Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 29   Mayu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Rayuwarmu
Mu Leka Hollywood
Malam Zurke
Mutanen Boye
Bukukuwa
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Akwai:
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 



Mu rika karfafa shari'a a finafinanmu


Inji Amina Muhammad, Jarumar shirin TABBAS

Daga ABUBAKAR MAIHOTO a Gusau

A MINA MUHAMMAD fitacciyar 'yar wasa ce da ke zaune a garin Gusau, hedikwatar Jihar Zamfara. Ita jarumar shirin Tabbas, wanda aka shirya a Zariya. Bayan haka ta fito a finafinai da dama, wadanda suka hada da Babu Maraya..., Mutum Ko Aljan?, Gudun Hijira, da kuma Sukuwa. A cikin dukkan wasannin da ta yi, Amina ta nuna hazaka kwarai, wadda ta sa ake ganin da a Kano ko Kaduna take, inda aka fi yin finafinai, to da tutarta za ta fi kadawa sosai. Duk da haka, Amina ta gamsu da inda take zaune, wato Gusau, inda take aiki a Hukumar Raya Fasaha da Al'adu ta Jihar Zamfara.

Shin wacece Amina Muhammad? Menene ra'ayinta kan wasan Hausa, musamman wasu bangarori nasa kamar rawa da waka? Kwanan baya, wakilinmu na Jihar Zamfara ya sadu da jarumar inda suka tattauna a kan rayuwarta:

Fim: Malama, zan so in san sunanki tare da takaitaccen tarihinki.

AMINA: Assalamu alaikum. Sunana Amina Muhammad kuma ni haifaffar Gusau ce. Na tashi a cikin garin Gusau, na je wurin kanwar innata a garin Funtuwa na zauna. Na yi karatun sakandare a Funtuwa. Da na gama sai na dawo gida Gusau, na nemi aikin gwamnati na samu. Ina aiki ne a Hukumar Raya Fasaha da Al'adu ta Jihar Zamfara (Council of Arts and Culture Zamfara State).

Fim: Menene dalilin son ki da wasan Hausa?

AMINA: Wata rana ina kallon fim din Hausa sai na yi sha'awar irin abubuwan da ake yi ciki na fadakarwa. Wata rana tafiya ta kama ni zuwa Kaduna. Matar yayana ce ta haihu. Da na je sai na zauna a Kaduna na wani dan lokaci ina zuwa karbo finafinan Hausa a wani video centre. Rannan sai wani mutum ya ce mani mi yas sa duk lokacin da zan zo ba ni da wani fim sai na Hausa? Sai na gaya masa ba ni da wani ra'ayin fim sai wanda yake nuna al'adarmu, ina kuma jin dadin yadda Kanawa suke kokarin hakan tare da mutanen Kaduna. Sai ya ce to in dai har ina da ra'ayi mi ya sa ba zan je inda ake shirya fim in fito a cikin fim ba? Sai na ce masa, "Ai ban san wajen wa zan je ba, wallahi da na je." Daga nan sai ya ce mani akwai wani fim wanda za a yi. Shikenan sai na ce mashi ina yi. Ana nan ana nan sai rannan mai fim din sai ya zo ya yi mani magana bayan da aka yi masa magana da ya zo muka yi magana sai ya ba ni takarda na sa hannu. Bayan na sa hannu sai aka dage fim din saboda rikicin Kaduna. Kuma a lokacin ni hutuna ya kare, sai na dawo gida. A lokacin da na sake komawa Kaduna domin shirya fim din sai hakan bai yiwu ba saboda Allah bai kaddara da ni za a yi fim din ba, amma ina nan aka kare komai. Ina nan sai wani furodusa da ke Zariya ya zo, ana kiransa Alh. Tukur. Da man an gayyace shi yana cikin wancan fim din na Wasila, sai ya yi wa wani mutum magana. Sai ya tambaye ni saboda da man mun saba da shi saboda shi yana Arts and Culture Kaduna State ni kuma ina Art and Culture Zamfara State. Sai na sanar da shi dalilin zuwana wannan wurin. Sai ya zama manajana, ya kai ni wajen Alh. Tukur yai mashi magana. Sai ya ce za su yi wani fim wanda ake ce ma Tabbas, ya ce yana son in fito a cikin fim din, zan iya? Sai na ce mashi insha Allahu zan iya. Shikenan aka ba ni rana cewa gobe za a fara. Daga Kaduna na yo Zariya na zama jarumar fim din Tabbas.

Bayan na kara dawowa gida, aka sake kirana zuwa Zariya na je na yi fim din Mutum Ko Aljan? Bayan na dawo aka sake kirana na je na yi fim din Gudun Hijira. Ina dawowa gida sai Aliyu Bulala na nan garin ya kira ni ya ce mu je Sokoto za a yi wani fim a can an gayyace mu. Shikenan sai muka tafi Sokoto tare da shi; shi ma ya zama manajana kenan.

Fim: Yaya sunan fim din da kuka je Sokoto kuka yi?

AMINA: Shi ne Sukuwa. Amma a lokacin da muka je wuri ya riga ya kure babu wurin da za a sa ni, to sai aka maida ni na fito a matsayin uwar yarinyar cikin fim din saboda wurin da zan zauna ganin ba mu zo da wuri ba an sa wani wurin. To amma ganin mun taso tun daga Gusau har Sokoto aka sa ni a uwar.

Bayan mun dawo gida na ci gaba da zuwa wurin aiki. Da man nan Gusau ina da darakta kuma manaja kuma maigida, shi ne Sani Bello. Sai ya zo ya ce mani za a yi wani fim a Gusau yana son in zamo wanda za su yi wasa a ciki. Sai na amsa masa na ce to insha Allah in dai harka tasa ce kowace iri ce zan yi in dai ya shafi harkar wasa ce saboda shi ne manajana, komai nawa a cikin Gusau, saboda dalilinsa na fara duk wani wasa a cikin Gusau.

Fim: A halin yanzu wadanne finafinai kika fi so?

AMINA: A gaskiya koda yake Gudun Hijira bai fito ba ina sonsa saboda ina cikinsa saboda ya fi ba ni dariya da kuma sha'awa.

Fim: Wane fim ne ya fi ba ki wahala?

AMINA: Babu wanda ya fi ba ni wahala irin Tabbas, don gaskiya na sha wuya a wurin waka. Ba furodusa ko darakta ne ya ba ni wahala ba, sai saboda kasancewata bakuwa a garin. Sannan shi ne fim dina na farko a wani gari. Sannan ni kadai ce daga Gusau. Amma ka ga kafin in je Zariya na yi wani a nan Gusau, shi ne Babu Maraya Sai Raggo. Sani Bello shi ne ya yi mani jagora. Babu wata matsala tunda ina gida, amma ka ga daga Zariya zuwa Kaduna na sha 'yar wahala saboda rashin idon sani don ba ni da aboki, dole na dauka kamar mun shekara goma tare da su amma tabbas wurin waka na 'yar wuya.

Fim: Yaya kike ganin sha'anin finafinai suke tafiya kasancewar yanzu an zo wani lokaci na Shari'a, ana ta kira ga jama'a da su guji kallon finafinai wadanda ake yi a Kudancin kasar nan da kasashen waje?

AMINA: Abin da zan ce da man ai mu Hausawa ba al'adarmu ba ce mafi yawancin al'adun da Kudanci suke amfani da su. Amma ai mun ce fadakarwa za mu yi a a cikin fim don jama'a su kalla don su gane gaskiya da aiki da ita, su guje ma karya. Saboda haka ai ka ga ba mu kama hannu ko rungume juna kamar yadda suke yi; ka ga wannan muguwar al'ada ce daga kasar waje wanda yake ko Musulmai ba sa iya yin ta. Saboda haka fim din mu ba mu son mu samu wata mishkila a cikinsa gaba daya wacce ta saba wa Shari'a, ba ma son komai ya taba mana Shari'armu domin muna son mu kara karfafa Shari'ar a cikin fim dinmu. In ka lura su ma finafinan Kudanci daukaka addininsu suke yi. Ya kamata mu ma mu daukaka namu addinin. Bai kamata a ce gaba daya an gama fim ba makarantar Islamiyya ko ta allo a cikinsa ba. Ya kamata su gane cewar mu ma mun san abin da muke yi kamar yadda suke yi wajen koyar da tsafin da suke yi. Mu ma muna da babban kundi wanda duk duniya shi ne na daya kuma babu na biyu balle ne na uku ko na hudu. Saboda haka ga da ma nan da za mu yi amfani da ita wajen yaki don dawowa hanya ta gaskiya.

Ana iya nuna mara lafiya a jawo wata ayar Alkur'ani a nema masa magani da ita; sai ka ga wanda ba Musulmi ba ya yi kokarin haddace ta don dai kawai ya gwada ta ya ga ko da gaske ne. Da zarar Allah ya yarda sai ka ga ya shiryu. To ka ga fim ya yi jihadi kenan.

Da man abin da yake bata mani rai da kallon fim din Kudu shi ne kokarin nuna addininsu shi ne ya fi na kowa. Babu yadda za a yi ka kalli kaset hudu babu addini a ciki. Saboda haka don Allah don Annabi mu ma mu yi kokari wajen saka addini a cikin namu. Ya kamata ko makaranta a ce ga ta ana karantun Kur'ani a cikinta.

Fim: Akwai wasu al'adu da mutane suke ganin na aro ne kuma suna daga cikin abubuwan da ke bata tarbiyyar yara, kamar haddace wakar fim to amma yaro bai haddace allonsa ba. Me za ki ce a kan haka?

AMINA: To furodusoshi na farko su suka fara bata shirin wannan tsarin da suka kawo wadanan abubuwa. Mutanenmu sun riga sun dauki wata dabi'a cewa in fim babu waka da kyar za ka ga jama'a suna rububin su kalle shi. Sai wani ya ba ka labarinshi amma da zarar kaset na rediyo ya fito sai ka ga fim ya samu daukaka saboda wakar ta riga ta yadu. Ka gane? Amma ni abin da gaskiya a yadda rayuwata take da yadda nake so, ba na ra'ayin waka a fim saboda wallahi wurin fim din Tabbas na wahala a wurin waka. Waka a fim ba aladarmu ba ce; in al'adarmu za a yi ta waka ai akwai al'adunmu, akwai 'yar fade irin wanda a da can ake yi. Ko yanzu ana ganin kamar lokacin ya wuce? Babu abin bakin ciki sai ka ga babban namiji ko babbar mace tana rera waka tare da namiji a cikin fim. Ni wallahi duk fim din da nake kallo zan tare waka idan na kawo wurin.

Fim: Shin kin taba yin aure?

AMINA: E to, a gaskiya na taba aure, amma a halin yanzu ba ni da miji. Ina neman masoyi ne. Ka dai gane kai ma.

Fim: Ko kin taba haihuwa?

AMINA: U'un, da sauki, da saura. Muna rokon Allah in ya sa muka samu wanda muke so, Allah ya ba mu haihuwa.

Fim: Na gode kwarai.

AMINA: Ni ma na gode.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin