SAI NA KASHE IBRAHIM SHEME, inji Sulaiman Sa'eed
Daga ABBAS SA'ID KIRU
a Kano
GASKIYAR maganar da Hausawa kan yi da suka ce "baki shi ke yanka wuya" ta fito fili kwanan nan a Kano. A Litinin, 1 ga Disamba, 2003, mawallafin mujallun Fim da Bidiyo, Ibrahim Sheme, ya je ofishin fitaccen dan wasa kuma daraktan nan Aminu A. Shariff (momo) da ke rukunin shagunan SHY Shopping Complex, Gadon Kaya, don yi masa ta'aziyyar rasuwar mahaifinsa. A wannan lokaci, mawallafin yana tare da wakilin mujallar Fim na Kano, wato Sani Mohammed Maitanga.
Ibrahim Sheme, Mawallafin mujallun Fim da Bidiyo.
|
Bayan sun kammala abin da ya kai su sai hirarsu ta kai su ga tattaunawa kan yadda mujallun harkar fim ke taka rawa a fagen shirin fim, musamman saboda shi Momo yana daga cikin wasu da suka kafa mujalla mai suna Mudubi.
Suna tsakar tattaunawar sai matashin dan wasa kuma daraktan nan mai suna Suleiman Sa'eed ya fito daga dakin da yake aikin tace wani sabon fim dinsa, ya durkusa a gaban Sheme ya shiga yin kalaman batanci gare shi. Da farko Sheme bai fahimci dalilin hakan ba sai daga bisani ya fahimci cewa Suleiman yana bayyana fushi ne kan labarin da Fim ta buga a watan Afrilu na 2003. Idan kun tuna, labarin ya bayyana rikici ne a tsakanin Misbahu M. Ahmad da budurwarsa ta lokacin, wato Rukayya Umar Santa, wadda shi Misbahu ya zarga da cewa an gan ta a daki tare da Suleiman a garin Jos lokacin da suka je shirya wani fim. A labarin na Afrilu, an buga hirar da mujallar ta yi da Suleiman inda ya kare kansa kan zargin Misbahu.
A babatun da Suleiman ya yi a gaban Momo, ya bayyana cewa an yi amfani da wasu kalmomi da yake ganin na batanci ne a kansa. Ya ce a gabatarwar hirar tasa, an ce shi ba ruwansa da kowa, kuma bai zuwa wurin kowa a Kano, "kullum yana zaune a gida kamar maye." Kalmar "kamar maye," inji shi, batanci ne. Na biyu, an rubuta cewa shi mayaudari ne wanda ke yaudarar 'yanmatan industiri da cewa zai aure su. Ya ce a nan ma batanci ne. A cewar Suleiman, Sheme ya tsane shi ne kawai, shi ya sa aka yi wancan rubutun. Don haka cikin fushi da gadara ya shiga rantsuwar cewa shi ne idan har aka kara buga wani labari kansa a mujallar Fim, "ko da kuwa wasikar yabo ce daga wurin masu karatu," to babu shakka zai kashe mawallafin mujallar. Hak kuma ya kara da barazanar cewa idan har Sheme ya bata masa rai a lokacin, to zai turo shi daga kan benen da suke a kai, a take ya mutu.
Sheme da Suleiman suka dinga gardama a kan labarin da aka buga, shi Sheme yana nuna masa cewa me ya sa bai yi kuka da labarin ba sai yanzu bayan watanni takwas? Ya kuma nuna masa cewa duk wani zargi da yake yi masa ba haka ba ne. Amma ina! Suleiman bai amince ba, ya shiga babatunsa. Shi kuwa Momo, ya shiga ba su magana a kan cewa su daina wannan tankiya.
"Duk mutumin da yake da hankali bai dace ya yi wasa da mutumin da ya ci alwashin daukar ransa ba," inji Ibrahim Sheme. Don haka sai ya kudiri aniyar daukar matakin da ya dace don ya kare kansa. Duk da yake Momo ya yi kokarin ba da hakuri tare da ganin an sasanta, amma a washegari sai abin ya kai ga 'yansanda. Sheme ya rubuta takardar kuka ga Kwamishinan 'Yansanda na Jihar Kano tare da rarraba ta ga hukumomin tsaro kamar su SSS. Duk wanda ya karanta takardar nan zai san ba abin wasa aka rubuta a ciki ba, kuma yadda aka zayyana kukan lallai sai masanin kundin tsarin mulki na kasa.
Bisa shawarar da aka ba shi kuma sai ya kai kukan ga ofishin difi'o na yankin Gwale cikin birni, wanda a yankinsa aika-aikar ta Suleiman ta faru. Ba tare da bata lokaci ba aka tura jami'an tsaro suka taso keyar daraktan, wanda yana can ofishin su Momo yana editin wani fim da aka ce nasa na kansa ne, suka kawo shi ofishinsu. Yana sanye da wandon jeans shudi da bakar riga damammiya da hula hana-salla.
Wakilinmu, wanda yana tare da 'yansandan lokacin da suka cafko Suleiman, ya lura da yadda dan wasan ya dinga tofa addu'o'i a cikin mota a kan hanyarsu ta zuwa ofishin 'yansanda. A ofishin, an bukaci Ibrahim Sheme ya maimaita karar da yake yi. Take ya aikata hakan da Turanci. Shi kuwa gogan naka da aka ce ya yi bayani sai ya ce ai shi sam ba ya jin Turanci. Jin wannan ya sa ran jami'i mai bincike, Mr. Agada, ya baci don ganin za a raina masa wayo. Duk da haka an nemi ya kare kansa da Hausa, inda ya karyata cewa ya ce zai kashe mawallafin. "Haba Ibrahim Sheme, sai ka ce ni ba Musulmi ba ne? Yaya za a yi in kashe mutum?" inji shi. Ya ce da ya ce, "Sai na kashe ka ni ma," ba yana nufin zai kashe ran Sheme ba ne, a'a wai a nufinsa tun da an "kashe shi" a mujalla, to shi ma sai ya bata sunan Sheme da wata mujallar, wai ya "kashe" shi kenan.
Jim kadan da wannan jawabi na Suleiman sai ya aiki wani yaro da suke tare da shi ya kira masa wani; da alamun dai Hamisu Iyan-Tama ne yake so a kira domin shi ne ya saba karbar 'yan fim daga hannun 'yansanda, don ba a ma dade ba da ya karbe shi a hannun wasu 'yansandan a kan batun kudin fim din Qaya da aka ce ya ci.
Wani abu da ba a sani ba shi ne ashe Ibrahim Sheme ya yi aikin nasa na dan jarida ya dauki duk kalaman da Suleiman ya furta a ofishin su Momo, har da inda yake cewa sai ya kashe shi, duk ya nade su a wata 'yar karamar rikoda da ke aljihunsa. A ofishin 'yansandan ne ya fito da rikodar ya danna, sai ga muryar Suleiman tana fitowa yana babatunsa. Sheme ya kuma ce babu abin da yake sosai 'yansanda su yi bincikensu kuma su shigar da maganar kotu, domin fa shi sai ya yi shari'a da Suleiman a kan batun. Ai da jin wannan kaset da kuma barazanar da Sheme ke yi, sai idon Suleiman ya raina fata.
Lokacin da Sheme da Abbas Sa'id Kiru da shi Suleiman suka kasance su uku a ofishin dansanda mai bincike, Suleiman ya so yin magana da Sheme don su sasanta. Amma shi sai ya ki yarda da hakan, ya ce masa, "Look Suleiman, yanzu muna wajen hukuma ne; duk maganar da za mu yi ka bari sai suna nan."
Bayan 'yansanda sun gama daukar dukkan bayanai a rubuce, sun nemi Sheme ya kawo shaidunsa guda biyu da aka yi abin a gabansu a ranar. Daga nan aka ajiye Suleiman a bayan kanta bisa zargin ya yi barazanar yin kisan kai.
Da yamma, shaidun suka isa ofishin 'yansandan inda suka rubuta bayanin abin da suka san ya faru a gabansu. Cikin bayanan nasu, sun nuna cewa babu shakka Suleiman ya yi barazanar yin kisan tare da fadin bakaken maganganu.
A wannan ranar dai labari ya bazu a industiri cewa Suleiman ya kara shiga tsomomuwa kamar yadda ya saba yi a baya, amma a wannan karon da 'yan mujalla yake yi. Lokacin da Ibrahim Sheme ya isa ofishin Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Hamisu Lamido Iyan-Tama, sai wasu 'yan fim, ciki har da shi Hamisu da kuma Hafizu Bello, suka shiga rokonsa kan cewa ya yafe wa Suleiman. Shi kuma ya ce, "Ba zan kyale shi ba, domin ku kun san da cewa akwai wani furodusa da ya taba yi mana irin wannan barazanar, na hakura na kyale shi. To abin da ba ku sani ba shi ne har yanzu ban daina nadama ba kan kyale shi din da na yi har ya je yana surutan banza a gari. Wallahi yanzu duk wanda ya taka mu, mu ma sai mun taka shi ko da kuwa da kyamarar shirya fim uwarsa ta haife shi."
Duk da haka, washegari sai Iyan-Tama ya garzaya ofishin 'yansanda na Gwale, inda ya gana da Suleiman na tsawon awa daya. Suleiman, wanda a nan ya kwana, ya amsa laifinsa kuma ya amince da cewa Iyan-Tama ya rokin Sheme idan ya zo a kan don Allah ya yafe masa bambarmar da ya yi. Suna nan sai kuma ga Dan'azimi Baba, wanda aminin Sheme ne kuma ubangidan Suleiman, shi ma ya ji labari ya zo. Daga nan Iyan-Tama ya tafi, suka gamu da Sheme, ya gaya masa cewa ga yadda suka yi da Suleiman. Hasali ma Suleiman ya ce zai rubuta takardar neman afuwa a ba Sheme, inji shi, wanda zai nuna tsantsar nadamarsa kan maganar da ya yi. Hamisu ya kuma bukaci Sheme da ya dakata kada ya kai maganar kotu domin dai Suleiman ya yi nadama.
Da Ibrahim Sheme ya koma ofishin 'yansanda, sai ya tarar da Dan'azimi da kuma sakataren Kungiyar 'yan kasuwa masu saida kaset, wato Alh. Ahmad Mohammed Amge, suna jiransa. Abin mamaki, babu wani dan fim da ya zo wurin Suleiman, wanda hakan bai rasa nasaba da rashin jituwar da ke tsakanin daraktan da yawancin 'yan fim. Dan'azimi ya yi wa Suleiman nuni da hakan, yana cewa, "Yanzu kai Suleiman, duk garin nan babu wanda ya yi bakin jininka a industiri. In kuwa ba haka ba ai da su kansu masu zuga ka kan mutane sun zo nan. Wa ka gani?"
A gaskiya bai ga kowa ba daga Iyan-Tama sai shi Dan'azimi da kuma Amge. Wadannan bayin Allah sun tasa Sheme a gaba suka ba shi magana. Kuma tun ma kafin ya iso har Suleiman ya rubuta takardar ba da hakuri da kansa, inda ya shaida wa Sheme cewa wallahi kuskure ya yi da ya yi wancan ikirarin.
A karshe, Sheme ya amince zai janye maganar daga gun 'yansanda, yana mai nuni da cewa zai yi hakan ne bisa ganin mutuncin mutanen da suka ba shi hakuri da kuma ganin cewa idan bai hakura ba, to Suleiman zai sha wuya a banza ne kurum.
To, inda gizo ke sakar shi ne ashe ya zuwa lokacin har 'yansanda sun shigar da kara a Babbar Kotu ta Jihar Kano (High Court), kuma an sa ranar da za a fara shari'a. Don tabbatar da hakan, 'yansandan sun kawo takardar sammaci sun nuna wa su Sheme, Suleiman, Dan'azimi, Amge da kuma wakilin mujallar Fim. Sun kuma nuna musu cewa zai yi wuya su koma kotu su janye karar. Duk da haka su Dan'azimi da Amge sun roki 'yansandan a kan su dai taimaka tunda aikinsu ne.
A karshe dai da difi'o ya zo sai ya amince da kukan nasu. Ya sa aka kira masa Suleiman ya yi masa fada tare da cewa don Allah ya daina jan fada. ya ce masa, "Ai idan ba ka yarda da wani labari da mujalla ta rubuta ba, ko ba a kanka ba ne, kana iya rubuta martani ga mujallar ka fadi naka ra'ayin; idan kuma a kanka ne, ka ga ba ka yarda ba, kana iya kai kuka ga shugabanninku na harkar fim kafin ma maganar ta je kotu. Amma a ce ka ce za ka dau ran mutum, ai ka wuce gona da iri."
Wani abin mamaki shi ne, a karshen ma tare da Sheme aka yi fafutikar kwatar Suleiman daga hannun 'yansanda. Kafin Sheme ya hau motarsa ya bar ofishin 'yansandan sai da Suleiman ya ce masa, "Ni dai rokona gare ka shi ne ko da wani ya zo ya ce maka na ce wani abu game da kai, wallahi karya ake mani, domin ba zan ce komai ba. Ka san halin mutane, kada kuma a zo a ce za a hada mu."
Kai daga jin wanna magana ka san ta fito ne daga bakin mutumin da ya yi magana ta zame masa jangwam, kuma yana nadamar yinta. Ko da gaske nadamar tasa ta kai zuci? Oho! Kuma ko 'yan fim irin Suleiman za su koyi darussa daga wannan harkallar ta Suleuiman Sa'eed? Shi ma ba mu sani ba. Amma lokaci zai nuna mana.
An kulle Suleiman Sa'eed!!
... saboda ya cinye kudin masu fim
Daga ABBAS SA'ID KIRU
a Kano
GA alama, za a dade ba a daina jin duriyar Suleiman Sa'eed a fagen shirin fim ba. Ba kurum don saboda finafinansa ba, a'a, har ma saboda rigingimun da yake jefa kansa a ciki. Idan kun tuna, ya taba yin rigima da 'yar wasan nan Maijidda Abbas, wato budurwarsa da suka bata. Ya kuma yi da wata jarumar wadda ita ta yi aure yanzu. Sa'annan ya zo ya yi da Misbahu M. Ahmad da Ali Nuhu a kan batun Rukayya Dawayya.
Suleiman Saeed yana yi wa abokan adawarsa mazurai.
|
To, kwanan kuma sai ta hado su da wasu mutum uku. A bangare daya akwai wadansu furodusoshi su biyu wadanda suka shirya fim din Qaya, a daya bangaren kuma akwai Ibrahim Sheme, mawallafin mujallar Fim. Kowa ya debo da zafi dai bakinsa zai kai, inji Hausawa. A halin yanzu ana nan ana tafka rikicin da ya shiga tsakanin shi Suleiman da tsohon dan wasan nan kuma marubucin laraban finafinan Hausa, Malam Wada Aliyu, wanda aka fi sani da 'Mr. Kent' saboda wasansa a cikin fim din Tsautsayin Takaba. Rikicin, wanda ake tafkawa a ofishin 'yansanda na 'Metro' a Kano, ya faru ne sakamakon karar da su Wada suka kai Suleiman bisa cin amanarsu da ya yi lokacin da suka yarje masa suka ba shi alhakin yin kasuwancin fim dinsa mai suna Qaya. Har ta kai ga an kulle Suleiman din a gadirun har zuwa lokacin da Shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Alhaji Hamisu Lamido Iya-Tama, ya je ya yi belinsa.
Shin ya al'amarin yake? Lokacin da muke hada wannan labarin, mun nemi mu ga Suleiman domin jin nasa bangaren, to amma bai ganu ba. An ce ya yi tafiya. Daya daga cikin wadanda suka shirya fim din kuma yake da kusan kashi 70 cikin dari na kudin da aka shirya fim din, Mohammed S. Bashir, ya bayyana yadda suka yi da Suleiman Sa'eed a kan fim din. A hirarsu da wakilinmu, Bashir ya bayyana yadda suka ba Suleiman amana, da yadda ya ci amanar da kuma matsayin da maganar take a yanzu.
FIM: Menene matsayinka a fim din Qaya?
BASHIR: Ni na shirya shi tare da taimakon Wada, wanda ake kira Mr. Kent.
FIM: Wane rikici ne ya auku a yayin kasuwancin fim din?
BASHIR: Abin da ya faru shi ne ka san an ce rashin sani ya fi dare duhu. Bayan mun gama fim din Qaya, sai muka kira shi Suleiman saboda ya dade a harkar, muka kira shi bisa amana ya yi mana kasuwancin fim din saboda wanda yake jagorancin abin ya rasu, wato Tijjani Ibraheem. Muka zauna da shi da manajana Mr. Kent, ya ba shi zabi uku. Na farko ko dai ya yi abin nan a biya shi wani kaso (percentage) ko ya yi a biya shi wani abu da yake ganin zai yanka a biya shi. Ya ce shi zai yi ne kawai, abin da aka ga kokarinsa sai a biya shi. Lokacin da ya je ya sa fim din ya kalla sai na yi ta jin ya fada wa mutane wai an baro shiri tun baya, duk wanda zai yi fim na 'action' wai shi aka sani a fagen, don haka wai fim din bai yi ba. To da ya tashi zai fitar da fim din muka je wajen yin mastan sai ya ce in tafi zai yi komai da kansa. Da yake ban zaci yana da wata manufa ba, sai na tafi. Ranar da ya bayar da mastan sai ya saka hoton ya yi duhu, ya cire muryar. A daren, wasu 'yan kasuwa suka same shi suka yi masa kuka ya sake wa wasu daga cikinsu akalla su biyar, amma don bakin ciki da mugunta maimakon ya bi ragowar ma ya sake musu sai ya ki.
Washegari da safe sai muka ba shi kwali duhu daya ya kai Kaduna, muka ba shi kudin mota N5,000.00 wai don dai ya ji dadi, amma sai ya ajiye kwalayen a dakinsa ya yi tafiyarsa Jos. Har gobe 'yan Kaduna ba su sami fim din ba. To tafiyarsa Jos ya bar ni da wahala, dole na rika sake wani aikin ina kai wa 'yan kasuwa ina sake musu masta. A karshe Suleiman ya sayar da kwali dubu biyar; aka sake buga dubu biyu ya sayar. Muka fara bin diddigin kudin, tunda an sayar da dubu biyar. Sai ya ce to ai an yi magana da shi babu maganar yarjejeniya, to yana so ya san menene hakkinsa a ciki domin yana ganin watakila ba za a ba shi abin da zai dace ba a karshe.
A karshe dai ya nemi a ba shi 20% (kashi ashirin bisa dari). Muka ce ba za mu yarda ba, to a karshe dai muka yarda za mu ba shi N30,000 idan an sayar da kwali 7,000. Muka tambaye shi wadanda ya sayar sun biya shi? Ya ce wasu ba su biya ba. Da ni da shi muka je wajen farko da muka je muna bin su N33,300.00. Sai na ce ina kudi? Sai ya ce ai ya zame kasonsa da aka yi alkawari, sai na ce to ai bai sayar ya kawo ba, yaya za a yi haka? Sai mai kantin ma ya ce ai akwai dubu takwas da ya kamata Suleiman ya biya shi yana binsa, to ni kuma ko da ma ya zame kudin ka ga ina da ragowar dubu uku da dari uku.
Sai muka tafi waje na gaba. Suka ce ai suna binsa wasu kudi, don haka idan akwai wani abu da za su cika min bai fi dubu biyu ba. Da na ga haka sai na same shi a gida na roke shi ya fada min menene yake faruwa? Ya ce shi babu wani abu. Na ce, "To idan na yi bincike zan dauki mataki, ba zan yarda ba." Ya ce ya yarda. Na bi 'yan kasuwa daya bayan daya na ji ta bakinsu da kuma hukuncin da zan dauka, wasu suka ce sun biya wasu suka nemi in dada ba su lokaci har dai na tabbatar kowa ya biya shi.
Daga nan sai na je wajen Wada (Mr. Kent) na sanar da shi halin da ake ciki da matakin da nake shirin dauka. Ya ce yana goyon baya. Na tafi 'Metro Police Station' na kai kara. Aka hada ni da I.P.O. (dansanda mai bincike) muka je muka taho da Suleiman. A nan Hamisu (Iyan-Tama) ya zo belinsa, aka tafi da shi da 'yansanda wajen 'yan kasuwar suna jin duk yadda suka yi da su. To suka ce in yi hakuri za su bi diddigin abin domin sun matse shi (sun gano) ba shi da wata kadara ko kudi a banki ko wani abu da zai iya biyana. To sai aka dibar masa lokuta ya rika zuwa yana kai wani abu, wata rana ya kai dubu biyar, wani lokacin ya kai goma. A karshe sai ya yi watsi da su ya ma daina zuwa. To da na je sai suka ce tunda haka yake to da ma sun ji yana da wani kes da Ibrahim Sheme, mawallafin mujallar Fim, to za su zo su mayar da kes din can Metro don a tabbatar da cewa shi mai laifi ne.
FIM: Daga cikin kudaden da yake mayarwa, nawa aka samu?
BASHIR: Naira dubu arba'in da biyar.
FIM: Nawa kuka hada kuka yi fim din?
BASHIR: Ina da naira dubu dari uku, shi kuma Wada yana da naira dubu dari da tamanin. Amma kashi na 1 da na 2 ne.
FIM: Yanzu aikin kashi na farko kuka ba shi kenan?
BASHIR: E, tunda shi ne ya fita kasuwa.
FIM: Yanzu kudin da kuka kashe kuke so ya dawo muku da su ko har ribar da aka samu?
BASHIR: Ai abu ne na bayar an sayar an biya kudi, ka ga ba zancen akwai asara a ciki.
FIM: To yaya bin diddigin kudin da kuka fara yi?
BASHIR: Sai ya rika zuwa wajen 'yan kasuwa yana debo ragowar kwalayen da ke wajensu da kuma wadanda muka ba shi ya kai Kaduna ya diba ya kai wa 'yansandan.
FIM: An ce ya yi fim kwanan nan. Ba ku tunanin kudinku ne ya yi amfani da su?
BASHIR: Ya yi fim tsakanin daukar fim din da editin kwana hudu kacal. Sunan fim din 'Indosa'. Amma dai sanin gaibu sai Allah. Idan ma wata hanya ce da shi ya samu kudin oho, idan kudinmu ne ma Allah yana kallonsa.
FIM: Idan ya kasa biyan kudin yaya za ka yi?
BASHIR: Ba zai yiwu ba tunda ya san hanyar da ya yi ya shiga dakin da ya ci kudi to dole ya nemi hanyar da zai bi ya fita, tunda akwai hukuma akwai shari'a ai shikenan. Na tabbatar Suleiman ko fashi yake zan iya wucewa ta gabansa amma hukuma ce a tsakaninmu.
FIM: Yanzu me za ka ce kan darussan da ka koya?
BASHIR: Na koyi darussa da dama, ciki har da zamantakewa da mutane.
FIM: Kana ganin za ka sake shirya wani fim nan gaba?
BASHIR: E. Ai wannan ba zai hana ni ba.
FIM: Me ya sa kuka ba Suleiman kwangilar tallata fim din alhali ba shi a cikin aikin fim din.
BASHIR: Tun lokcin da muke buga wakokin fim din a can Lenscope muka saba da shi har wada ya ce zai yi fim, aka gabatar da Suleiman din gare mu. To abin da ya hana ma a ba shi sai ya ce shi a Jos zai yi domin 'yan wasan Jos sun fi na nan biyayya da sanin abin da darakta yake so, to sai Wada ya share shi. Ba a dade ba ya sami Wada ya ce ya ba shi aron N5,000 wani dan'uwansa ya fado bishiya zai yi masa magani. Sai Wada ya tausaya masa ya kawo kyautar naira dubu goma ya ba shi ya ce kyauta ya ba shi. To again sai ya zo da script ya ce da Wada ga fim yana so ya yi amma yana so Wada ya biya, fim din zai ci naira dubu dari biyu. To sai Wada ya ce min, "Ka ji abin da ya ce, ga shi ba a gama da Qaya ba," don haka ba zai yi ba. To a karshe dai a haka muka yi tunanin ba shi ya yi marketing fim din.
FIM: Yaya dangantarka da shi yanzu?
BASHIR: Ba wani abu. Ko gobe za mu yi fim tare da shi, za mu ci abinci, sai dai ka san idan ka je gari ka ga mutanen garin da jela kai ma sai ka jawo ganye ka saka!
FIM: Mun gode. Allah ya kyauta.
BASHIR: Yauwa.
SHARI'ARMU DA SULEIMAN BA SASSAUTAWA, cewar Mista Kent
Suleiman ya ci kudin Qaya, amma shi ma kaya ta soko shi, inji furodusan
MALAM WADA ALI (Mr. Kent na cikin fim din Tsautsayin Takaba), shi ne wanda ya kai karar Suleiman a ofishin 'yansanda na 'Metro' a Kano sakamakon cinye kudin Qaya da dan wasan ya yi. Wakilinmu ya tattauna da shi a cikin makeken shagonsa na sayar da atamfofi da ke kasuwar Kantin Kwari. Tun da fari sai da suka yi magana kan asalin shi Wada, domin mutane da yawa ba su sani ba, da kuma dalilin da ya sa ba a cika ganinsa a finafinai ba a yanzu. Bismilla:
FIM: Za mu so mu ji ainihin sunanka na gaskiya.
WADA: Sunana Wada Ali.
FIM: Yaya ake kiranka da Mr Kent?
WADA: Sunan fim ne, a Tsautsayin Takaba.
FIM: Menene tarihin rayuwarka?
WADA: An haife ni a shekarar 1967 a garin Daura da ke Jihar Katsina. Na yi firamaren Bayajidda a 1973-1979, daga nan na yi sakandaren Daura a 1979-1984. Na tafi kwalejin share fagen shiga jami'a ta Zariya 1986-1989, sai na tafi A.B.U. Zariya a 1989-1993. Bayan na gama sai na fara aiki da Sosa OK Plast a 1993-1997, kuma a lokcin na fara shiga harkokin finafinan Hausa.
FIM: A wace shekara ka fara harkar fim kenan?
WADA: A 1994, a matsayin dan wasa kuma wanda ya rubuta labari.
FIM: Finafinai nawa ka rubuta labaransu?
WADA: Tsautsayin Takaba, Jikan Hardo, Ke Duniya, Dan'uwa, sai kuma Qaya.
FIM: Kafin fitowar fim din Qaya, mun ji ka yi shiru har an fara mantawa da kai. Me ya faru?
WADA: Abin da ya sa na daina harkar fim a baya shi ne, na farko akwai cin amana daga daraktoci; duk yadda ka amince musu a karshe sai sun ba ka kunya, sannan da rashin kyawon kasuwar finafinan, sannan ga uwa uba rashin hadin kai, kowa yana jin haushin kowa, wannan ba ya son wancan ya ci gaba
FIM: Mecece alakarka da furodusan fim din Qaya?
WADA: To a takaice dai sai in ce dan'uwana ne.
FIM: An ce an sami wani sabani tsakaninka da daraktan fim din.
WADA: E to, amma dai tunda ya mutu bai kamata a yi maganar ba, amma da yana da rai da sai in fadi duk abin da ya faru. Tunda mu Musulmi ne ina ganin a bar wannan maganar kawai.
FIM: Har ila yau an ce kun yi rikici da wani a kan fim din.
WADA (ya yi gyaran murya): Haka ne. Akwai wani yaro Suleiman, saboda kaunarsa da nake yi a matsayinsa na dan fim, sai na kira shi na ce ina so ya yi mani kasuwancin fim din, to amma daga karshe sai ga shi ba fim din ba kudin ba kuma dalilinsu.
FIM: Ba ku yi wani tsari ba ne da shi?
WADA: Da farko lokacin da na yi masa maganar sai ya ce ya yarda amma sai na ba shi jari na naira dubu dari. To daga baya shi da kansa sai ya je ya yi tunani ya dawo ya ce za mu yi a kan kaso (percentage), zan ba shi naira dubu talatin.
FIM: To a ina aka sami matsala kenan?
WADA: You see, bayan lokacin da aka yi za a kawo kudi sai ya ce ai 'yan kasuwa ba su biya ba. Da na ga dai abin yana nema ya zama rainin hankali sai na hada shi da polis aka fara yin bincike a nan 'Metro Police Station.' Da 'yansanda suka yi bincike sai suka ga ashe ya karbi kudin, karya yake musu. To da yana tsare sai aka yi wa Hamisu Iyan-Tama waya; shi ne ya je ya karbi belinsa.
FIM: Maganar ta mutu kenan?
WADA: A'a. Suna nan dai suna bincike tukuna.
FIM: A karshe idan suka kasa gano komai suka sallami maganar fa?
WADA: Tab! ai wannan magana babu sassautawa; idan suka sallami case din sai in tafi kotu. Ina tabbatar maka ba zan yarda ba!
FIM: Wace shawara gare ka ga masu irin wannan halaye nasa?
WADA: Na fada maka abin da ya sa na fita daga harkar kenan a baya. Cin amana da yaudara. To ya kamata masu irin halayen Suleiman su gane cewa kashe harkar nan suke yi, ba gyara ta ba. Misali, idan ka dubi kamar ni ka ga shagona nan inda nake harkata (shagunan atamfofi ne sun fi na miliyan a ciki); don haka ba wai da fim din na dogara ba. To amma idan irinmu da muke da sha'awar dan tsoma hannu a ciki kuma haka tana faruwa, to me kake zato?
FIM: A karshe wace shawara gare ka ga industiri din baki daya?
WADA: Kirana shi ne hadin kai, rikon amana, son juna da kishin harkar. Mu tsaya mu yi wa harkar aiki ko da ba mu za mu ci gajiyarta ba. Kuma ina son in yi kira ga gwamnati ta farka ta zo domin sana'a ce da ke da dubban mutane da yawa suke cin abinci a cikinta. Hukumomin tace finafinai kada su rika matsa wa finafinan Hausa. Ya kamata gwamnati ta lura cewa finafinan Hausa fa ba sa dauke da wani abu na batsa, fim ne da za ka iya kalla kai da 'ya'yanka, ba wani taraddadin ko za a yi wani abu maras kyau. Gwamnatin nan ita ce take kula da gidajen STV da NTA kuma aka yarda suke nuna fim din karshe na Turawa masu nuna iskanci da wakokin Turawa, amma duk ba a hana su ba ko an sa musu ido, sai na Hausa kawai don dan abin da aka ga ana samu. To lallai ina son gwamnati ta farka ta lura da wannan. Sannan ina son mujallunku su buga hotunan duk ma'aikatanku domin sau uku ana zuwa ana cutata kudin talla wai a ce za a sa a mujalla. To ka ga idan da hoto kuwa, shikenan. A karshe shi kuma Suleiman ya ci kudin Qaya, amma 'kaya' to soko shi.
FIM (dariya): To Malam Wada mun gode.
WADA (ya yi dariya): Ni ma na gode.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|