Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Ra'ayi Ba Gaba Bane
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Yadda nake waka da muryar Ibro

Sadi Sidi Sharifai

Sharifai
Sadi Sidi Sharifai
Daga IRO MAMMAN da SANI MOHAMMED MAIKATANGA a Kano

SADI Sidi Sharifai yana daga cikin fasihan mawakan finafinan Hausa. Sunansa ya kasance ruwan-dare-game-duniya. In dai za a lissafa mawaka biyu ko uku, to Sadi, wanda akan kira da sunan Sharu, yana cikinsu.

Wani abu da ya bambanta Sadi da sauran mawaka, kamar yadda muka taba gaya maku can a watannin baya lokacin da muka yi hira da shi a kan rayuwarsa, shi ne yadda yake iya sarrafa muryarsa ya yi waka da ita: yakan iya yin muryar karamin yaro, ko muryar mace (kamar yadda ya yi a wakar fim din A'isha 1), ko kuma ya yi da karin muryar wani jinsi, misali Indiya (dubi wakarsa ta fim din Alaqa, da wakokin fim din Ibro Dan Indiya wanda bai fito ba).

A cikin hikimarsa ta sauya murya, a halin yanzu, Sadi yakan kwaikwayi muryar Rabilu Musa Danlasan (Ibro) ta yadda sai mutum ya rantse da Allah a kan cewa lallai Ibro ne yake yin wakar da kansa, ba wani ba ne ya yi a situdiyo shi kuma ya hau a fim. Ya fara yin hakan ne daga fim din Kallo Ya Koma Sama na fitaccen darakta Bala Anas Babinlata. To amma wakokin da ya yi a shirin Ibro Awilo su ne suka fi yin fice a wannan fanni. Su ne ma suka sa aka yi ta sayen kaset din rikoda na fim din ta yadda in ban da wakokin fim din Sangaya, babu kaset din wakoki da ya yi cinikin na Ibro Awilo. Hasali ma dai Ibro Awilo ne ya haifar da wani tsere da ake ciki yanzu na yin finafinan Ibro inda Ibro yake kwaikwayon wani shahararren mawaki. Sun ko hada da Ibro Bob Marley, Ibro Shata, Ibro Dan Indiya, Ibro Craig David, Ibro Chaka-Chaka, da sauransu. Kuma duk muryoyin da ke cikin wakokin wadannan finafinan, Sadi Sidi Sharifai ne ke yin su. Shi ke rubuta waka kuma y aba ta kari sa'annan ya rera ta tare da amshin abokan aikinsa. A wannan fanni dai, kamar yadda yake fadi a Ibro Awilo, "Afirka Afirka, Har kasar waje, Can ma na shiga, ... Na yi zarra!" Kuma ya yi tambaya a kan wakar, yana cewa, "Ko akwai kamarta? Babu kamarta!"

Saboda gwanintar Sadi a wannan fanni na yi wa Ibro wakokin da zai bi a fim, ya kasance mutane da dama sun dauka Ibro din ne ke yin abinsa. Wasu ma har gardama sukan yi a kan cewa Ibro ne ke yin wakokin. Ba shakka, Sadi ya taimaka gaya wajen kara wa Ibro farin jini a gun masu kallon fim.

A gaskiya, Sharu ya ciri tuta a wannan fage ta yadda har ya zama zakara.

To, amma kada a yi tuya a manta da albasa. Ban da waka akwai kida. Duk wakokin Ibro, shahararren makadin nan Alee Baba Yakasai ne yake buga masu kida a situdiyon 'Iyan-Tama Multimedia,' cikinsu har da Ibro Awilo da Ibro Dan Indiya. Shi ma tilas a yabe shi.

Shin yaya Sharu yake yin wadannan wakokin? Mun sadu da shi a wurin aikinsa, wato situdiyon 'Iyan-Tama,' kuma ya amsa tambayoyin da muka yi masa, ciki har da batun soyayyar da ke tsakaninsa da fitacciyar zabiyar finafinai din nan Jamila A. Sadi. Bismilla:

FIM: Ya aka yi har kake sarrafa muryarka kana waka da muryar karamin yaro ko mace ko wani dan wasa da aka sani?

SADI: E to, alhamdu lillahi. Kafin in ce komai bari in yi salatin Annabi: Allahumma salli ala sayyida Muhammadu wasallam. Allah ya kara wa Annabi daraja, amin!

Wannan abu Allah ne ya ba ni, kuma dalilinsa soyayya ga Annabi. Na sami wannan abu ne ta bangaren Ubangijina; mahaliccina ya ba ni baiwa ce.

Yaushe ne ka fara kwaikwayon muryar Ibro kuma a wane fim ne?

SADI: Da ma ina son wannan tambayar. Akwai wani fim din Bala Anas da muka yi wanda shi ne muka fara muryar Ibro, wato fim din Kallo Ya Koma Sama. Daga shi kuma na fara yi wa Ibro waka har kawo ga yau.

Wane nazari ka yi wa Ibro har kake kwaikwayon muryarsa?

SADI: Ni wallahi ba wani nazari da na yi masa, illa kawai ina kallon finafinansa, sai na ji muryarsa ta yi min in yi waka da ita.

Furodusoshi ne suka takura maka ka rika kwaikwayon muryar Ibro?

SADI: Ba furodusoshi ba ne ba, amma za a iya cewa su ne. To amma kuma sila Allah ya daukaka Ibro kuma Allah ya kawo wannan yanayi na waka. Kuma mutane suka yaba da yadda yake yi.

Wace matsala kake fuskanta wajen kwaikwayon muryar Ibro?

SADI: Gaskiya muryar Ibro tana ta masifar matsala, wanda dole idan ba wanda ya yi haddar wasu maganganu da wasu abubuwa da Ibro yake yi a fim ba ko a wakoki to gaskiya abin da wahala. Kuma ba za ta taba daukaka ba kuma ba ba za a ce shi ne ba. Amma kuma ka ga yadda nake yi ina kwaikwayon wasu abubuwa nashi da dama sai ake ganin shi ne yake yi, in ka ce wa wasu ma ba Ibro ba ne sai ku yi rigima a kan haka.

Muna so ka gaya mana yadda aka yi har ka yi wakokin shirin Ibro Awilo da muryar Ibro.

SADI: E, Ibro Awilo, akwai wata waka da aka fara yi ita ce za ta fito a kashi na 2 amma ita ce audio (kaset na rikoda) wakar farko. To sai daga baya kuma na ba su shawarar a saka ta a na 2, sai kuma shawarar ta karbu, sai suka kawo na sake rubuta masu, na rera masu ita.

Da gaske ne mai fim din Ibro Awilo ya yi maka karin kudi ko kuma wata kyautar musamman saboda cinikin da ya yi a fim din Ibro Awilo?

SADI: Gaskiya abin da Abdullahi mai fim din Ibro Awilo ya yi min, babu wanda ya taba yin shi; in ma za a kamanta, sai dai a ce Hamisu Iyan-Tama gaskiya.

Me za ka ce wa mutane da suke cewa ainihin Ibro da kansa ne yake rera wakokinsa?

SADI: Abin da zan ce masu shi ne wanda suka san Ibro ne yake rera wakarsa su tafi a haka, wadanda kuma suka san akwai wanda yake rera wa Ibro waka su ma su tafi a haka kawai, saboda raba rigima, sai ka ce wa mutum Ibro ne yake yin wakokinsa ku zo kuna rigima ko kuma ka ce ba shi ba ne ku zo kuna rigima.

Shin da gaske ne kana cajin kudin wakar Ibro fiye da sauran wakokin?

SADI: Haka ne, saboda gaskiya tana da wahala kuma gurin fitar da kidanta ma ana samun matsaloli da dama. Shi ya sa ake cajin daban.

Kana jin a mawaka akwai wanda zai iya yin wakar da ba za ka iya yi ba?

SADI: Wannan kuma Allah ne ya bar wa kansa sani. Ni ma kaina na sani, saboda haka ni ba zan iya cewa wani ba zai iya abin da ba zan yi ba, ko kuma zan iya abin da wani zai iya.

Me ake ciki a kan batun aurenka da abokiyar aikinka Jamila A. Sadi?

SADI: Wannan abu da Allah ya bar wa kansa sani, amma Jamila tana sona iya sona, ni ma kuma ina sonta. Abin da ya sa Jamila ta zo ta same ni an sa mana rana da wata 'yar'uwarta. To shi ne dalili. Kuma saura wata biyu; za a yi (auren) ne kafin azumi.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin