Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 31   Yuli 2002
BABBAN LABARI

BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN

Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

Wulakanci a bikin Abida!

A bikin Abida
Baballe Hayatu, Zahra'u Shata, Ahmed S. Nuhu, Rukayya Umar Santa, a zauren walimar da aka yi dabdala da su a Ni'ima Guest House

Daga WAKILANMU a Kano

An daura auren Jarumar Jarumai Mata, Abida Mohammed, da furodusa Hamza Mohammed Danzaki, da misalin karfe 10 na safe. Lokacin da wani wakilin mujallar Fim ya isa kofar gidan da za a daura auren a cikin Fagge, Kano, da misalin karfe 9:25, ya tarar babu kowa sai dai kawai an shimfida tabarmi ana jiran isowar jama'a. Yaran da ke tsaye a kofar gidan suka tambaye shi, "Daurin auren Abida ka zo?" Da ya duba bayansu sai ya ga wata motar sojoji kirar Fijo mai tambarin 'PATROL TEAM.' Sojojin da ke aiki ne aka dauko don kare lafiyar wasu 'yan wasa.

Daga nan sai wakilin namu ya garzaya Sabon Titi bakin ofishin angon, wato 'Home Alone Production'. A can ya ga wasu 'yan fim da suka fara hallara. Sun hada da Adamu Kwabon Masoyi, Bala Anas Babinlata, Abubakar mijin Maijidda Abdulkadir, da sauransu. Sai wajen karfe 9:50 aka fara taruwa sosai. Sai ga Saminu, furodusan Laila, da Kabiru Iyan-Tama, Aminu Shehu Ilu Dambazau, Aminu A. Shariff (Momo), Rabi'u Ibrahim (HRB), Yusha'u, Hafizu Bello, Ibrahim Maishinku, darakta Aminu Shariff Hassan, Isma'ila I.U.I., da Abdurrahman I.U.I. Ango da abokansa irin su Ahlan Yoko sun yi anko na farin yadi. Tare aka dunguma zuwa wurin daurin auren.

'Yan wasa da jama'ar gari da yawa sun halarci daurin auren. A kofar gidan daurin auren, wani darakta ya ce wa wakilinmu, "Abin bakin ciki ne a ce Abida za ta yi aureamma ba a sanar da duniya ba. Dubi dai auren Fati! Wannan ko rabi rabinsa bai kai ba."

Kamar yadda aka saba, yara sun rika bin fitattun 'yan wasa rii suna kallonsu. Sai da ta kai sojoji biyu sun kakkare Ali Nuhu har ya shiga motarsa ya fice daga wurin. Shi ma shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama, jama'a sun yi ta binsa duu kamar kudan zuma shi kuma yana daga masu hannu.

Bayan an daura auren, sai aka koma bakin 'Home Alone Production', aka taru. Daga nan sai aka dunguma zuwa wurin cin abincin rana a unguwar Kabuga Jan Bulo wadda ke wajen birni daga yamma. Daga nan ne kuma da yamma aka tafi yin walima a otal din 'Ni'ima Guest House' da ke kan titin 'Sulaiman Cresent'.

Daruruwan jama'a da suka kunshi 'yan fim da kuma masoyan Abida sun yi da-na-sanin zuwan da suka yi otal din domin halartar walimar auren. Tun safe an raba katin gayyata, aka rubuta cewa za a fara yin taron da karfe 5:00 na yamma. Ya zuwa karfe 5:10 kuwa mutane har sun hallara otal din. Amma saboda matsalar rashin kai kayan kida da wuri, ba a fara gudanar da biki ba sai kusan karfe 8:00 na dare. Su kansu ango da amarya sai kusan wannan lokacin suka je.

Lokacin da aka bude kofar shiga dakin walimar, an umurci wasu sojoji da ke dauke da bindigogi da bulalai su tsaya a kofar, kada su bar kowa ya shiga sai mai kati a hannu. Wata majiya ta sanar da wakilanmu cewa katin gayyata 200 aka raba. Haka aka fara shiga ana nuna kati. Lamarin ya fara kazancewa ne sa'adda masu katin da suka yi dafifi domin shiga suka ga ana ta yin shigar-kutse da 'yan alfarma marasa kati. Su kuma sauran jama'a da ba su da kati sai suka rika matsawa suna nuna sani don kokarin shiga. Ko kafin mai kati ya ankara tuni har sojojin sun fara labta wa masoyan na Abida bulala. Wata mata ta ba jama'a tausayi lokacin da aka rika jibgarta da bulala mai harsuna rututu. Da abin ya yi zafi sai da ta kai ba wanda ba a daka ba, kama daga mai katin shiga har maras katin. Bayan an dauki lokaci mai tsawo kuwa, sai gaba daya aka hana masu kati shiga, aka ce, "Wadanda ke ciki sun isa haka".

Daga cikin fitattun jama'a wadanda suka sha duka har da Jamila Haruna, wadda ta fusata amma daga bisani ta shiga; da Sulaiman Gambo Awaisu, jarumin shirin Alaqa, da kuma jarumi Ahmed S. Nuhu; wani matashi kuma mawaki da aka fi sani da suna 'Mai Dawayya,' ya sha dukan tsiya a kokarinsa na shiga. Tun kafin a zo, matashin dai ya yi ta yin ganganci da babur a bakin ofishin Hamza da ke Sabon Titi don nuna murnar aurensa.

Haka dimbin mutane da suka ci ado suka yi tsaye cirko-cirko a wajen dakin. 'Yanmata wadanda ba 'yan fim ba da suka cabo ado don taya Abida murna wasunsu sun sha jibga. Dalilin gudun bacin rana ne ma ya sa dimbin 'yan fim manya da dama ba su shiga ciki ba. Mujallar Fim ta ga wani darakta ya yi kyauta da nasa katin, ya juya ya koma inda ya fito, yana tsaki. Mudassir Haladu ('Young Producer'), cewa ya yi, "Ga katina a hannu amma ba zan matsa ba don kada a doke ni a buga a mujalla". Wani dan wasa kuma ya ce, "Wallahi nan suka shanya ni wai in jira za su aiko min da kati. Amma ba komai, da ban zo ba ai da ba su wulakanta ni ba!"

Da ma tun kafin a fara shiga sai da wakilan mujallu daga Garkuwa, Nishadi, Annur, Sharhi, Marubuciya da kuma Fim suka wakilta editan Fim, Ashafa Murnai Barkiya, ya gaya wa 'yan kwamitin gudanar da walimar cewa su ba su da katin shiga, sabodaamma ba a sanar da duniya ba. Dubi dai auren Fati! Wannan ko rabi rabinsa bai kai ba."

Kamar yadda aka saba, yara sun rika bin fitattun 'yan wasa rii suna kallonsu. Sai da ta kai sojoji biyu sun kakkare Ali Nuhu har ya shiga motarsa ya fice daga wurin. Shi ma shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Alhaji Hamisu Lamido Iyan-Tama, jama'a sun yi ta binsa duu kamar kudan zuma shi kuma yana daga masu hannu.

Bayan an daura auren, sai aka koma bakin 'Home Alone Production', aka taru. Daga nan sai aka dunguma zuwa wurin cin abincin rana a unguwar Kabuga Jan Bulo wadda ke wajen birni daga yamma. Daga nan ne kuma da yamma aka tafi yin walima a otal din 'Ni'ima Guest House' da ke kan titin 'Sulaiman Cresent'.

Daruruwan jama'a da suka kunshi 'yan fim da kuma masoyan Abida sun yi da-na-sanin zuwan da suka yi otal din domin halartar walimar auren. Tun safe an raba katin gayyata, aka rubuta cewa za a fara yin taron da karfe 5:00 na yamma. Ya zuwa karfe 5:10 kuwa mutane har sun hallara otal din. Amma saboda matsalar rashin kai kayan kida da wuri, ba a fara gudanar da biki ba sai kusan karfe 8:00 na dare. Su kansu ango da amarya sai kusan wannan lokacin suka je.

Lokacin da aka bude kofar shiga dakin walimar, an umurci wasu sojoji da ke dauke da bindigogi da bulalai su tsaya a kofar, kada su bar kowa ya shiga sai mai kati a hannu. Wata majiya ta sanar da wakilanmu cewa katin gayyata 200 aka raba. Haka aka fara shiga ana nuna kati. Lamarin ya fara kazancewa ne sa'adda masu katin da suka yi dafifi domin shiga suka ga ana ta yin shigar-kutse da 'yan alfarma marasa kati. Su kuma sauran jama'a da ba su da kati sai suka rika matsawa suna nuna sani don kokarin shiga. Ko kafin mai kati ya ankara tuni har sojojin sun fara labta wa masoyan na Abida bulala. Wata mata ta ba jama'a tausayi lokacin da aka rika jibgarta da bulala mai harsuna rututu. Da abin ya yi zafi sai da ta kai ba wanda ba a daka ba, kama daga mai katin shiga har maras katin. Bayan an dauki lokaci mai tsawo kuwa, sai gaba daya aka hana masu kati shiga, aka ce, "Wadanda ke ciki sun isa haka".

Daga cikin fitattun jama'a wadanda suka sha duka har da Jamila Haruna, wadda ta fusata amma daga bisani ta shiga; da Sulaiman Gambo Awaisu, jarumin shirin Alaqa, da kuma jarumi Ahmed S. Nuhu; wani matashi kuma mawaki da aka fi sani da suna 'Mai Dawayya,' ya sha dukan tsiya a kokarinsa na shiga. Tun kafin a zo, matashin dai ya yi ta yin ganganci da babur a bakin ofishin Hamza da ke Sabon Titi don nuna murnar aurensa.

Haka dimbin mutane da suka ci ado suka yi tsaye cirko-cirko a wajen dakin. 'Yanmata wadanda ba 'yan fim ba da suka cabo ado don taya Abida murna wasunsu sun sha jibga. Dalilin gudun bacin rana ne ma ya sa dimbin 'yan fim manya da dama ba su shiga ciki ba. Mujallar Fim ta ga wani darakta ya yi kyauta da nasa katin, ya juya ya koma inda ya fito, yana tsaki. Mudassir Haladu ('Young Producer'), cewa ya yi, "Ga katina a hannu amma ba zan matsa ba don kada a doke ni a buga a mujalla". Wani dan wasa kuma ya ce, "Wallahi nan suka shanya ni wai in jira za su aiko min da kati. Amma ba komai, da ban zo ba ai da ba su wulakanta ni ba!"

Da ma tun kafin a fara shiga sai da wakilan mujallu daga Garkuwa, Nishadi, Annur, Sharhi, Marubuciya da kuma Fim suka wakilta editan Fim, Ashafa Murnai Barkiya, ya gaya wa 'yan kwamitin gudanar da walimar cewa su ba su da katin shiga, sabodahaka a san yadda za a yi da su. Ashafa ya sami furodusan Dawayya, Ahmad Salihu Al-Kanawy, ya yi masa bayani. Al-Kanawy ya shiga ciki ya sami sauran 'yan kwamitin. Can bayan kimanin minti 20 ya dawo ya ce, "Baba Shariff (Sakataren Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano) ya ce a fada maku ango da amarya sun ce ba su bukatar 'yan jarida".

Ashafa ya shaida wa sauran wakilan mujallu cewa shi fa yana da kati, saboda haka zai shiga don kawai a koro shi ya kara tabbatarwa. Bayan an sake shawara kuma sai ya fasa shiga. Sai daga baya daya daga cikin kirjin bikin, Tijjani Paris, furodusan Alqibla, ya zo ya ce zai shigar da su da kadan kadan. Sai ya debi wakilan Annur guda biyu da kuma editan Nishadi, Bala Makosa. A nan aka bar sauran manema labarun, suna tunanin yadda aka hana su su yi aikinsu wanda dokar kasa ta ba su 'yancin su yi, wato su fadi abin da ya kamata jama'a su sani daga al'amarin wani ko wata da jama'ar ke da hakkin jin wani abu da ya shafe shi.

Shin ana jin tsaron inna ne? inji 'ya'yan mayya, shi ya sa aka hana 'yan jarida shiga? Wani dan wasa da ya zo daga Wudil, wanda bai son a bayyana sunansa, ya ce a lurar da ya yi bisa yadda al'amura suka gudana a dakin bikin, an hana masu mujalla shiga ne don kawai wasu mutane su sami damar sheke ayarsu kuma su gwangwaje. Wani wakilin musamman na wannan mujallar ya samu shiga dakin bikin ba tare da an sani ba, kuma ya ga yadda 'yan fim masu fada a ji suka yi rawar ba-zata lokacin da aka yi wata rawar kwamacala. Wani furodusa da ya shirya fim daya tal ya ce shi dai ya san Hamza ba zai ce a hana 'yan jarida shiga ba, kuma Abida ta so ta yi magana da masoyanta ta hanyar mujalla. Da aka tambaye shi to laifin su wanene, sai ya ce ba zai wuce abokan ango da wasu manyan 'yan fim ba da yake su ba su san illar hana dan jarida shiga taron da ake cakude tare da mata ba.

Wakilinmu da ya ga komai a dakin ya lura cewa an fara gudanar da walimar da misalin karfe 8:00 na dare. An fara gabatar da wadanda za su zauna a teburin manyan baki. Baba Shariff ne farko, sai Hadiza Kabara, Fati Mohammed da kuma Maijidda Abdulkadir. Wannan shi ne karo na farko da Fati da Maijidda, wadanda shahararrun 'yan wasa ne da suka yi aure a bara, suka bayyana a bainar jama'a - domin su taya kawarsu farin ciki.

Can sai ango da amarya suka bullo. Hamza yana sanye da shadda ruwan bula, ita kuma Abida ta dauro shudin leshi da dankwali baki mai roko-roko. Suna fitowa sai aka dauki tafi da ihu. Ganinsu sai wadanda aka nada su hana manema labarai daukar labari ko hoto suka shiga aikinsu. A ciki, akwai masu daukar hoto, yawancinsu amintattun mashirya bikin. Wani yaro mai suna Nura Shariff, wanda ke aikin hada hoton bidiyo a 'Iyan-Tama Multimedia,' ya tunkari wani mai daukar hoto mai suna Nasiru, wanda ya zo daga Kaduna, ya ce masa kada ya kuskura ya dauki hoto a wurin domin wai shi ma'aikacin mujallar Fim ne. Da ma tun da rana, Nura din ya hana Nasiru ya dauki amarya da kawayenta hoto a gidan da aka daura auren a kan zargin cewa ma'aikacinmu ne. Duk da magiyar da mai daukar hoton ya yi masa, matashin, wanda yana daga cikin abokan ango, ya kafe a kan lallai bai amince ba. Tilas ta sa Nasiru ya ba wani yaro kyamararsa ya daukar masa hotunan. A gaskiya, Nasiru ba ma'aikacin mujallar Fim ba ne, kuma duk hotunanbikin Abida da muka samu babu guda daya wanda shi Nasiru ya dauka ko ya sa aka dauka aka kawo mana.

Duk da cewa an umurci mutane idan za su yi liki su yi daya-bayan-daya, ai da ango da amarya suka fito suna rawa sai wurin ya hautsine. Da aka natsa, wani furodusa ya mike yana bambadanci, yana tonon silili na cewa 'yan fim ba 'yan iska ba ne, har ya nuna ma'auratan (bayan ya sa sun mike tsaye), yana cewa, "Jama'a yanzu wadannan 'yan iska ne?" Aka ce, "A'a!" Har wani mawakin finafinai, Musbahu M. Ahmad, daga can baya ya ce, "Fanka dai! Fanka dai!" Wasu jama'ar gari kuma suka rika cewa, "Me ya kawo wannan maganar? Mu ba mu gane ba."

