WASU gungun furodusoshi sun sake daura sabuwar aniyar ganin bayan mujallar Fim, yayin da suke amfani da wani sharhi da aka buga cikin mujallar ta watan jiya a matsayin madogara.
Sharhin, mai taken "Har Mun Cika Shekara Uku!", ya fito ne a shafi na 2 na mujallar kuma Babban Editan Fim, Malam Ibrahim Sheme ne ya rubuta shi don juyayin cika shekaru uku da kafa mujallar.
Wakilanmu sun sami cikakken bayanin haushin da sharhin ya ba wasu 'yan fim.
Masu kumfar baki a kan sharhin sun yi kwakkwarar suka a kan Sheme da mujallar saboda wasu kalamai da ya ambata a cikin sharhin nasa, musamman inda ya ce ana aikata ayyukan assha a harkar.
Sakamakon rubutun, 'yan fim da dama, musamman a Kano, sun aibanta marubucin da mujallar, suna cewa ya kamata a hukunta su "kamar yadda ake hukunta dan fim da ya yi laifi." Suka ce masu harkar fim ba za su sami sakat ba muddin ana buga mujallar Fim da sauran mujallu ire-irenta.
An ji daya daga cikinsu yana cewa, "Ai ni, ko ba wanda zai yi wani abu, ni zan yi; ni sai na ga bayan wannan mujallar; ku kuke ganin amfaninta amma ni sai na durkusar da ita."
A wani taro da aka yi a ofishin wani darakta a Kano, a makon da aka yi auren Shu'aibu da Balaraba, wani dan wasa ya kawo shawarar a kafa wata sabuwar mujalla wadda za ta yi hamayya da Fim, sa'annan a umarci kowane dan fim ya mara mata baya.
Mun so jin ba-bakin masu korafi kan sharhin, amma duk wanda aka nufa sai ya noke. Wani fitaccen dan wasa ya ce, "Ni ban yarda mutum kamar Sheme zai so ya ruguza harkar fim da gangan ba, domin na san shi na san akidarsa. Ina so ka gaya mani wani mutum guda daya rak a Industry wanda ya fi Sheme son habaka shirin fim na Hausa. Mujallar Fim ai albarka ce ga Industry. Abin kunya ne surutun da wasu ke yi a kan wannan abu.
"Kuma shi Sheme da ake cewa wai yana so ya rusa sana'ar fim, shi sana'ar me yake yi? Ai in babu 'yan fim shi ma ba zai buga mujallar ba. Shin ba kwanan nan ma ya shirya fim dinsa Gagarabadau ba?"
Da wakilinmu ya tuntubi Malam Ibrahim Sheme a kan wannan muhawarar sai ya ce, "E, ni ma an gaya mani wasu sun ji haushin sharhina, suka ce wai zan zubar wa da 'yan fim mutunci. To, ka san kowane mutum da iyakar fahimtarsa. Ba mamaki jin hakan.
"To amma ka gane, ni ba na da wani nufi na cin zarafin wani ko wata, amma na san tunda wannan abu (buga mujalla) kamar kasuwanci ne, tilas ka samu masu goyon bayanka da wadanda suke ganin ko menene za ka yi ba za ka burge su ba. Kamar yadda na fada a sharhin da ake ce-ce-ku-ce a kansa, in da manufar wannan mujalla ita ce cin zarafi da gangan, to da yanzu ta durkushe, domin kuwa Allah ba azzalumin kowa ba ne.
"Duk da haka, ina ba da hakuri ga duk wanda bai ji dadin wancan kalami nawa ba. Da ma yana da kyau idan an yi wa mutum wani abu ya ji bai ji dadi ba, ya fito ya fadi. Kuma wannan hayaniyar ta karantar da ni wani nau'i na aikin jarida, da kuma halin dan'adam."
Sheme ya ce ya yi mamakin kalaman da ya ji wasu 'yan fim suka furta a kan maganar, domin "ba su ne suka dace da fadin irin maganganun ba." Ya ce ba da dadewa ba zai yi bayani a kan ainihin matsayinsa kan al'amarin.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin