Daukar shirin DAREN FARKO
Yau da kallo, gobe da labari
Hagu zuwa dama: Alasn Kwalle, Yahaya Skito, Hafizu Bello (a zaune), Al-Amin Ciroma (da tabarau) Ibrahim Sheme, da Musa Alhasan...lokacin daukar shirin Daren Farko
|
Daga SHAFI'U MAGAJI USMAN a Kaduna
A TSAKANIN ranakun Laraba, 15 ga watan Mayu da Laraba, 22 ga watan aka aiwatar da aikin daukar wani sabon fim mai sun Daren Farko. Kamfanin 'Northern Star Films' da ke Kaduna, mallakar mujallar Fim, shi ne ya shirya shi a karkashin shugabancin mawallafi Ibrahim Sheme. Fim din ya kunshin shahararru da sababbin 'yan wasa da suka hada da Hamisu Lamido Iyan-Tama, Maryam Mashahama, Galin Money, Yusuf Barau, A'isha Musa, Ahmed S. Nuhu, Alasan Kwalle, Aisha B. Umar, Sadiya Abdu Rano, Aliyu Abdullahi Gora II, Sani Moda, Hajara Abubakar (Dumbaru), Musa Mohammed Abdullahi, Fatima Ahmed, da Asma'u Mu'azu.
Har ila yau akwai Wasila Isma'il, Rashida Bello, Ashiru Sani Bazanga, Zulai Dalhat (Illah), Shafi'u Magaji Usman, Musa Alhassan (Kalla), Rabi'u Rikadawa (Dila), Mudassir Haladu, Fati Idon Gwal, Nata'ala Aliyu Zariya, Hadiza Ibrahim (Indiyar Daji) da Abdullahi Nasir (Ability).
Nasara ta farko da kamfanin zai yi tinkaho da shi a wannan aiki shi ne tun da aka fara har zuwa ranar da aka kammala shi ba a samu wata hatsaniyar da ta dakatar da daukar shirin ba. Kuma dukkan 'yan wasa da ma'aikatan da suka yi hidima wajen daukar fim din an biya kowa hakkinsa ba tare da je-ka-ka-dawo ba, kamar yadda aka yi yarjejeniya da shi tun farko. Manajan gudanarwar shirin (Production Manager) mai suna Abdurrasheed Mohammed Kankiya, ya kada baki ya ce, "Mun biya kowa hakkinsa a lokacin da ya gama aikinsa ba tare da wani jinkiri ba, kuma na kalubalanci duk wanda yake ganin ba a biya shi ba da ya fito ya yi magana." Wannan nasara ce babba, sabanin yadda ake yi a wasu wurare inda za ka ga an gama daukar fim, wani ma har ya fito kasuwa, ba tare da an biya jama'a hakkinsu ba; ko dai furodusa ya hana ko kuma ya ba wani wakilinsa wanda shi kuma ya yi kememe ya hana.
Ba za a ce ba a samu matsalolin da suka nemi kawo wa daukar shirin tsaiko ba. An samu matsalar cacar-baki da rashin fahimtar juna a tsakanin wasu 'yan wasa a masaukin daukar shirin, wato 'MIA Motel' da ke unguwar Barnawa. Ga dai wurin ya hadu (kuma ba a taba shirya wani fim a cikinsa ba), to amma halartar wasu yaran 'yan wasa wadanda ba a gayyata ba a wurin ya haifar da gardandami ta yadda sai da darakta Hafizu Bello ya shafa wa idonsa yaji ya fatattaki wasu daga cikinsu.
A ranar da za a kammala aikin daukar shirin, da misalin karfe 11:30 na safe, mutane sun yi dafifi a harabar kamfanin shirya finafinai mai suna 'Bazanga Communications,' wanda ya taba shirya fim mai suna Aminan Zamani, da ke Tudun Wada. Mutanen unguwar maza da mata, yara da manya sun zo domin gane wa idonsu 'yan wasa da suke begen gani a zahiri. 'Yan fim sun zo wurin domin daukar wani bangare na shirin (wato gidan Galin Money da matarsa Asma'u Mu'azu a shirin) da kuma wata waka. Abinka da taron jama'a masu yawa, tilas a samu na kirki da kuma bata-gari. Ana cikin aikin sai daya daga cikin'yan wasan da suka fito daga Kano, Mudassir Haladu, wanda kuma shi ne manajan kula da tufafi a shirin, ya fita daga harabar domin sayen sigari. Sai wasu 'yan iska suka far masa da duka bayan sun lura yana da kudi a jikinsa. Sun fidda masa da jini a jikinsa baya ga N1,500 da suka kwace masa. Sakamakon hakan ya nemi ya yamutsa wurin baki daya har aikin ya gagara, amma Allah cikin ikonsa sai aka shawo kan matsalar cikin mintoci kalilan, sannan aka ci gaba da aikin bayan an dauki wasu sababbin matakan tsaro.
Wannan shi ne karo na biyu da mujallar Fim ta shirya fim. Fim dinta na farko, Gagarabadau, ya fito a ran 20 ga Yuli, 2002, kuma ya burge masu kallo saboda ba a taba yin irinsa ba - wato yin fim a cikin mota tana tafiya daga farko har karshe. Shi ma Daren Farko, ya sha bamban da irin finafinan Hausa na wannan zamanin. Yana ba da labarin yadda wani manajan banki (Iyan-Tama) ya kashe kudi tsababa ya auri wata budurwa (Aisha B. Umar) wadda take son wani saurayi (Ahmed S. Nuhu). To amma inda gizo ke sakar shi ne ashe shi manajan, Alhaji Mani, ba ya da lafiyar gaba, don haka tun a "daren farko" bai taba anamarya ba; hasali ma ta share watanni a gidansa "bai ce mata komai ba." Can kuma saurayinta Haidar ya shiga soyayya da yarinyar da ta yi mata babbar kawa (Sadiya Abdu Rano). Yaya kenan? Labarin da fim din ya kunsa a dunkule fadakarwa ce ta wata mummunar al'ada da addini ya yi hani a kanta, ta kyamar auratayya a tsakanin Fulani da mahauta. Shi Ahmed S. Nuhu ya fito ne a matsayin dan Sarkin Fawa (Musa Mohammed Abdullahi) kuma an hana shi auren masoyiyarsa Amani ne wai saboda iyayenta (Yusuf Barau da Aisha Musa) Fulanin zaure ne, wai babu aure a tsakaninsu; nan kuwa an dai rabe da guzuma ne domin a harbi karsana - don kurum an ga Alhaji Mani Manaja ya fi iyayen Haidar kudi. Shirin yana son ya nuna illolin da matsalar ta rashin lafiyar da da namiji yakan samu da kuma musibun da suke biyo bayan zamansa da mace da ya aura ba tare da an san halin da yake ciki ba, da kuma musibun da suke tattare da wannan mummunar al'adar ta hana mahauta aure ba tare da hujja ba.
Wakilanmu da suka kasance a dukkan wurarren da aka dauki shirin sun ruwaito cewa in ban da matakan tsaro masu tsauri da aka dauka wajen hana cincirindon masu son ganawa da wasu 'yan wasa, to da aikin ya faskara a wasu unguwannin garin inda aka dauki shirin. An samu kwararowar wasu sababbin 'yan wasa har ma da wasu kalilan cikin wadanda suka yi fice a duniyar finafinan Hausa wadanda ba a gayyata ba, wanda faruwar haka shi ma ya rika kawo cikas .
Har ila yau wakilan namu sun ji ra'ayoyin wasu cikin 'yan wasa da ma'aikatan da suka gudanar da aikin daukar Daren Farko, musamman kan aikin da kuma ra'ayoyinsu kan shigar mujallar Fim cikin harkar shirya finafinai maimakon ta tsaya kan aikinta na watsa labarai. Maryam Mohammed Danfulani (Mashahama) ta ce, "Labarin wannan fim yana da kyau sosai" kuma shigar mujallar cikin harkar shirya finafinai kyautatawa ce ga harkar fim a kasar Hausa." Dattijo Musa Mohammed Abdullahi kuma ya ce "shigowar mujallar Fim wajen shirya finafinan Hausa ta dace. Dalili shi ne yadda take watsa labaran matsalolin da furodusoshi ke fama da su kafin su shirya fim, a yanzu ita ma za ta gane wa idonta." A cewar Musa Alhassan (Kalla), wanda ya fito da sunan Tukur Sabalikita a wasan kuma kawun amarya, "Ina kira ga furodusoshin finafinai da su kwaikwayi abin da Ibrahim Sheme yake yi wajen rashin nuna bambanci ga ''yan wasa gwanaye da sababbin shiga ko kuma dan gari kaza da na gari kaza."
Fitaccen jarumi Alasan Kwalle shi ma ya tofa albarkacin bakinsa inda yake cewa, "Mun yi wa Allah godiya ya kaddara muna cikin wannan fim mai suna Daren Farko da wannan mujalla mai farin jini ta shirya. Kuma shigar mujallar ga harkokin shirya finafinai tamkar kara fadada harkokinta ga masu sha'awarar su rika shigo da sababin abubuwa komar yadda suka yi a wannan." Asma'u Mu'azu ta ce, "Da ganin yadda ake aikin wannan fim, kai ka san zai yi kyau. Kuma na taya wannan kamfani murna da suka biya dukkan ''yan wasa kudadensu".
Ahmed S. Nuhu, wato jarumi shirin, ya yi ta kyalkyata dariya a yayin da wakilinmu yake tattaunawa da shi. Dalilin faruwar haka kuwa shi ne a daidai lokaci ne furodusan Daren Farko Ibrahim Sheme ya cika ya tumbatsa saboda bata masa rai da su suka yi ana cikin aikin. Ahmed ya kada ya ce, "Zan yi alfahari da zamantowa na fito a matsayin jarumin Daren Farko, kasancewar labarin fim din ya burge ni duk da iya matsalolin da ma fuskanta a lokacin daukar shirin. Kuma shigowar mujallar Fim a harkar shirya fim ya burge ni, don a yanzu ne za su san matsalolin da ake sha wajen shirya fim, ba wai su dinga ba da labaran kawai ba." Ya yi dariya ya kara da cewa, "Yanzu Ibrahim Sheme can an kuna shi ya fusata har yana neman fita hayyacinsa!"
Furodusan shirin Mutum Ko Aljan?, Alhaji Nata'ala Aliyu Zariya, yana daga cikin 'yan wasan da suke fito a wannan fim din. Abin da ya ce shi ne: "Na ji dadin shigowar mujallar Fim cikin film productions. Amma a daukar shirin nan Daren Farko bai kamata a ce an dauki yawan kwanakin da aka dauka wajen daukar shirin ba. In ni ne cikin kwanaki hudu na gama domin yawaita kwanaki shi ya haifar da wasu matsaloli masu dama musamman ga 'yan wasa. Ni din nan ko a finafinai da na shirya ban fuskanci matsalar zirga-zirga kamar yadda na sha a wannan fim ba."
Mai daukar hoton shirin (cameraman), shahararren nan ne Yahaya Skito. Shi ma ya ce wani abu: "Ina yi wa mujallar Fim fatan alheri kan shigowarta harkar shirya fim. Kuma kamar yadda ta daukaka a kan aikinta na watsa labarin fim, haka za ta daukaka wajen shirya finafinai. Kuma 'yan matsalolin da aka fuskanta wajen wannan aiki matsaloli ne da aka saba fuskantar irinsu a kowane irin production."
Wani dan wasan da ake yi ta kwaikwayo da shi har na tsawon mako guda da aka yi ana wannan aiki shi ne Sulaiman Gambo Awaisu (Alaqa). Ya rako abokinsa Ahmed S. Nuhu wajen daukar fim din. Shi ma ya shaida wa wakilinmu cewa, "Ba ni cikin wannan fim amma fim din ya burge ni matuka a lokacin da ake daukarsa. Sha'awata da labarin fim din ya sa na yi sha'awar ina ma ina ciki."
Mun tambayi shugaban shirin, Ibrahim Sheme, ko yaushe ne fim din zai fito? Sai ya ce, "Ka san yanzu don ka gama daukar fim, aikinka bai kare ba. Domin na farko dai za ka koma gida ka yi ajiyar zuciya, ka dan sarara, hankalinka ya dawo jikinka. Daga nan za ka tafi wurin aikin hada hotuna, wato editing. Sai kuma ka garzaya Abuja hukuma ta duba fim din ta ba ka satifiket na amincewa da fitowarsa, gwamnatin Kano ma ta duba ta amince. Sai kuma ka je ka buga kwalin gidan kaset din. Sa'annan sai ka bi layin fito da fim din. To, ka ga duk wadannan abubuwan suna cin kudi da lokaci. Sai a hankali. Amma insha Allahu kwanan nan za mu je mu yi editing na fim din, daga nan mu shiga yin sauran abubuwan da ake bukata har a fito da shi. Amma ina tabbatar wa jama'a cewa ba za a samu dadewar da aka samu wajen shirya fitowar Gagarabadau ba, insha Allah." A kan yadda ya dukufa wajen shirya finafinai, Sheme ya ce, "Sha'awa ce kurum. Na ji ma wasu na cewa babu riba. To, su sun dauki riba a matsayin kudin da ka samu daga fim dinka. Ni ko na dauki riba a matsayin samar da aiki da na yi ga matasa da sauran 'yan fim - domin dai dole ne wani ya ci abinci ta hanyata idan na shirya fim - da fadakarwar da na yi, da kuma nishadantarwar da na yi. Saboda haka dai kamfaninmu ya kudiri ci gaba da shirya finafinai wadanda a hankali a hankali wasu za su lura da cewa sun bambanta da wasu finafinan da suka kalla. Yanzu haka ma muna da wani labari na wani fim din; ba da jimawa ba za ka ji duriyarmu mun sake fita za mu dauki fim din. Mun gaji da ce wa mutane ga irin fim din da muke ganin ya dace a yi. Tunda wa'azin ba zai isa ba, muka ce to bari mu tashi tsaye mu nuna masu ta hanyar aikatawa. Ko da wani zai ce ba mu yi fim kamar na su wane ba, na san za a ce mun dai tabuka. Allah dai ya ba mu sa'a."
To, amin malam.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|