dawo anjima. A karshe dai ta ki yarda saboda wasu dalilai na kasin kanta wadanda ba ta bayyana ba. Sai dai wata kawarta ta ce A'isha tana tsoron yin magana ne domin tana jin kila mujallar Fim ta yi mata magana kan wani abu da ba ta son a fada. Har bayan daurin auren wanda ya gudana a wani gida mai lamba 16, Madachi South, Jafaru Estate, Costain Club, Kaduna, wakilinmu ya yi kokarin gano inda amaryar take don jin ta bakinta, amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba saboda wai an boye ta, domin ba ta gidansu.

Amma shi angon nata, ya zanta da wakilinmu ana sauran kwana hudu a daurin auren, inda ya bayyana matukar farin cikinsa kan aukuwar wannan aure. Ali Nayara yana da mata biyu kafin aurensa da A'isha, wato ita ce ta uku yanzu, kuma yana da 'ya'ya kimanin guda goma.

A binciken da muka yi, mun fahimcin cewa hatta kannen amaryar ma sun nuna matukar rashin gamsuwa da yin auren a halin yanzu ko kuma da Alhaji Ali Nayara. Wannan dalili ya haifar da wata baraka tsakanin iyalan bisa nacewar da A'isha ta yi kan cewa sai an daura mata auren ko ana ha-maza ha-mata saboda goyon bayan da ta samu daga wasu 'yan'uwa da abokan arziki.

Wani dan wasa a Kaduna, Adamu Danjuma Kinafa, ya nuna farin cikinsa da yiwuwar wannan aure har yake cewa, "A gaskiya na yaba wa A'isha kan wannan al'amari kuma Allah ya yi mata kyakkyawar sakayya."

An dai daura auren 'yar wasan 'yar shekara 31 da haihuwa lami lafiya kan sadaki na N20,000. Washegari an yi gala a dandalin 'Ranchers Bees' sa'annan aka yi kwallo. Tsarin ya burge jama'a matuka. Mu a Fim muna yi wa ango da amarya fatan Allah ya yi wa wannan aure albarka kuma ya kawo fahimtar juna a tsakaninsu da wadanda ba su so a yi auren ba.

Mun kyautata sunna ne da wannan auren

-Ali Nayara

Ango Ali Nayara, ya bayyana farin ciki kan aurensa da shahararriyar 'yar wasan:

Fim: Alhaji Ali Nayara, bayan tsawon lokaci da kuka dauka kuna soyayya da A'isha sai ga shi a yau Allah ya kawo lokacin da za ku yi aure. Ya kake jin wannnan al'amarin a zuciyarka?

ALI NAYARA: A gaskiya ina matukar farin ciki da Allah ya kawo lokacin aurena da A'isha. Saboda akwai mutane da yawa da suke zaton yaudararta nake, ba aurenta zan yi ba. Ita ma ta bangarenta akwai mutanen da suke ambaton yaudarata kawai take yi ba aurena za ta yi ba. Amma cikin yardar Ubangiji har mun zo ga raya sunnar Annabi (SAW).

FIM: Shin bayan wannnan aure za ta ci gaba da aikinta da kuma harkar fim?

NAYARA: A gaskiya game da wasannin kwaikwayo ba za ta ci gaba ba domin addininmu bai yarda mace ta fita waje tana wasanni da mijin da ba nata ba. Haramun ya shigo cikin wannan. Amma in ba ta da aure tana iya yin abinta. Amma aikinta na ofis za ta iya ci gaba da shi. Kodayake ko a ofis din nasu, kamar raye-rayen da suke yi za mu kauda dukkan wadannan bidi'o'i gaba daya.

FIM: Tunda ba za ta ci gaba da yin fim ba, ya za ka fuskanci matsalolin masoyanka a wannan bangare da za su rika kokarin ziyartarta bayan ta yi aure?

NAYARA: Ita wannan matsala a gaskiya akwai ta, don tana faruwa. Amma ba a iya janye mutane a lokaci daya, komai na rayuwa sai a hankali. Ni kaina dan wasa ne, na yi wasan kwallon kafa da ya janyo mani masoya maza da mata. In irin wannan ta kasance sai hakuri, ba dai za ka iya raba mace da mace 'yar'uwarta ba. Amma in har namiji ne da matarka ta aure, to dole ne ka tsawatar a kai.

FIM: Cikin bukukuwan wannnan aure har akwai wasan kwallo kafa tsakanin 'yan wasan fim na Kano da Kaduna. Me ya sa aka tsara yin kwallo maimakon yi gala don taya ku murna?

NAYARA: E, to batun yin kwallo ni na kawo masu idea din, kuma suka gamsu (masu shirya bikin). Abin ba ya sa ni dai na yi zamanina a kwallo, ita kuma ta yi nata a dirama, yin wannan kwallo ka ga mun tabo waje biyu, 'yan diraman nan su ne suka taya ta buga wannan wasa, ni kuma a fannina an buga mani kwallo. Ka ji dalilin yin kwallo maimakon Galan nan da aka saba yi, don komai yana son canji.

FIM: Akwai masu tunanin mata 'yan fim ba su cika sha'awar yin aure ba, ko kuma in sun yi auren ba za su iya zama ba. Sai ga shi a yanzu muna ganin da yawansu kuma shahararru suna yin auren kuma su zauna. Menene shawararka ga masu irin wancan tunani?

NAYARA: Wato abin da nake so in ba da shawara ga mu maza, duk 'yar wasan kwaikwayo da za ka nema da aure sai fa ka dauki hakuri da duk irin abin da za ka gani. Kai dai ka yi kokari ka raya wannan sunna da ka zo dominta. In kuwa har ka ga mutum yana neman 'yar wasa da aure amma ya dinga zarge-zarge, to da ma ba ya zo don Allah ba ne don ya aure ta, ya zo da wata niyya tasa ta daban.

FIM: A'isha ba ita ce mata ta farko a gare ka ba, akwai wasu biyu kafin ita. Ko za ka iya gaya mana yadda ka tsara zamanku?

NAYARA: A gaskiya ba zan tara su waje daya ba a yanzu. Annabin rahama ya ce in kana da wadata dukkan matanka kowace ka sama mata gidan kanta, ba sai ka hada su waje daya ba. In kuma Allah ya yi nufin da in hada su waje daya nan gaba sai in hada su.

FIM: A karshe menenen kiranka ga kawaye da abokan aikin A'isha mata da ba su kai ga wannan matsayi ba?

NAYARA: Ina son don Allah ko wace ta yi aure, ta daina hangen dan abin da take samu din nan a harkar fim. Zaman aure ya fi komai muhimmanci ga 'ya mace; shi kuwa arziki nufin Allah ne, ko mace tana dakinta sai Allah ya azurta ta.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin