A WANI yunkuri don ceto al'ummar Hausawa daga ramin da ake gani sun fada har aka tafi aka tsere masu, shugaban Kungiyar Tuntubar Juna ta Arewa (ACF) kuma dan takarar zama shugaban kasa a karkashin jam'iyyar MDJ, Alhaji Muhammadu Dikko Yusufu, ya yi taro da wasu jigajigan harkar fim don nuna aniyarsa ta yin amfani da finafinan Hausa wajen wayar da kan jama'a.
An yi wannan taro ne a ranar 23 ga Fabrairu, 2003 a dakin cin abinci na otal din 'Tahir Guest Palace' da ke Kano. Kafin M.D. Yusufu ya fara jawabinsa, sai da tsohon shugaban Kungiyar 'Yan Jarida ta Kasa (NUJ), Malam Sani Zorro, ya gabatar da M.D. din inda ya dan bayyana matsayinsa na can baya da dimbin jama'a suka manta. Ya ce M.D. Yusufu marubuci ne na tun dauri. A nan ne ya tunatar da 'yan jarida da marubuta labaran fim cewa M.D. Yusufu yana daya daga cikin membobin hukumar tace luggar Hausa, kayyade sharuddan rubutu da kuma tsaida karbabbiyar Hausa da aka kafa a cikin 1965.
Da ya tashi yana nasa jawabin, Alhaji M.D. Yusufu, wanda ya taba rike mukamin sufeto-janar na 'yansandan Nijeriya (I.G.), ya bayyana cewa wannan yunkuri da yake yi sam ba shi da nasaba da yakin neman zaben da yake yi na shugabancin kasar nan. Ya lura da cewa tarbiyyar matasa a kasar Hausa ta kai gargara a fagen lalacewa. Dalili kenan ya fahimci harkar fim ce kadai za a iya sanyawa a gaba don cin nasarar wannan gagarumin aiki, inji shi.
Ya kara yin tuni da cewa ya yi amanna da cewa da harkar fim aka fi saurin cin kasa da yaki ta hanyar shigo masu da bakin dabi'u, akidu da kuma karkatar da hankulansu. A nan sai ya shawarci 'yan fim da su fito da wata kwakkwarar hanyar yin nagartattun finafinai da za a iya yin amfani da su don tarbiyya da kara himma ga matasa.
Har ila yau, dan takarar, wanda ya yi gwagwarmaya don ganin bayan mulkin soja a zamanin Abacha ya bayyana takaici kan yadda gwamnatin tarayya ta yi watsi da masu shirya finafinai ta yadda ba ta saka su cikin hukumar nan ta wayar da kan 'yan kasa ba, wato National Orientation Agency. Ya ce, "Ai ta hanyar fim ne aka fi saurin wayar wa da jama'a kansu."
Ganin cewa "duk duniya babu al'ummar da ta san ciwon kanta da za ta yi wasa da kafar finafinai," sai M.D. Yusufu ya tabbatar da babbar murya cewa, "Ni a kashin kaina a shirye nake in na ga hali ya yi in rika daukar dawainiyar yin finafinai da suka ginu a tushen da na zayyana a baya". Yin haka ne ya ce zai ba da tasa gudunmuwar don "fitar damu daga cikin kangi na jahilci da muke ciki, mu tashi tsaye don sauran kasashe su rika girmama mu," inji shi.
Bayan ya gama jawabinsa ne kuma sai Malam Sanusi Shehu Daneji, marubuci kuma sanannen dan jarida, ya mike ya nuna godiya ganin cewa yanzu iyaye kuma dattawan Arewa sun fara nuna sha'awar gina wa harkar finafinan Hausa bangon jingina. Ya kuma kara yin bayani kan yadda aka bar Bahaushe a baya ta yadda babu komai a gabansa sai "sharholiya da kokarin neman kudin kara aure."
Ya kuma nuna yadda kasashe irin su Indiya, Amerika da Japan suka yi amfani da finafinai suka cimma kudirori masu yawa, cikinsu har da na tattalin arziki. Shi ma Malam Yusuf Adamu, wanda marubuci ne a mujallar Ihsan, ya nuna jin dadin wannan rana ta samun babban jagora kuma dattijo a harkar fim.
An yi wasu bayanan da dama a wurin. Shugaban kungiyar MOPPAN ta Arewa, Alhaji Abdulkareem Mohammed, ya nuna cewa harkar fim kafa ce mai bukatar FADI SONKAfawa don ilimantar da jama'a. Ya yi kira a rika kiran masu harkar fim don neman kawo gyara. Abdulkareem ya yi kuka da cewa wata matsala da 'yan fim ke fuskanta ita ce yadda jama'a ba su kallon gudunmuwar da suke bayarwa, sai dai a rika yi masu bi-ta-da-kulli da wasu abubuwa. Sai ya yi roko da a rika yi wa harkar fatan alheri.
Shi kuwa shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama, tashin farko yabo ya yi ga Katsinawa kan yadda suka yi fice wajen FADI SONKAbar harkar fim. Sai ya yi nuni da Alhaji Abdu Haro Mashi wanda shi ne kashin bayan kafa kungiyar furodusoshin Arewa a Katsina. Ganin cewa Alhaji M.D. Yusufu wanda shi ma Bakatsine ne ya shigo a cikin harkar yanzu, sai Iyan-Tama ya ce lallai tilas a yabe su.
Shi ma shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Mandawari, ya yabi Katsinawa kan yadda suka dauki harkar fim da muhimmanci. Sai dai kuma ya yi nuni da cewa ba za a samu ci-gaba a arewa ba sai an jefar da kin yarda da juna. "Sai Bahaushe da Bafillatani sun yarda cewa duk daya suke, sai kuma mun daina yin halin gaiwa na cin kanmu da kanmu", inji shi.
Wannan taro dai Malam Sani Zorro ne da mataimakin editan Al-Mizan, Malam Danjuma Katsina ne suka yi hidimar gudanar da shi. Tun da farko kafin a fara sai da aka ci abinci aka koshi. Bayan an kammala kuma M.D. Yusufu ya gana da wasu 'yan fim da suka hada da Abdulkareem Mohammed, Hamisu Iyan-Tama, Ibrahim Mandawari, Bala Anas Babinlata, da Hajiya Umma Ali, inda suka tattauna kan hanyoyin da zai iya bi na shiga ya agaza wa shirin fim. Daga cikin wadanda suka halarci taron har da Alhaji Saleh Jambo (ya bada uzuri ya fita), da Shugabar Kungiyar furodusoshi Mata, Hajiya Umma Ali, da Sakataren Kungiyar Furodusoshin Jihar Kano Alhaji Baba Shariff, da sauransu.
'Yan jarida marubuta labarai a mujallu sun hada da wakilai daga Tauraruwa, Fim, Garkuwa, Marubuciya, Ihsan, Nishadi, da Al-Mizan. An tashi taron da misalin karfe 10:30 na dare.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin