|
'Yan fim za su shirya babban taron kara wa juna sani
Farfesa Abdallah Adamu
|
Daga IRO MAMMAN
a Kano
BISA la'akari da yadda wasu jama'a suke yi wa harkar fim mugun kallo, 'yan fim na Kano suna nan sun fara share fage don gyara fuskarsu ta hanyar shirya wani gagarumin taron kara wa juna sani.
Wannan ya biyo bayan taron da Cibiyar Nazarin Hausa ta Jami'ar Usmanu Danfodiyo ta shirya a Sakkwato a watan Yuli na bana inda manazarta da jama'ar gari suka ragargaji harkar fim suna cewa tana bata tarbiyya.
Wata majiya ta ce taron da ake shirin yi a Kano zai tattaro masana daga jami'o'i da sauran manyan makarantu, da jama'ar gari, da kuma su kansu masu harkar fim din. "Muna ma da nufin gayyato masana daga kasar waje," inji majiyar.
Ya zuwa yanzu har an yi zama guda uku a ofishin 'Moving Image' da ke kan Titin Zoo a Kano, inda a taro na baya-bayan nan, wanda aka yi a ranar Lahadai, 25 ga Agusta, aka zabi masanin adabi din nan Furofesa Abdalla Uba Adamu a matsayin shugaban kwamitin tsare-tsare na taron.
A zaman da aka yi kwanan nan din, 'yan fim da dama (musamman furodusoshi da daraktoci) sun hallara, kuma sun tattauna matsalolin da ke addabar sana'arsu da kuma yadda suke jin taron kara wa juna sanin zai kasance. Mun sami labarin cewa a wurin, Furofesa Abdalla ya nuna bukatarsa ta maida taron ya zama dandalin ilimintar da juna ba na sukar juna ko fashe haushi ko taka rawar muguwar rarrabuwar da ta sha kan harkar fim a Kano ba.
Shi dai Furofesa Abdalla, an nada shi ciyaman ne saboda dacewarsa, sa'annan saboda shi ba memba ba ne na wani gungu a cikin sansanonin siyasar harkar fim. Haka kuma kasancewarsa malamin jami'a da ake girmamawa zai iya ba taron da za a yi karin daraja a gun masana.
Mun ji cewa za a kai cikin farkon badi kafin a yi taron, domin Abdalla da sauran shugabanni suna so a yi tsari mai kyau kafin lokacin. An tsayar da Asabar, 7 ga Satumba, 2002 a matsayin ranar da za a yi zama na gaba inda za a tattauna kan irin jawaban da ake son a yi a taron na kara wa juna sani.
Dillalan kaset za su zabi shugabanni
Daga ASHAFA MURNAI BARKIYA a Kano
'YA'YAN Kungiyar 'yan kasuwa masu sayar da kaset na bidiyo da rikoda na Jihar Kano za su zabi shugabanninsu a ranar Lahadi, 8 ga Satumba, 2002.
Wakilinmu ya gano cewa ko shaka babu za a kara sosai idan aka yi la'akari da jerin sunayen 'yan takarar mukamai, musamman mukamin shugaban kungiyar. Mutum uku ake jin za su kara wajen neman zama shugaba; su ne: Alhaji Idris Danzariya, mai kantin sayar da kaset da shirya fim na 'El-Duniya,' da Alhaji Sama'ila T.M. wanda ke sayar da kaset na rikoda a Kasuwar Kofar Wambai, da kuma Malam Tukur mai saida kaset na rikoda a Kasuwar Kofar Wambai.
Za a yi zaben ne a gidan sinima na Oriya da ke Kofar Wambai, Kano. Tuni dai 'yan takarar mukamai daban-daban suka dinga yin kamfen a wurin 'yan'yan kungiyar, kowane da alkawuran wasu abubuwa da yake ganin sai an yi su kafin kungiyar ta samu ci-gaba. Ita dai wannan kungiya, ta dade tana cikin rikici na shugabanci, ta yadda har ma ta kasu gida-gida, wasu 'ya'yanta na cewa ba su yarda da wasu ba. Kila in an yi wannan zabe a samu sa'ida.
Furodusoshin Gombe sun dinke barakarsu
Daga SANI AHMED SASA
a Gombe
BARAKAR nan da ta addabi Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Gombe, wadda muka ba ku labarinta a watan jiya, ga alama yanzu ta kau, sakamakon zaben sababbin shugabannin wucin-gadi na kungiyar da aka yi kwanan nan.
Furodusoshi 20 ne suka yi zaben yayin da hudu suka ki jefa kuri'arsu, wato suka yi jemage kenan.
Shugabannin su ne: Kasimu A.Y. Musa a matsayin ciyaman; mataimakin shugaba - Umar Dan Sadiq; ma'aji - Umar Ardo, sai jami'in hulda da jama'a - Sa'adu Lawan.
Shugaban, wato Kasimu, haifaffen Gombe ne wanda ya yi makarantun 'Central Primary' da 'Comprehensive Day Secondary' a Gombe. Bayan kammala karatunsa na sakandare sai ya fada harkar kasuwanci yana saida magani, daga baya kuma ya bude kamfanin shirya fim mai suna 'M.D.V. Videos'. Ya fara fitowa a fim a farkon shekarun 1990 da fim mai suna Maci Amana.
Da mujallar Fim ta tambaye shi batun alakarsa da sauran furodusoshin jihar yanzu da yake ya zama shugabansu, sai ya ce, "Tun tuni ina da kyakkayawar alaka da dukkan furodusoshi har ma da shi Sadiq Dan Nana" - wanda suka yi rikici da shi kwanan baya.
Ya dora laifin rikicinsa da Sadiq a kan Sadiq din, har ya ce Sadiq "bai dace ya yi shugabanci ba."
Kasimu ya yi kira ga dukkan 'yan fim na Jihar Gombe da su ba shi hadin kai don ya cimma kudirorinsa.
Da yake kwatanta ci-gaban shirin fim a Gombe da Kano kuwa, sai ya ce, "Muna da hazikan 'yan wasa da yawa. In da a ce muna da abu biyu, da yanzu mun yi nisa: na farko shi ne da masu kudinmu za su sa kudinsu, sannan kuma a ce gwamnati ita ma ta taimaka, da wallahi babu wani abu da 'yan fim na ko'ina za su nuna mana."
Kasimu ya bugi kirji a kan gasar finafinan Hausa ta kasa da ake shirin yi a Kano cikin Disamba, ya ce, "Tunda yanzu an rigaya an zabe ni a matsayin shugaba, to fa lalli ne duniya ta ji tsoron fim din da za mu fitar a wannan gasar. Kuma ina mai shaida ma cewa finafinan Gombe za su yi tasiri sosai, in har furodusoshinmu sun ba da hadin kai sosai."
A karshe ya yi kira ga abokan hamayyarsa kamar haka: "Kiran da zan yi a kan su wadannan 'yan tawayen shi ne su zo mu hada kai don ci-gaban harkar fim a Gombe. Kamar ita Hajiya Bebe Gafa, babu yadda ba mu yi da ita ba amma ta ki ba da hadin kai, ba mu dai san nan gaba ba."
Ita dai wannan kungiyar, an yi mata rijista ta jiha, amma dai satifiket din bai shigo hannu ba tukuna domin Kwamishinar Mata da Matasa ta jihar, wadda ya kamata ta sa hannu a kan satifiket din, ta tafi kasar waje. Duk da haka a ran 15 ga Yuli kungiyar ta samu takardar izini daga ofishin kwamishinar mai lamba MOWAYD/RCA/S/8/1, mai dauke da sa hannun Lawenji M. Laison, inda aka gaya wa kungiyar cewa ta ci gaba da aiwatar da harkokinta bisa doka da oda kafin a gama yin binciken tsaro a kanta.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|