Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Ra'ayi Ba Gaba Bane
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection


Yadda Idris Danzariya ya zama sabon shugaban masu sayar da kaset

Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA a Kano

Idris Danzariya
Idris Danzariya

RUWAN da aka rika zukawa tun da misalin karfe 7:00 na safe har zuwa 9:30 bai hana dimbin 'ya'yan kungiyar masu sayar da kaset na bidiyo da rikoda na Jihar Kano zuwa wurin zaben sababbin shugabanninsu ba. Ana dauke ruwan, jama'a kamar jira suke yi, sai suka rika yin tururuwa suna nufa gidan sinima na Oriya da ke bakin Kasuwar Kofar Wambai inda a can ne aka gudamar da wannan zabe a ranar Lahadi, 8 ga Satumba, 2002.

Da farko 'yan takara uku suka nemi kujerar shugabancin kungiyar, amma ana gab da ranar zabe sai Malam Tukur Kofar Wambai ya janye ya bar Alhaji Idris Danzariya da Alhaji Isma'ila Ibrahim T.M. Wadannan 'yan takara guda biyu sun yi ta yakin neman zabe haikan kafin zuwan ranar. Wakilinmu ya sha ganin Danzariya ya je kamfen a cikin Kasuwar Kofar Wambai inda can ne babbar matattarar masu sayar da kaset na rikoda.

Wannan zabe ya dauki hankalin jama'a da dama musamman garin irin yawan jami'an tsaron da aka jibge don hana 'yan hauma-hauma yi wa zaben kafar ungulu. Tun kimanin karfe 11 na safe gidan sinimar ya cika da jama'a inda wasunsu da dama sababbin dinkuna suka sanyo. A cikin sinimar, an kafa rumfa inda aka ware manyan iyayen kungiya da yawa a ciki, kamar su Alhaji Badaru Rawayau, Alhaji Yakubu Matazu, Alhaji Hassan Adamu, Alhaji Adananu Miloniya, Alhaji Musa Na Malam Kato, Alhaji Musa Na Sale, Alhaji Muhammadu Kalarawi, Alhaji Ibrahim Waca-Waca da Alhaji Tukur Bada.

Zabe biyu ne aka gudanar, wato na shugaba da kuma mataimakin shugaban na biyu. 'Ya'yan kungiyar sun amince cewa wanda aka kada tsakanin Danzariya da Isma'ila to shi ne zai zama mataimakin shugaba na daya. Alhaji Lawali Mohammed Dan Sakkwato da Alhaji Kabiru Mohammed Rawayau su ne suka fito a matsayin 'yan takarar mataimakin shugaba na biyu. Shi Alhaji Kabiru Rawayau shi ne shugaban masu sayar da kaset "kan Alpha" - wato masu sayarwa a kan keke da babur. Ba mamaki shi ya sa 'yan Alpha suka ajiye kekuna da babura suka tsaya wurin zabe. Dukkan sauran mukaman kuwa an ci su ba hamayya.

Bayan an kawo kayan aiki kuma malaman zabe sun bayyana, sai shugaban shirya zabe, Alhaji Garba Ja'oji, ya yi wa jama'a takaitacen bayani kan zaben inda ya nuna cewa mukamai biyu ne kadai za a yi takara kansu - na shugaba da na mataimakin shugaba na biyu. Daga nan sai daya daga cikin manyan masu sayar da kaset na rikoda, Alhaji Aminu Kankana, ya yi wa jama'a nasiha da su yarda da wanda duk Allah ya bai wa rinjaye kan abokin takararsa. Ya yi wannan jawabi ne kuwa yayin da yake tsaye tare da 'yan takarar shugaban su biyu.

Karfe 11:25 daidai aka rufe kofar shiga cikin sinimar domin fara zabe. An umurci jami'an tsaro wadanda suka hada da 'yan kato-da-gora dauke da makamai da kada su bari kowa ya kara shigowa. Da karfe 11:45 aka fara kiran sunaye ana zuwa ana kada kuri'a, wanda zaben sai da ya kai har karfe 2:10 na rana.

An fara kirga kuri'u kenan sai ruwa ya sake gocewa wanda ya sa tilas aka sake wuri, aka koma cikin rumfa. Ba a yi wata-wata ba kuwa aka kammala kidayar da misalin karfe 3:40 na yamma, sai aka bayyana sunayen wadanda suka ci.

Alhaji Idris Danzariya ya sami kuri'u 178 yayin da Alhaji Sama'ila T.M. ya samu 141. A mukamin mataimakin shugaba kuwa, Alhaji Kabiru Mohammed Rawayau ne ya kada Alhaji Lawal Mohammed. Kabiru ya samu kuri'a 160, shi kuwa Lawal ya samu 133.

Sakamakon zaben ya nuna jerin sababbin shugabannin kamar haka: Idris Mohammed Danzariya - Shugaba; Isma'ila Ibrahim T.M. - Mataimakin shugaba; Kabiru Mohammed Rawayau - Mataimaki na biyu; Alhaji Musa Na Malam Kato - Ma'aji; Alhaji Ahmed Moh'd Amge - Sakatare; Isma'ila I.U.I. - Sakataren Kudi; Alhaji Sani Lamma - Jami'in hulda da jama'a, sai Sanusi Bala - Mataimakin Sakatare.

Daga cikin wadanda suka sa ido a wurin gudanar da zaben akwai wakilai daga wurare kawar CIB, SSS, Z11B da CID na Kano, Akwai kuma wakili daga Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, da Hukumar Al'adu da Tarihi ta Kano da Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya wadda mataimakin darakta Mista Bernard Boyit ya wakilta, sai wakilin kwamishinan 'yan sanda.

A gaban 'yan takara aka kirga kuri'un, kuma aka bayyana sakamako. Dukkansu kuwa sun amince da sakamakon, sun kuma sa hannun amincewa. A karshe an raka sabon shugaba har babban kantinsa da ke El-Duniya tare da motoci biyu makare da jami'an tsaro.

Duk wanda bai yarda da ni ba bai da gaskiya

-Danzariya

Jim kadan bayan tawagar magoya bayansa da jami'an tsaro sun raka shi kantinsa, sabon shugaban ya dan samu natsuwa inda ya yi 'yar takaitacciyar tattaunawa da wakilinmu:

Fim: Mujallar Fim na yi maka murna da wannan nasara da ka yi.

DANZARIYA: To madalla. Na ji dadi da wannan murna wadda ake yi min.

Me za ka ce kan wannan nasara da ka yi?

DANZARIYA: Alhamdu lillahi na yi farin ciki da wannan nasara. Na yi wa Allah godiya da kuma jama'a baki daya.

Lallai ka gaji wani jan aiki daga shugaban da ya sauka kai kuma ka hawo.

DANZARIYA: Shugabanninmu na baya sun yi iya kokarinsu. Na ga jan aikin da suka yi. Ka san shi dan'adam ba a iya masa. Daga cikin abin da ya wahalar da shugabancin na bayanmu shi ne yadda mutane kan daukar masu alkawari daga baya kuma sai su warware.

Wane shiri gare ka na gyaran matsalar kasuwar kasakasan finafinan Hausa domin furoduoshi da ku 'yan kasuwa a sami sa'ida?

DANZARIYA: Muna nan za mu fito da tsari don kawo gyara. Ya kamata mu da su furodusoshin mu zauna mu fito da hanyoyin gyara don ci-gabanmu.

Wasu furodusoshi na yi maka kallon wani mai ra'ayin rikau wanda in ya tsaya kan abu daya ba mai iya lankwasa shi. Don ba za a manta da rikicinku da furodusoshi ba a bara.

DANZARIYA: Duk furodusan da bai yarda da ni ba to bai da gaskiya. Ai da ina kawo rudu da ba a zabe ni ba. Me ya sa aka ba ni shugaban tsaro can baya? Ga shi kuma aka zabe ni shugaba yanzu? Ni tsarina ba na neman batawa ba ne, na gyara ne. Ba na neman tauye hakki ko cusguna wa kowa. Ina kira ga wanda bai san Idris Danzariya ba to ya zo ya same ni, idan yana da wata shawara sai ya bayar, amma ba a koma bayan fage ana zagina ba.

Wane kira za ka yi wa wadanda za ka ja ragamar shugabancin tare da su?

DANZARIYA: Kirana shi ne su zauna mu hada kan mutane, a taimaki wanda matsala ta kaddara ta aukawa. Da shugaba da mai yawo da kaset a hannu duk daya muke. Ina maraba da wanda zai zo ya ba ni shawara, idan na yi kuskure kuwa, sai a yi min gyara, don aikin ba karami ba ne.

Shekara nawa za ku yi?

DANZARIYA: Idan da tsawon rai za mu yi shekara hudu daidai.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin