Sabuwar furodusa AISHA TIJJANI tana so matan da ke shirya finafinai su hada kansu, kuma su guji hassada, don samun ci gaban junansu
WANNAN ba zamani ba ne na shigar raggaye cikin sana'ar shirya fim. Dole ka san abin da ka taka. Dole ka yi bajinta, ka rufe ido, ka ba naira kashi don samun aiki karbabbe. Babu maneji. Babu fargabar wai kila kasuwa ta yi kasa. Wannan aiki sai jan gwarzo.
Ko kuma mu ce "jar gwarzuwa". Kila kirarin da za mu yi wa HAJIYA A'ISHA TIJJANI kenan, Babarbariya wadda ta sako kafa cikin industiri da zummar shirya finafinai masu burgewa. A'isha, wadda daliba ce yanzu a Jami'ar Maiduguri, tana da sha'awar fim, don haka har ta shirya guda biyu; daya na siyasa ne, wato Mala Ta-zarce, wanda aka yi don taimaka wa Gwamnan jiharsu ta Borno ya zarce da mulki. Sai dai kash!, bai zarce din ba. Na biyun, sunansa Ta Bayyana, wanda zai fito kwanan nan.
Kwanan nan Hajiya A'isha ta yi wata tafiya zuwa garin Kaduna, inda suka hadu da Mataimakin Editanmu, ALIYU A. GORA II, wanda ya waiwaye ta kan batun shigowarta wannan fage mai wuyar sha'ani, da burinta a fagen, da sauran al'amura. Ga yadda ganawar tasu ta kasance:
FIM: Hajiya, mai karatu zai so ya fara da sanin tarihinki a takaice.
A'ISHA: Ni dai sunana Hajiya A'isha Tijjani. An haife ni a garin Maiduguri a Jihar Borno. A can na yi makaranta na kare firamare har sakandare. Yanzu haka ina karatu ne a Jami'ar Maiduguri.
FIM: Me ya jawo ra'ayinki kika shigo sana'ar shirya fim?
A'ISHA: Wallahi ni dai sha'awa ce kawai ta sa ni har na shiga harkar fim. Kuma ga shi Allah ya sa na yi dace har na shirya finafinai guda biyu.
FIM: Finafinan da kika shirya din sun fito ko suna kan hanya?
A'ISHA: A yanzu dai daya ne ya fito, daya kuma yana kan hanya.
FIM: Menene sunayen finafinan naki?
A'ISHA: Na farko dai fim din da aka shirya, ka gane, na farkon shi ya dawo na biyu. Don an samu matsala ba a ci gaba da fim din ba. Sai da aka zo aka yi na biyu ya fito sannan aka samu damar kammala na farkon. Na farkon sunanshi Mala Ta-zarce, wanda aka yi wa gwamnan Borno. Na biyun kuma sunanshi Ta Bayyana. Da, sunanshi Bayyana, sai wani ya shirya fim da suna Bayyana, sai muka canza namu ya koma Ta Bayyana.
FIM: Wanene daraktan fim din?
A'ISHA: Ibrahim Mandawari ne.
FIM: Kafin ki shigo wannan harka, kin samu wata gudunmuwa ne ta kudi daga gwamanti ko wani mutum, ko da ma a shirye kike da kudin kanki kika shirya fim?
A'ISHA: A'a, kudin kaina ne. Ni na shirya abuna, ba wanda ya taimake ni.
FIM: Kafin ki shigo kin nemi shawarar wani ne daga cikin wadanda suka dade a cikin sana'ar ta shirin fim?
A'ISHA: Ni dai ba wanda ya ba ni shawara, kawai dai na sa kaina ne. Na zo kuma na samu Mandawai, shi ya yi mani.
FIM: Kwangila ke nan kika ba Mandawari?
A'ISHA: E, kwangila na ba shi mana.
FIM: To Hajiya A'isha kin zabi sana'ar shirin fim ne don ki samu hanyar samun kudin shiga, ko dai kina da wata manufa daban?
A'ISHA: Ni dai don sha'awa ne. Kuma in samu riba. Na dauke shi kamar bizines ne.
FIM: Kamar yadda wasu furodusoshi ke kukan cewa kasuwar finafinai ta lalace, wannan bai karya maki kwarin gwiwa ba?
A'ISHA: Bai karya ba. Don ko fim dina da na fitar Gwamna ne ya saya kuma da kudi masu dan kauri ya saya. Ban samu wata matsala ba.
FIM: Me ya sa ba ki tallata fim din ba jama'a suka san shi?
A'ISHA: Ban tallata ba gaskiya amma na biyun zan tallata shi sosai.
FIM: Akwai kungiyar furodusoshi mata a nan Jihar Kano. Kkin yi rajista da su?
A'ISHA: E, na yi rajista da su. Don da na je, wannnan,… ba ni aka samu ba, a H.R.B ne Aminu ya ce ana neman sunayen furodusoshi mata, to sai ya ba da sunana. Daga baya ne ma yake gaya mani.
FIM: A matsayinki na sabuwar furodusa, akwai matsalolin da kika fuskanta kafin a gama daukar shirin finafinan naki?
A'ISHA: E, na samu matsaloli amma a fim dina na farko ne. Ka san fim din da aka je yi, komai abinka da za ka yi na farko dole sai ka samu matsala. An je shutin a Maiduguri, to a lokacin na shirya na ce tunda za a je ana son kallon 'yan wasa a Maiduguri, a shirya gala. To har na ba da kudin gala aka zo aka yi, sai na samu matsala, abin ya baci. Sai ya kasance har kudin da zan kara a ci gaba da fim din babu. Sai da aka dakatar, na zo na yi fim na biyu, sannan na zo aka ci gaba da fim din.
FIM: Kafin ki shigo industiri har ki yi tunanin shirya fim, kina da masaniyar ko nawa ya kamata a tanada kafin a shirya fim?
A'ISHA: Gaskiya ban taba sani ba.
FIM: To ke nawa kika tanada kafin ki shirya naki?
A'ISHA: Kai, na kashe kudi da yawa…(ta yi dariya)
FIM: Da fim dinki na farko da na biyun wanne ya fi cin kudi?
A'ISHA: Na farkon ya fi cin kudi. Ka san komai abin da za ka yi na farko dole ka samu matsala. Amma da aka zo aka yi na biyun a gaskiya ban kashe kudi kamar yadda na kashe a na farkon ba. A gaskiya, fim dina na fara a farko ya ban wahala, don duk abin da ba ka taba yi ba, a farko dole ya ba ka wahala. Amma da na zo na biyu bai ban wahala kamar na farkon ba. Kuma babbar matsala da na samu shi ne na hada fim da gala a lokaci daya, hankalina ya rabu kashi biyu. Sai na yi asara a gala, inda har daraktana ya tausaya min, ya ba ni shawara na kara wani abu kadan, ya kara sinasinan fim din, ya raba shi biyu, kashi na daya da na biyu. Na yarda na kara din. Kuma Allah ya ba mu sa'a fim din ya yi kyau, na tabbata zai kayatar da masu kallo.
FIM: Su waye 'yan wasan cikin Ta Bayyana?
A'ISHA: Jaruman fim din su ne Ahmed S. Nuhu da Farida Jalal, inda Farida ta fito a fim din kamar Abida Mohammed. Kuma akwai manyan 'yan wasa kamar su Ibrahim M. Mandawari, Shehu Hassan Kano, Hauwa Ali Dodo, Ladi Mohammed, Ibro, Sani S.K., Isa Bello Ja, Ciroki, Saratu Gidado, Hajiya Amina Garba, da sauransu. Kuma akwai wani shirin da zan shirya a gaba mai suna Wata Ta Fi Wata, wanda zan shirya shi a Kaduna.
FIM: Duk finafinan naki Mandawari ne daraktansu?
A'ISHA: Na farkon dai Mandawari ya yi, na biyu kuma Idris Shu'aibu Lilisco shi ya yi.
FIM: Yaushe na farkon zai fito?
A'ISHA: Nan da dai 'yan kwanaki kadan. Sai na fara tallarsa sosai tukun, don a gaskiya na sa kudi sosai har ya kasance na raba fim din gida biyu.
FIM: Menene sunan kamfaninki?
A'ISHA: Sunan kamafanina 'Amart Entertainment'. Kuma shi 'Amart', sunaye ne na hada na mahifiyata da babana da kuma nawa.
FIM: A kamfanin, fim kawai ake shiryawa ko akwai wasu abubuwa da kuke yi?
A'ISHA: A'a, musamman don shirin fim na kafa kamfanin.
FIM: Kina da wata shawara zuwa ga 'yan'uwanki furodusoshi mata?
A'ISHA: A gaskiya ni dai da za a hada kai ana taimaka wa juna, da zai fi. Misali kamar a kungiya, idan wata ta samu matsala, abin taimako ne a hada a ga dai ta ci gaba da abin da take yi.
FIM: Ban da kasancewarki furodusa, za ki iya fitowa a fim a matsayin 'yar wasa?
A'ISHA (ta yi dariya): Ba za a bar ni ba ai. Don ko yanzu harkar da nike yi wallahi a gida ba so ake yi ba, kawai dai ni na sa ra'ayi ina yi.
FIM: Ko dai kina da irin tunanin nan na wasu da ke ganin idan mace na yin fim ba ta samun mijin aure?
A'ISHA (dariya): Ba haka ba ne.
FIM: A karshe, kina da wata shawara zuwa ga 'yan fim baki daya?
A'ISHA: Ni shawarata ita ce, don Allah mu hada kai mu so juna, mu guji hassada da mugun nufi ga junanmu.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin