Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 45   Disamba 2003
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection


Aminu Moh'd (H.R.B.): Ya Soma Kwatar Muryarsa

Ashe shi ne ya rera wasu wakoki da ake cewa na Yakubu Muhammad ne?

Daga wakilinmu a Kano

WANI lokaci, fasihi yakan bullo ne a inda ba ka tsammani ko a lokacin da ba ka tsammani, ko kuma wanda kake zaton bai iya yin abu ashe ya iya. AMINU MOHAMMED, wanda ake kira Aminun H.R.B., ma'aikaci ne a kamfanin shirya fim na 'H.R.B. Enterprises' da ke Kano, wato kamfanin da finafinansa ke tashe a yanzu. Shi ne yake kula da bangaren rikodin na finafinai ko wakoki.

Da yawan wadanda suka san shi, ba su san cewa ya iya waka ba, wato irin wakokin da ake rerawa a situdiyo ana saka su cikin finafinan Hausa. To, Aminu da kansa ya tabbatar wa da mujallar Fim cewa shi cikakken mawaki ne, wanda ya tabbatar da rade-radin da ake yi cewa yana yin wakar. Haka kuma ana rade-radin cewa wasu wakoki da ke fitowa ana cewa fitaccen mawaki Yakubu Muhammad ne ya rera su, shi Aminu ne ya rera su, musamman ma wadanda ke fitowa cikin finafinan H.R.B., to amma wai sai a sanya sunan Yakubu. Dalili shi ne, da farko shi Aminu bai son a gane cewa yana waka, na biyu kuma muryarsu irin ta Yakubu din ce. Wannan bayanin dai yana da ban-mamaki, musamman da yake shi kansa Aminu ya tabbatar da shi.

Mu koma baya kadan. Shi dai Aminu Muhammad haifaffen Kofar Nassarawa ne cikin Birnin Kano. Ya yi makarantar firamare zuwa karamar sakandare a Kano, daga nan ya wuce babbar sakandare ta Kawaji. Da ya gama sai ya tafi Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano (CAS). Daga nan ma bayan ya ga ma sai ya tafi ya yi diploma a Jami'ar Bayero. "Bayan nan ne har yanzu ban ci gaba ba; ina nan H.R.B. ina rikodin," inji shi.

Da aka tambaye shi abin da ya ba shi sha'awar shiga harkar fim, sai ya amsa da cewa, "Da man aikin da nake yi kenan tun tuni, tun maigidana shi Rabi'u Ibrahim H.R.B. yana Kofar Wambai muna harkar audio kawai. Sai bayan wannan harkar ta fim ta yi dan suna sai shi ma ya fara yin wani fim 'Abin Sirri Ne'. Daga nan shikenan, yanzu ga shi ya zamanto mun samu daukaka da taimakon Ubangiji."

Tun farkon fara wannan harka Aminu bai fara nuna basirarsa ta wake ba. Shin bai samu dama ba ne?

Aminu: "Gaskiya a da tsananin da muke da shi a gidanmu ne ya hana ni farawa, wanda ina tunanin ba za a bar ni ba, shi ya sa. Amma tun a wancan lokacin ma ina dan yi amma sai a rubuta sunan Yakubu tunda da ma shi mawaki ne, kuma mun fi kusa da shi, sannan muryarmu ta zo daya. Ni dai an fi sanina da rikodin kawai."

To ba ya tunanin zai samu matsala tsakanin harkar rikodin dinsa da wakar da yanzu an fara saninsa a kan ta, musamman idan aka rika ba shi aiki sosai? Mawakin ya ce bai hango wata matsala ba a nan. "Duk wadannan bangarorin guda biyu tunda shi kanshi ubangidan nawa komai sai da saninsa da izninsa zan yi, ko da bai sani ba na samu waka sai na sanar da shi, lokacin da ba ni da rikodin in ya amince sai in je in yi, tunda da ma komai na zama shi ne sanadiyya."

Tunda Aminu ya yi ikirarin cewa wasu wakoki da Yakubu ya rera shi ne ya yi su amma aka sa sunan shi Yakubun, mun so ya gaya mana su, amma sai ya ce, "Wadannan tunda ba da sunana na yi su ba, ba zan lissafa da su ba tunda an yi amfani ne da sunan Yakubu Muhammad. Amma yanzu na yi waka a fim din Sutura na Alhaji Musa na Malam Kato, sannan a cikin Kasko ma akwai wakar da ni da Yakubu muka yi; ni na rubuta wakar 'Auren So Da Dadi,' 'Mun Ji Zancenku,' da kuma ta wani sabon fim, da wacce na yi wa shugabar makarantar A.T.C."

Wato dai kenan shi ma kana iya rubuta wakoki, ko? "Ina rubutawa ni ma kamar yadda sauran suke yi."

Wakilinmu ya tambaye shi yadda yake cajin mutane kan kowace waka da zai yi. Aminun H.R.B. ya amsa: "Ina tambayar mutum in ce 'Yaya kake ba wa sauran?' In ya ce kaza, sai in ce 'Ni ma haka za ka ba ni.'" To tunda dai likkafarsa ta fara dagawa, me yake so ya zama a cikin wannan harkar ta finafinan Hausa? Sai sabon mawakin ya ce, "Zama wani abu wannan duk nufi ne daga Ubangiji. Ni kuma ina yin wannan waka ne saboda nishadi, amma duk wani ci-gaba a wannan harkar ai sai dai in ce alhamdu lillahi."

Mun nuna masa cewa ana zargin wasu mawaka da cewa suna sa kalamai da ake ganin batsa ne a wasu wakokinsu. Shin shi ma ya yarda da hakan na faruwa?

Aminu: "Gaskiya wani lokacin shi wanda ya rubuta wakar ba haka yake nufi ba; kawai wani ne yake yi mata wannan fassarar. Amma daga yanzu in mutum ya ji wani abu mai kama da wannan sai ya samu wanda ya yi wannan wakar ya tambaye shi ya ji shi me yake nufi."

A karshe, mawakin ya nuna mana cewa shi ne ya rubuta wakar nan ta HRB wadda ta yi tashe kwanan baya mai suna "Mace Mai Dusa" ta cikin fim din "Tubali". Ya kuma gaya mana ma'anar karin wakar inda ake cewa, "mace mai dusa, mace mai dusa mace mai dusa, sa dusa; lubajiya in ba ji, mace mai dusa sa dusa in bajiya in ba". A cewarsa, "Ma'anar mace mai dusa ko in ce abin da wakar ma take nufi sai an shiga cikin wakar sannan a fahimci ma'anar ita kanta wakar, amma amshi da 'mace mai dusa,' lokacin da muna tafiya mun riga mun ma wuce sai na tuna da matar da muka wuce tana saida dusa. To da na dawo sai na tashi waka da 'mace mai dusa,' domin a lokacin ta fado min a rai. Sai kuma aka kirkiri sauran gangar jiki, kuma an yi ne domin ta gyara. Ta kuma kayartar da mai kallo."

Yanzu tunda Aminu ya fito fili, ya soma kwatar muryarsa daga wajen Yakubu kenan.

Muna daf da buga mujalla mun samu labarin cewa Aminu ya bar kamfanin HRB saboda wani sabani tsakaninsa da Rabi'u.

Aminu H.R.B
Aminu Muhammad H.R.B

Bayan sun kammala abin da ya kai su sai hirarsu ta kai su ga tattaunawa kan yadda mujallun harkar fim ke taka rawa a fagen shirin fim, musamman saboda shi Momo yana daga cikin wasu da suka kafa mujalla mai suna Mudubi.

Suna tsakar tattaunawar sai matashin dan wasa kuma daraktan nan mai suna Suleiman Sa'eed ya fito daga dakin da yake aikin tace wani sabon fim dinsa, ya durkusa a gaban Sheme ya shiga yin kalaman batanci gare shi. Da farko Sheme bai fahimci dalilin hakan ba sai daga bisani ya fahimci cewa Suleiman yana bayyana fushi ne kan labarin da Fim ta buga a watan Afrilu na 2003. Idan kun tuna, labarin ya bayyana rikici ne a tsakanin Misbahu M. Ahmad da budurwarsa ta lokacin, wato Rukayya Umar Santa, wadda shi Misbahu ya zarga da cewa an gan ta a daki tare da Suleiman a garin Jos lokacin da suka je shirya wani fim. A labarin na Afrilu, an buga hirar da mujallar ta yi da Suleiman inda ya kare kansa kan zargin Misbahu.

A babatun da Suleiman ya yi a gaban Momo, ya bayyana cewa an yi amfani da wasu kalmomi da yake ganin na batanci ne a kansa. Ya ce a gabatarwar hirar tasa, an ce shi ba ruwansa da kowa, kuma bai zuwa wurin kowa a Kano, "kullum yana zaune a gida kamar maye." Kalmar "kamar maye," inji shi, batanci ne. Na biyu, an rubuta cewa shi mayaudari ne wanda ke yaudarar 'yanmatan industiri da cewa zai aure su. Ya ce a nan ma batanci ne. A cewar Suleiman, Sheme ya tsane shi ne kawai, shi ya sa aka yi wancan rubutun. Don haka cikin fushi da gadara ya shiga rantsuwar cewa shi ne idan har aka kara buga wani labari kansa a mujallar Fim, "ko da kuwa wasikar yabo ce daga wurin masu karatu," to babu shakka zai kashe mawallafin mujallar. Hak kuma ya kara da barazanar cewa idan har Sheme ya bata masa rai a lokacin, to zai turo shi daga kan benen da suke a kai, a take ya mutu.

Sheme da Suleiman suka dinga gardama a kan labarin da aka buga, shi Sheme yana nuna masa cewa me ya sa bai yi kuka da labarin ba sai yanzu bayan watanni takwas? Ya kuma nuna masa cewa duk wani zargi da yake yi masa ba haka ba ne. Amma ina! Suleiman bai amince ba, ya shiga babatunsa. Shi kuwa Momo, ya shiga ba su magana a kan cewa su daina wannan tankiya.

"Duk mutumin da yake da hankali bai dace ya yi wasa da mutumin da ya ci alwashin daukar ransa ba," inji Ibrahim Sheme. Don haka sai ya kudiri aniyar daukar matakin da ya dace don ya kare kansa. Duk da yake Momo ya yi kokarin ba da hakuri tare da ganin an sasanta, amma a washegari sai abin ya kai ga 'yansanda. Sheme ya rubuta takardar kuka ga Kwamishinan 'Yansanda na Jihar Kano tare da rarraba ta ga hukumomin tsaro kamar su SSS. Duk wanda ya karanta takardar nan zai san ba abin wasa aka rubuta a ciki ba, kuma yadda aka zayyana kukan lallai sai masanin kundin tsarin mulki na kasa.

Bisa shawarar da aka ba shi kuma sai ya kai kukan ga ofishin difi'o na yankin Gwale cikin birni, wanda a yankinsa aika-aikar ta Suleiman ta faru. Ba tare da bata lokaci ba aka tura jami'an tsaro suka taso keyar daraktan, wanda yana can ofishin su Momo yana editin wani fim da aka ce nasa na kansa ne, suka kawo shi ofishinsu. Yana sanye da wandon jeans shudi da bakar riga damammiya da hula hana-salla.

Wakilinmu, wanda yana tare da 'yansandan lokacin da suka cafko Suleiman, ya lura da yadda dan wasan ya dinga tofa addu'o'i a cikin mota a kan hanyarsu ta zuwa ofishin 'yansanda. A ofishin, an bukaci Ibrahim Sheme ya maimaita karar da yake yi. Take ya aikata hakan da Turanci. Shi kuwa gogan naka da aka ce ya yi bayani sai ya ce ai shi sam ba ya jin Turanci. Jin wannan ya sa ran jami'i mai bincike, Mr. Agada, ya baci don ganin za a raina masa wayo. Duk da haka an nemi ya kare kansa da Hausa, inda ya karyata cewa ya ce zai kashe mawallafin. "Haba Ibrahim Sheme, sai ka ce ni ba Musulmi ba ne? Yaya za a yi in kashe mutum?" inji shi. Ya ce da ya ce, "Sai na kashe ka ni ma," ba yana nufin zai kashe ran Sheme ba ne, a'a wai a nufinsa tun da an "kashe shi" a mujalla, to shi ma sai ya bata sunan Sheme da wata mujallar, wai ya "kashe" shi kenan.

Jim kadan da wannan jawabi na Suleiman sai ya aiki wani yaro da suke tare da shi ya kira masa wani; da alamun dai Hamisu Iyan-Tama ne yake so a kira domin shi ne ya saba karbar 'yan fim daga hannun 'yansanda, don ba a ma dade ba da ya karbe shi a hannun wasu 'yansandan a kan batun kudin fim din Qaya da aka ce ya ci.

Wani abu da ba a sani ba shi ne ashe Ibrahim Sheme ya yi aikin nasa na dan jarida ya dauki duk kalaman da Suleiman ya furta a ofishin su Momo, har da inda yake cewa sai ya kashe shi, duk ya nade su a wata 'yar karamar rikoda da ke aljihunsa. A ofishin 'yansandan ne ya fito da rikodar ya danna, sai ga muryar Suleiman tana fitowa yana babatunsa. Sheme ya kuma ce babu abin da yake sosai 'yansanda su yi bincikensu kuma su shigar da maganar kotu, domin fa shi sai ya yi shari'a da Suleiman a kan batun. Ai da jin wannan kaset da kuma barazanar da Sheme ke yi, sai idon Suleiman ya raina fata.

Lokacin da Sheme da Abbas Sa'id Kiru da shi Suleiman suka kasance su uku a ofishin dansanda mai bincike, Suleiman ya so yin magana da Sheme don su sasanta. Amma shi sai ya ki yarda da hakan, ya ce masa, "Look Suleiman, yanzu muna wajen hukuma ne; duk maganar da za mu yi ka bari sai suna nan."

Bayan 'yansanda sun gama daukar dukkan bayanai a rubuce, sun nemi Sheme ya kawo shaidunsa guda biyu da aka yi abin a gabansu a ranar. Daga nan aka ajiye Suleiman a bayan kanta bisa zargin ya yi barazanar yin kisan kai.

Da yamma, shaidun suka isa ofishin 'yansandan inda suka rubuta bayanin abin da suka san ya faru a gabansu. Cikin bayanan nasu, sun nuna cewa babu shakka Suleiman ya yi barazanar yin kisan tare da fadin bakaken maganganu.

A wannan ranar dai labari ya bazu a industiri cewa Suleiman ya kara shiga tsomomuwa kamar yadda ya saba yi a baya, amma a wannan karon da 'yan mujalla yake yi. Lokacin da Ibrahim Sheme ya isa ofishin Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Hamisu Lamido Iyan-Tama, sai wasu 'yan fim, ciki har da shi Hamisu da kuma Hafizu Bello, suka shiga rokonsa kan cewa ya yafe wa Suleiman. Shi kuma ya ce, "Ba zan kyale shi ba, domin ku kun san da cewa akwai wani furodusa da ya taba yi mana irin wannan barazanar, na hakura na kyale shi. To abin da ba ku sani ba shi ne har yanzu ban daina nadama ba kan kyale shi din da na yi har ya je yana surutan banza a gari. Wallahi yanzu duk wanda ya taka mu, mu ma sai mun taka shi ko da kuwa da kyamarar shirya fim uwarsa ta haife shi."

Duk da haka, washegari sai Iyan-Tama ya garzaya ofishin 'yansanda na Gwale, inda ya gana da Suleiman na tsawon awa daya. Suleiman, wanda a nan ya kwana, ya amsa laifinsa kuma ya amince da cewa Iyan-Tama ya rokin Sheme idan ya zo a kan don Allah ya yafe masa bambarmar da ya yi. Suna nan sai kuma ga Dan'azimi Baba, wanda aminin Sheme ne kuma ubangidan Suleiman, shi ma ya ji labari ya zo. Daga nan Iyan-Tama ya tafi, suka gamu da Sheme, ya gaya masa cewa ga yadda suka yi da Suleiman. Hasali ma Suleiman ya ce zai rubuta takardar neman afuwa a ba Sheme, inji shi, wanda zai nuna tsantsar nadamarsa kan maganar da ya yi. Hamisu ya kuma bukaci Sheme da ya dakata kada ya kai maganar kotu domin dai Suleiman ya yi nadama.

Da Ibrahim Sheme ya koma ofishin 'yansanda, sai ya tarar da Dan'azimi da kuma sakataren Kungiyar 'yan kasuwa masu saida kaset, wato Alh. Ahmad Mohammed Amge, suna jiransa. Abin mamaki, babu wani dan fim da ya zo wurin Suleiman, wanda hakan bai rasa nasaba da rashin jituwar da ke tsakanin daraktan da yawancin 'yan fim. Dan'azimi ya yi wa Suleiman nuni da hakan, yana cewa, "Yanzu kai Suleiman, duk garin nan babu wanda ya yi bakin jininka a industiri. In kuwa ba haka ba ai da su kansu masu zuga ka kan mutane sun zo nan. Wa ka gani?"

A gaskiya bai ga kowa ba daga Iyan-Tama sai shi Dan'azimi da kuma Amge. Wadannan bayin Allah sun tasa Sheme a gaba suka ba shi magana. Kuma tun ma kafin ya iso har Suleiman ya rubuta takardar ba da hakuri da kansa, inda ya shaida wa Sheme cewa wallahi kuskure ya yi da ya yi wancan ikirarin.

A karshe, Sheme ya amince zai janye maganar daga gun 'yansanda, yana mai nuni da cewa zai yi hakan ne bisa ganin mutuncin mutanen da suka ba shi hakuri da kuma ganin cewa idan bai hakura ba, to Suleiman zai sha wuya a banza ne kurum.

To, inda gizo ke sakar shi ne ashe ya zuwa lokacin har 'yansanda sun shigar da kara a Babbar Kotu ta Jihar Kano (High Court), kuma an sa ranar da za a fara shari'a. Don tabbatar da hakan, 'yansandan sun kawo takardar sammaci sun nuna wa su Sheme, Suleiman, Dan'azimi, Amge da kuma wakilin mujallar Fim. Sun kuma nuna musu cewa zai yi wuya su koma kotu su janye karar. Duk da haka su Dan'azimi da Amge sun roki 'yansandan a kan su dai taimaka tunda aikinsu ne.

A karshe dai da difi'o ya zo sai ya amince da kukan nasu. Ya sa aka kira masa Suleiman ya yi masa fada tare da cewa don Allah ya daina jan fada. ya ce masa, "Ai idan ba ka yarda da wani labari da mujalla ta rubuta ba, ko ba a kanka ba ne, kana iya rubuta martani ga mujallar ka fadi naka ra'ayin; idan kuma a kanka ne, ka ga ba ka yarda ba, kana iya kai kuka ga shugabanninku na harkar fim kafin ma maganar ta je kotu. Amma a ce ka ce za ka dau ran mutum, ai ka wuce gona da iri."

Wani abin mamaki shi ne, a karshen ma tare da Sheme aka yi fafutikar kwatar Suleiman daga hannun 'yansanda. Kafin Sheme ya hau motarsa ya bar ofishin 'yansandan sai da Suleiman ya ce masa, "Ni dai rokona gare ka shi ne ko da wani ya zo ya ce maka na ce wani abu game da kai, wallahi karya ake mani, domin ba zan ce komai ba. Ka san halin mutane, kada kuma a zo a ce za a hada mu."

Kai daga jin wanna magana ka san ta fito ne daga bakin mutumin da ya yi magana ta zame masa jangwam, kuma yana nadamar yinta. Ko da gaske nadamar tasa ta kai zuci? Oho! Kuma ko 'yan fim irin Suleiman za su koyi darussa daga wannan harkallar ta Suleuiman Sa'eed? Shi ma ba mu sani ba. Amma lokaci zai nuna mana.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin