Magana ta kare:
An daura auren A'isha Ibrahim da Oumaten Atta
Daga ALIYU ABDULLAHI GORA II da SHAFI'U MAGAJI USMAN a Kaduna
RANAR Asabar, 17 ga Agusta, 2002, rana ce ta farin ciki ga fitacciyar jaruma A'isha Ibrahim (Saliha) da angonta dan kasuwa mazaunin Amerika, Malam Oumaten Atta, domin a ranar ne aka daura aurensu a Kaduna. An daura auren da karfe 10:40 na safe a kan sadaki N20,000 a gidan su A'isha da ke Layin Argungu. Jama'ar arziki da dama sun halarta, musamman masoya jurumar ta finafinan Saliha? da A'isha.
Duk wannan ya biyo bayan watannin da aka dauka ba a yi auren ba tun lokacin da mujallar Fim ta bayyana wa duniya a watan Janairu na bana cewa za a yi shi a cikin kankanen lokaci.
Yawancin 'yan fim ba su halarci daurin auren ba. Daga Kano, Ibrahim Mandawari da Hauwa Ali Dodo (Biba) ne kadai suka zo. Sa'annan duk da yake 'yan fim na Kaduna da dama sun halarta, amma furodusoshi biyu kadai ne a cikinsu - Sakataren Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Abdullahi Maikano Usman, da kuma Rabi'u Koli. Daga cikin fitattun 'yan wasa kuma Sani Idris Kauru (Moda) ne kawai ya halarta, shi ma bayan an gama shafa addu'a. Wakilinma sun ji wasu 'yan fim suna korafin cewa su ba a gayyace su ba shi ya sa suka kaurace wa daurin auren, wasu kuma suka ce sun kiyayi zuwa ne saboda sun gani a jikin katin gayyata an rubuta 'Stricktly on Invitation,' wato sai wanda aka ba kati kawai ake son gani a wajen. "Muna tsoron aukuwar irin wulakancin da aka yi wa jama'a a bikin Abida Mohammed," inji wani da ya ce mu sakaya sunansa.
Angon, dan shekara 39 da haihuwa, Oumaten Atta, wanda sunansa na ainihi Abubakar, dan kasar Nijar ne kuma dan kabilar Buzaye. Shi ma bai samu halartar daurin auren ba daga Amerika, sai dai waliyyansa sun zo daga Nijar. Sun hada da mahaifinsa Malam Usman ibn Hammada, wanda babban malami ne, da kuma wan ango, Abdurrahman Usman, wanda babban mai shari'a ne a kasarsu, sai kuma wasu mutum biyu ciki har da kanen angon.
Oumaten Atta ya aika wa jama'a sanarwar auren ne ta hanyar intanet, ta cikin zauren tattaunawa kan finafinan Hausa wanda Furofesa Abdalla Uba Adamu da Ibrahim Sheme suke gudanarwa, kwanaki kadan kafin a daura auren. Membobin zauren sun a'aika da sakonnin taya murna ga ango da amaryar ta cikin intanet.
Koda yake an ce rashin zuwan angon abin damuwa ne ga ita amaryar, mun ji cewa da ma tana sane ba zai zo din ba. "Da a ce tai ta zama hakanan bayan labarin da aka yada ai gwamma a daura din ko ma dai yaya ne," inji wata kawar amarya.
An dai daura auren kawai, bikin tarewa kuma sai nan gaba. Allah ya ba da zaman lafiya, amin.
A'isha Ibrahim
|
RA'AYOYIN IYAYEN ANGO DA AMARYA:
ALH. BELLO ADO BALA, wan amarya:
FIM: Menene ra'ayinka dangane da wannan aure na kanwarka?
ALH. BELLO: Wannan lamarin a wannan babbar rana, alhamdu lillahi, don ko wa yake da kanwa ko 'ya yana fatan ya ga yadda za ta karashe rayuwarta a gidan mijinta. Don abin da duniya take ciki a yau ya fara zama abin tsoro: muna da yara mata, yawanci auren da ake nema ba a samu an yi ba.
Saboda haka wannan lamarin da ya faru abin farin ciki ne a gare mu.
Menene ra'ayinka kan aure da ta yi a Nijar?
BELLO: Ai Nijar da Nijeriya duk daya ne, kuma ai Musulmi dan'uwan Musulmi ne - ko fari ko baki - duk daya muke wurin Allah.
Wace nasiha za ka yi masu?
BELLO: Su yi hakuri da junansu, kuma su tsare gaskiya da fahimtar juna. Muna taya su addu'a da farin ciki, da fatan su samu zaman lafiya.
*
ALH. MUHAMMADU KABIR HARUNA DANBIRNI,
Kanen mahaifin A'isha:
FIM: Baba, za mu so mu ji fatanka game da auren wannan 'yar taka.
DANBIRNI (bayan ya yi sallama tare da doguwar addu'a da Larabci): Wannan rana ce da ni a rayuwata ban taba samun irinta ba. Kusan ina iya cewa na yi gamo-da-katar a rayuwata, domin a tsakanin 'ya'yan da na haifa da na 'yan'uwana, ita (A'isha) ita ce ta 79 da muka aurar a yau. Amma ba mu taba yin irin wannan ba. Domin wadanda suka shude da 'ya'yan 'yan'uwa muke hadawa - wa na da mace kane na da namiji, sai a hada su. Amma ita A'isha sai ta yi dogon zango, ta fada kasar Shehu Dahiru na birnin Agadas, wanda ya nemi mujaddadanci tare da Shehu Usmanu. Don haka ta fada wuri mai darajar gaske, wanda ya sanya ni farin ciki har nake mata fatan Allah ya albarkace ta da zuriya cikin wannan jinsi na mutane. Domin mutane ne masu asali da dukiya da sana'a da kuma ilimin addini.
Wace shawara za ka ba ma'auratan?
DANBIRNI: Ni a nawa ba maganar shawara, sai rike carbi da fuskantar alkibla ta hanyar kai kukana ga Wanda ya halicce mu baki daya. Allah ya hada fuskokinsu, ya tsare masu shaidan, ya kiyaye su daga sharrin duniya. Allah ya hada fuskokinsu su zama magada juna.
*
ALH. ABDURRAHMAN USMAN, wan ango
FIM: Muna so mu ji dangantakarka da angon.
ALH. ABDURRAHMAN: Sunana Abdurrahman, babana kuma sunansa Usman. Matsayina kuwa a Nijar (shi ne) Chief Judge. Shi kuma Abubakar (wato ango Oumaten Atta) kanena ne wanda ya sanyo mu mu zo kamar yadda ya dauki alkawari da A'isha na mu zo a daura masu aure. A kan hanyarmu daga Niamey (Yamai) muka kwana Kwanni, kuma a jiya muka iso da misalin karfe 7 na yamma ni da babanmu da kuma wani kanenmu ga shi nan zamne.
Kasancewar wannan aure ne da ya shafi kasa da kasa, ya kake ji in da za a ci gaba da yin irinsa?
ABDURRAHMAN: To, ai ka san irin wannan, ba mamaki gare shi, don ka san ita duniya yadda Allah ya yi ta babu bambanci. Sanin Nijeriya da Nijar wannan ilimin mutane ne, mutane suka kawo bambanci. Shi harkar so da kuma harkar rabo ba ya da iyaka; kana Amurka in rabonka yana Kaduna dole ka zo ka yi auren a nan. Don rubutacce ne, inda Allah ya rubuto maka nan za ka zo. Shi ne Hausawa suke cewa matar mutum kabarinsa. Kuma lokacin da muka zo al'amuran da muka saba gani a can Nijar su ne muka tadda a nan. Kenan al'adodi da zumunci da komai ba su canza a gare mu ba. Mutanen wajen A'isha sun karbe mu da hannu goma, mun ji dadi. Kuma muna masu godiya tare da sauran 'yan Nijeriya tunda ba a nuna mu baki ba ne daga wata kasa.
Me ya burge ka game da 'yan Nijeriya da suka halarci wannan daurin auren?
ABDURRAHMAN: To, ni abin da ya fi burge ni shi ne hulda. Na ga duk mutanen da muna gani cikin fim, wadanda suke wasa da ita A'isha - kamar Ibrahim Mandawari da wasu wadanda ban iya saninsu duka - duka sun zo. Don ba ka sanin masoyinka sai irin wannan ta zo. Don haka abin da mun ka gani mun ji dadi kwarai.
Kamar yadda dan'uwanka ya auri 'yar Nijeriya, kana jin kai ma in ka samu za ka iya aura?
ABDURRAHMAN: Yanzu in kun ba ni sai in dauka! Yanzu-yanzun nan! Ai wasan kwaikwayo ba wani abu ba ne. Wani al'amari ne wanda addinin Musulunci bai hana ba, in dai ba a barna a ciki.
Wane kira za ka yi ga ango da amarya?
ABDURRAHMAN: To shi Abubakar na san shi, malami ne masanin Alkur'ani. Kenan duk abin da ya biyo na mace ga hakkin aure duk ya sani. A'isha ita kuma babana da ya samu gaisawa da ita - don ni ban gan ta ba har yanzu - ya ga yarinya ce mai hankali da da'a, ga kuma son addini gare ta. Ina ganin duk wanda son addini yake a zuciyarsa, ba sai ka ce masa ka yi haka ka yi haka ba. In dai mutum yana da imani da tsoron Allah ai shikenan. Mace ta san hakkin mijinta, miji ya san hakkin matarsa. Ni dai abin da kawai zan ce (shi ne) Allah ya kau da shaidan a tsakaninsu, kuma ya ba su hakuri. Kuma muna fata yadda ta saba da mutanenta a nan kada wannan aure ya kau da zumuntarta da 'yan'uwanta.
*
MALAM USMAN IBN HAMMADA, uban ango:
Baba, muna so ka tofa albarkacin bakinka kan wannan aure.
MALAM USMAN: Farin cikin da zan nuna kan wannan aure ya yi yawa kwarai. Don da rani ma na zo nan, na ji dadin zuwa, na ga mutane duk sun yi mani maraba. Kuma na gode masu kwarai. Kuma ina ganin halin yarinyata mai kyau ne.
Kamar yadda danka ya samu auren 'yar wasan kwaikwayo a nan Nijeriya, shin kai ma za ka iya ba da 'yarka ga dan wasa?
M. USMAN: Wannan ba mamaki; ko yau ya bide ta sai in ba shi, tunda akwai su kuma suna murnar Nijeriya kwarai.
A karshe, kana da wani kira da za ka yi ga ango da amarya?
M. USMAN: Shawarata gun su (ita ce) su yi zaman alheri da juna. Allah shi ba su zama mai lafiya kuma a kan addini.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|