Yadda hadarin jirgi ya shafi wasu 'yan fim
Kannen Sani Lamma sun rasu, kuma gidan su Rabi'u 'Lalala Action' ya kone
Daga BALA MOH'D BACHIRAWA da SANI MOHAMMED MAI KATANGA
Wasu konannun sassan jirgin da ya fado a Gwammaja
| A FARKON watan jiya ne bala'in hadarin jirgin sama ya auka wa birnin Kano, ya jawo salwantar rayuka kimamin 100. Yawancin mazauna gidajen da jirgin ya fada kuma sun sami munanan raunuka. Daga cikin wadanda dukiyarsu ta salwanta ta hanyar gobara, akwai wani dan wasan fim mai suna Haruna Rabi'u, wanda aka fi sani da Baba Kusa. Cikin wannan labari za ku ji asarar da dan wasan ya yi da kuma wasu bayanai da sauran mujallu ko jaridu ba su ba ku su ba.
MUTANEN da ke zaune unguwar Gwammaja da ke cikin Karamar Hukumar Dala a birnin Kano sun sami kansu ciki hargitsi da bala'in da ba su taba tsamanin a rayuwarsu zai same su ba. Misalin karfe 2 na yamma ne wani jirgin daukar fasinjoji ya fado a kan wasu gidajen da ke cikin unguwar. Jirgin, wanda ke dauke da fasinjoji kusan 80, cikinsu har da Ministan Wasanni, Mista Ishaya Mark Aku, da matar tsohon Ministan Abuja, Mrs Julie Useni, ya konekurmus tare da fasinjojin. Mutane biyu ne suka tsira da ransu, wadanda daga baya su ma suka ce ga garinku. Jirgin, mai lamba BAC 1-11-500 mallakar kamfanin EAS, ya fado ne bayan tashinsa da niyyar tunkarar birnin Legas. Daga Legas ya tashi a ranar, ya je Jos, daga can ya zo Kano ya debi fasinjoji.
Marigayi Alh. Hamisu Lamma
| Wani abin gigita game da hadarin shi ne rasuwar wasu bayin allah su biyu, Alhaji Sadi Lamma da Alhaji Hamisu Lamma. Mutanen biyu wa da kane ne kuma dukkansu kanne ne ga Alhaji Sani Lamma, wani fitaccen dillalin kaset na finafinan Hausa.
Alhaji Sani Lamma, wanda yana daya daga cikin 'yan kwamitin Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano masu kula da gidajen sinima da na kallon bidiyo, ya shaida wa mujallar Fim yadda 'yan'uwan nasa biyu suka rasu. Ya ce da ma shi Sadi Lamma baWasu konannun sassa na jirgin da ya fado a Gwammajashi da lafiya to sai Hamisu ya zo ganinsa tare da wasu mutane. Bayan sun gaisa ne ya fito gidan zai shiga mota abin ya faru. Lokacin da jirgin ya yi kasa-kasa sai ya rika zubar da man da ke cikin tankinsa. To wannan mai ne, inji Sani Lamma, ya zubo wa Hamisu ya kone shi tare da motarsa.
Wannan bala'a duk a kan idon mara lafiya Sadi aka yi shi, yana kan bene yana kallon dan'uwansa na cin wuta. A wurin ya gigice, ya kidime har abin ya kai shi ga fara sambatu. Shi ma washegari sai ya rasu. Shi Sadi dan kasuwa ne wanda can baya ya taba yin wata doguwar tafiyar da sai da aka rika cigiyarsa.
Marigayi Alh. Sadi Lamma
| Alh. Sani Lamma ya taba rike kyamara tun farkon fara harkar fim. Sun yi wani fim na Turanci mai suna The Raiders, sai Turu da kuma wani shirin Canis na Hausa. Allah ya jikan Sadi da Hamisu Lamma, amin.
Wani dan wasa mai suna Haruna Rabi'u (Baba Kusa) ya tsallake rijiya da baya inda wani sashe na jirgin ya kone gidansa. Ga wata hira da ya yi da mujallar Fim a cikin gidansa da jirgin ya washe.
Fim: Da farko muna so mu ji sunanka.
Haruna: Sunana Haruna Rabi'u Baba Kusa, amma an fi sanina da sunan 'Lalala Action.'
Fim: Kai dan wasa ko furodusa?
Haruna: Ba furodusa ba ne ni, ni dan wasa ne.
Fim: Kamar wadanne finafinai ne ka fito a cikinsu?
Haruna: Na fito a cikin Zato, Haske Biyu, Kantafi, Kowa Ya Tuna Bara na 1 da na 2, da sauransu.
Fim: Lokacin da hadarin ya faru kana ina?
Haruna: Ina cikin G.S.S. Gwale.
Fim: Na ga kai ma gidanku ya kone.
Lalala: Kwarai kuwa, ya kone.
Fim: Akwai wanda ya mutu ne a gidanku?
Haruna: Babu wanda ya mutu; domin ina zuwa na taimaka wajen fitar da duk wanda ke gidan har ma da na makwabtanmu.
Fim: Daga cikin wadannan dakuna da suka kone ko akwai wasu kayayyaki da suka shafi harkar fim?
Malam Haruna Rabi'u a gigice..cikin gidansu da jirgin ya babbake
| Haruna: Babu, sai dai kawai kaset kaset na bidiyo da kuma bidiyon, da sauransu.
Fim: Lokacin da abin ya faru hankalinka ya tashi?
Haruna: Ai dole ne, domin ji na yi cikin ya dume, ban ci abinci ba kafin lokacin amma sai na ji ko yunwa ba na ji. A ranar kuma barci bai yiwu ba saboda tsananin tashin hankali.
Fim: An ce gwamnatin tarayya ta ba ku taimako na naira miliyan 10. Shin wannan kudin zai ishe ku?
Haruna: Wannan sam ba za su isa ba domin miliyan 10 ko a gidan Alhaji Yusuf Habibu sai ta kare, wato wanda gangar jikin jirgin ta fada kan gidansa.
Fim: Mun ga gidaje da yawa sun ruguje wasu kuma sun kone. Kai kana ganin za su kai nawa?
Haruna: Gida 21 ne suka kone, sa'annan 19 ne suka ruguje.
Fim: 'Yan unguwarku wadanda jirgin ya fada masu da suka mutu za su kai nawa?
Haruna: Na san mutum goma sha biyu duk sun mutum wadanda duk na san su, sa'annan ashirin da biyu da na sani sun kone.
Fim: Akwai wani ko wasu 'yan fim da suka zo don yi maka jaje?
Haruna: Akwai darakta Maikudi Bawa, ya zo ya kuma jajanta min. Sa'annan kungiyarmu ta 'Dala Traditional' ta turo wakilai domin yi min jaje. Shugabanninmu kuma sun ce su ma suna jaje.
Fim: Allah ya kiyaye.
Haruna: Amin, na gode.
Kafin jirgin ya rifta kan gidajen jama'a kuwa, wani matashi dan shekara 22 mai suna Kabiru ya shaida wa mujallar Fim cewa yana tsaye a Kofar Ruwa kusa da Tashar Kuka "sai muka ga jirgin yana mashalo a kasa-kasa, wasu sam ba su fahimci abin da ya faru ba, sai suka yi tsammani ko sojojin sama ne ke atisaye". Kabiru ya kara da cewa, " Ni kuma sai na ce ai jirgin sojoji kore ne (green)." Daga nan, inji shi, sai suka ga ya yi kasa, kura ta turnuke, kuma wuta ta tashi.
Wata majiya ta ce jirgin lafiya lau ya iso Kano daga garin Jos , amma yana tashi daga filin jirgin na Malam Aminu Kano mintuna biyu kacal sai ya fado. Lokacin da jami'an harkar tashin jirage a filin jirgi suka fahimci halin da ake ciki, wata majiya da ta nemi boye sunanta ta furta cewa an nemi matukin jirgin da yin saukar gaggawa a cikin wani kududdufi da ke bayan makabartar Sheik Nasiru Kabara. Jirgin ya fadi taku kadan kafin ya kai ga kududdufin.
Dukkan fasinjojin jirgin in ban da daya daga cikin direbobin da kuma wani fasinja daya mai suna Najib Ibrahim duk sun kone. Mafi yawan wadanda suka kone kuwa ba a iya shaida su. Ita kanta matar tsohon Ministan Abuja Jeremiah T. Useni, ba a shaida ta ba. Wakilinmu da aka rika zakulo gawarwaki a gabansa ya shaida cewa lokacin da wasu mutane daga Jos suka zo don karbar gawar matar tsohon ministan, an yi tankiya yayin da suka nuna gawar wata suka ce tasu ce. Nan take 'yan'uwan matar suka ce tasu ce. Don tabbatar da shaida sai kuma mutanen suka ce su 'yar'uwarsu tana da juna biyu. Da aka tambayi dangin matar Janar Useni din idan tana da ciki, sai suka ce a'a.
'Yan kungiyoyi agaji daban-daban da suka rika kwashe gawarwaki sun rika kai su Asibitin Murtala Muhammed da kuma asibitin sojojin sama da ke Ashton Road, duk da cewa an hana 'yan jarida shiga asibitin wakilinmu da ya samu shiga ya gano cewa dakin ajiye gawa a asibitin sojojin yana da matukar tsafta sai dai kuma wani wakilin namu da ya je dakin ajiyar gawa na Asibitin Murtala ya yi fatan kada Allah ya kara kai shi wurin.
Ranar Litinin ne aka tattara gawarwakin mutanen da suka rasa rayunkansu aka nade su cikin likkafani bayan an yayyafa masu ruwa, aka kwashe su cikin motar kwasar kasa (tipper) guda hudu aka kai su kofar gidan mai martaba Sarkin Kano aka yi masu salla. Dimbin jama'a sun halarci wurin. Bayan an gama ne kuma sai aka rarraba su a makabartu daban-daban aka rufe su.
Daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su akwai wata Baturiya da wasu Turawa suke je suka karbi gawarta.
An dan samu sabani tsakanin jami'an tsaro 'yan sanda da kuma sojojin sama a wurin da hadarin ya auku. Sabanin ya faru ne bayan an tattara wasu kudade da kayayyaki masu daraja daga cikin rugurguzajjen jirgin. Yayin da su 'yan sanda suka nemi a ba su kudaden su tafi da su domin bincike, su koma sojojin sai suka nuna cewa su ya kamata su tafi da kudin domin aikin da suke yi suna yi ne a madadin kamfanin jirgin. Su kuma jami'an kamfanin jirgin har aka kwana biyu da kammala kwashe gawarwakin ba su zo wurin ba. Binciken da Fim ta yi ya gano cewa sun ki zuwa wurin ne don gudun kada fushin jama'a ya kare a kansu. Shi kansa shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ya ziyarci wurin kwana daya da hadarin, ya je ne da misalin karfe 6 na safe kuma ya bar Kano awa daya kacal da zuwansa. Da alama yana gudun kada abin da ya faru kan mataimakinsa Atiku Abubakar shi ma ya faru a kansa. Shi dai Atiku jama'a sun yi masa a-ture da kasa kuma an tozarta shi a ranar da hadarin jirgin ya faru a dakin motsa jiki na dandalin 'Sani Abacha Sports Complex' a Kano. Abin ya faru ne wurin kaddamar da wani littafi da aka rubuta kan tarihin Danmasarin Kano.
Duk kuma da cewa gwamnatin tarayya ta ba da taimako na Naira miliyan 10, hakan bai sa jama'a sun fasa la'antarta ba. Ita kanta gwamnatin Jihar Kano ta sha suka musamman ganin cewa babu abin da ta yi lokacin da abin yana zafi-zafi.
Ana wata kuma sai ga wata. A ranar da Ministar Zirga-zirgar Jiragen Sama, Miss Kema Chikwe, ta bada sanarwar soke amfani da jirgi kirar BAC 1-11500, wani jirgin ya tsallake rijiya da baya, inda ya kusa yin hadari a filin jirgi na Malam Aminu Kano. A daidai lokacin da ake rubuta wannan labarin kuma bayani ya iso ofishin mujallar Fim cewa mutane biyu din nan da suka tsira daga cikin jirgin da ya fado su ma sun mutu.
Allah ya jikan Musulmin da suka rasu kuma ya kyauta gaba, amin.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|