Bayan wasu 'yan jawaban, sai aka sake kiran ango da amarya su tashi su kara rausayawa. Ganin haka jama'a suka kara dawowa suna yi masu liki. Mawakan finafinai kamar Sadi Sidi Sharifai, Musbahu M. Ahmad, Mudassir Kasim, Yakubu Muhammad da Abubakar Sani, sun dan wake wurin inda Yakubu ke rera waka sauran na amsawa. Shi ma Musbahu ya rera sauran sun amsa. Bayan sun gama sai aka sake umartar ango da amarya su fito su taka rawa 'yan'uwansu su yi masu liki. Da suka gama sai aka gayyato kowane furodusa mace ko namiji da su fito "su dan cashe". Haka aka rika fito da su Ali Nuhu, Aminu A. Shariff (Momo), Maryam Mashahama, da sauran 'yan wasa, suka taya su cashewa.

Da suka gama suka zauna sai kuma aka kira wasu kamar su Fati Mohammed matar Sani Musa Mai Iska, da shi Sani Mai Iska din, Maijidda Abdulkadir da kuma Abida da Hamza su taya su yanka kek. Suka kuwa yanka, ango ya bai wa amarya a baki, ita ma ta ba shi. Sai amayar ta juya ta ba Fati da Maijidda duk a baki. Daga nan sai su duka ukun suka rungume juna. Ganin haka sai wata mai kallon finafinai ta nisa ta kada baki ta ce, "Wato 'yanmatan cikin Mujadala duk sun yi aure kenan!"

To daga nan ne sai aka fara bayar da kyaututtuka ga amarya. Fati Mohammed, wadda ke rike da tarhon GSM a hannunta, hakorinta na Makka yana ta walkiya a dakin, ita ce ta fara mika tata kyautar, sai wasu 'yan wasa mata su uku, sai darakta Tijjani Ibraheem da ya aiko sakatarensa da tasa kyautar. Da gani, kyautar Fati ce mafi girma, har wasu na zaton ko a Ingila da ta je kwanan baya ne ta yi wa amaryar tsaraba amma ba ta ba ta ba sai a nan wurin walima.

Da ma'auratan suka gama karbar kyaututtuka sai aka sa wata waka da Musbahu M. Ahmad, wanda abokin angon ne, ya yi wa Abida da Hamza. A daidai lokacin da ya fara wakar sai ita ma Abida ta fara bin wakar. Tun ba ta yi nisa ba sai ta barke da kuka, hawayenta suna diga a kan farin gilashin ido wanda ta sanya. A nan Fati, Abida da Hadiza Kabara suka fara lallashinta. A karshe dai sai fitar da ita suka yi.

Kafin nan kuwa an raba kayan lashe-lashe, kalanda da kuma hankici mai dauke da hoton Abida da Hamza wanda wata Hajiya Habiba ta yi a matsayin gudunmuwarta.

Da za a tashi daga taron, sai aka sa sojoji su fara korar jama'a daga filin. A waje ma a harabar otal din 'iyalin gwamna' din sun raraki mutane da bulala har aka fito waje kan kwalta. Ana korar mutane da bulala suna turar motoci. Wani da aka biyo ya girge ya fadi, bayan ya tashi ya fita, wakilin Fim ya tambaye shi abin da zai ce. Sai ya ce, "Me zan ce fa? Cuta ce dai an riga an cuce mu don kuwa an ba ni kati, an raba ni da harkata na zo kuma an hana ni shiga, ga kuma duka na sha". Wani sabon darakta bai shiga ba, cewa ya yi, "Ni don ban shiga ba ai ba wani abu ba ne. Amma ka ga hana 'yan jarida shiga zai kara sawa mutane su rika zargin mu." Ya kara da cwa, "Da idona na ga 'yan jarida a wurin daurin aure, amma da yake wurin party shagali za a yi, sai aka hana su shiga."

Ko shakka babu a wurin bikin an yi rawar tambotsiai. Har akwai wanda mutane ba su yi tunanin zai taka rawar ba, shi ma da aka ce masa "ai babu 'yan jarida a ciki," sai ya zage ya yi ta tsalle-tsalle abinsa.

Abida dai ta tare a gidan su Hamza can a wani gari mai suna Danzaki da ke cikin Karamar Hukumar Gezawa a jihar Kano. Wata majiya ta fada mana cewa da, a Kano Angon ya so su zauna, to amma iyayensa suka ce faufau, sai dai ya kai amaryar tasa can karkara inda suke. Shi kuma ya bi umurninsu. Shi dai Hamza, shi ne Furodusan finafinai uku: Nadama, Ajizi, da Zahiri. Wannan shi ne aurensa na biyu, bayan rabuwarsa da matarsa ta fari, A'ishatu Mohammed, wadda ta rikide ta zama Furodusa ita ma, har ta shirya fim mai suna Tababa.

Wakilanmu sun lura cewa yunkurin da aka yi na hana a sanar da duniya labarin auren Abida ya ci tura. Bayan mujallu, masu kalanda ma sun ci kasuwa da labarin.

Mujallar Fim na yi wa Hamza da Abida fatan alheri, tare da addu'ar Allah ya ba su zaman lafiya da haihuwa, amin.

Kawayen Amarya Sun Ba Wadanda Aka Doka Hakuri!
ZAHARA'U SHATA:

GASKIYA abin da zan ce da 'yan'uwanmu maza da mata Musulmi da kawayen abida, shi ne mun gode madalla. Allah ya saka masu da alhairi kuma Allah ya maida kowa gidansa lafiya. Su masoyan Abida na nesa abin da za mu ce masu, su yi wa Abida addu'a tunda ba su san ranar aurenta ba, ba su sami damar zuwa ba. Su yi mata addu'ar Allah ya zaunar da ita a gidan mijinta kuma Ubangiji Allah ya ba ta zuri'a tagari ita da mijinta.

'Yanmata masoya Abida da suka je wurin biki sojoji suka dake su, to muna ba su hakuri saboda a gaskiya mun yi iya bakin kokarinmu don sojojin nan su bar su su shigo amma abin ya ci tura. Ina ba su hakuri. Don Allah su yi hakuri!

Yau dai ga ranar karshe ta zo. Da masu son Abida da wadanda ba su son Abida, da wadanda ke cewa Hamza ba zai auri Abida ba, yau ga ranar karshe ta zo, Hamza ya aure ta. Masu bakin ciki yaya za su yi? Masu farin ciki kuma sai su taya ta addu'a Allah ya zaunar da ita gidanta lafiya.

UMMI NUHU (ta cikin fim din Al'amari):

GAME da auren Abida ba abin da zan ce sai godiya. Saboda duk abin da muka kudiri niyya Allah ya cika mana mun yi shi yadda muke so. Kuma auren Abida an yi ba-zata saboda ya yi matukar ba da mamaki. Allah ya ba su zaman lafiya. Abida da Hamza su yi hakuri. In dai da so da kauna to hakurin ma yana nan.

Don haka a matsayina na kawar Abida nake ce wa Hamza wannan yarinya ta nuna masa iyakar kauna. Duk abin da take cewa shi ne babu wani sai shi har Allah ya cika mata kudirinta. Ana aure da yawa a Industry; an yi, an sake an yi. Ba wai na ce na Abida ya fi ba, ya zo da wani sabon system. Saboda duk abin da aka tsara aka ce za a yi, cikin yardar Allah an yi shi. Duk wadanda aka gayyata sun zo.

Ka san shi soja bai da laifi. Wani abu ne, ina daga cikin wadanda suka sa su amma ba cewa aka yi su daki mutane ba, saboda 'yan daba da 'yan iskan nan shi ya sa aka aje su sai mutun ya nuna karfi. Amma su wadanda suka zo masu kaunar Abida suka hadu da wannan hadari (duka), ba abin da zan ce masu sai Allah ya ba su hakuri. Allah ya huci zuciyarsu kuma Allah ya sa ba za su yi fushi ba, suna nan kan bakansu na son ta.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin