Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 35   Nuwamba 2002
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
TALLA
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Duniyar Finafinai
Rahoto
Malam Zurke
Rayuwarmu
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Ana so 'yan fim su yi aiki da hukunce-hukuncen Musulunci Daga MUHAMMAD NASIR a Kano

A WANI kwarya-kwaryan taro na wuni daya da aka gudanar don isar da sako da kuma jawo kan wasu fannonin fadakarwa da Musulmi ke da su, an bukaci masu shirin fim da su karkatar da akalar fadakarwarsu daga tsayawa kan batun aure da soyayya zuwa neman ilimin addini da na zamani, kishin kai da kuma kawo karshen matsalar cin amana musamman a cikin Hausawa Musulmi.

Takardar da aka gabatar a taron tana da take kamar haka: "Musuluntar da Fannonin Ilimi: Sako Ga Marubuta, 'Yan Jarida da 'Yan Wasan Kwaikwayo," Malam Sa'idu Suleiman, shugaban Sashen Ilimin Tsimi da Tanadi na babbar Kwalejin Ilmi mai zurfi ta Jihar Kano, shi ne ya gabatar da itar. Wata cibiya ta duniya mai suna International Institute of Islamic Thought da ke reshe a Nijeriya kuma mazauninta na Jami'ar Bayero, Kano, ce ta shirya taron.

A ci gaba da jawabinsa, Malam Sa'idu ya nuna cewa 'yan wasan kwaikwayo sun fi saurin isar da sako ga jama'a masu dimbin yawa. Ya kuma yi tuni da hani da yada karairayi ga jama'a, inda ya jawo ayoyi daga cikin Alkur'ani mai girma wadanda suka yi hani da yada karya.

Saboda muhimmanci da tasiri wasan kwaikwayo ne har malamin ya kira su da cewa "suna cikin malamai domin suna koyar da darussa kuma ana kwaikwayonsu kamar yadda ake kwaikwayon halayen jama'a."

Da yake taron ba kan 'yan fim ne kadai aka yi shi ba, an kuma gayyaci marubuta da 'yan jaridu. Shi ne ya sa ma takardar taro da aka karanta mai shafuka 10 duk kusan sako daya ta isar ga masu shirya fim, marubuta da 'yan jarida.

An sami Abdulkareem Mohammed da Ibrahim Mandawari da Adamu Mohammed (Kwabon Masoyi) daga cikin masu shirya finafinai da suka halarci taron. Mandawari shi ne bako na farko da ya fara isa wurin taron.

A bangaren marubuta kuwa, akwai jigajigan Kungiyar Marubuta (ANA) ta Jihar Kano da suka hada da Dokta Yusuf Muhammad Adamu, Ado Ahmed Gidan Dabino wanda marubuci ne furodusa ne kuma dan jarida. Akwai kuma Lubabatu Ya'u Bichi, Alkhamees D. Bature Makwarari da wasu da yawa.

Malam Ibrahim Sheme, mawallafin mujallar Fim, da Ashafa Murnai Barkiya suna daga cikin 'yan jaridar da suka halarta. Haka shi ma Magaji Shitu Daneji, mawallafin Marubuciya da editan mujallar, da malam Kabiru Yusuf na mujallar Wakiliya duk sun halarta.

Ita dai wannan cibiya (IIIT) an kafa ta ne shekaru 20 da suka gabata sakamakon wani taro da wasu Musulmi su 314 da suka fito daga kasashe 77 suka yi a Saudi Arebiya. Wadannan manyan malamai na duniya sun tattauna al'amura da dama daga ciki har da dalilan da ke sanyawa kasashen Musulmai ke zama koma-baya. Daya daga cikin dalilan da ne suka gano shi ne koma-baya ta fuskar ilmi.

Don haka ne kamar yadda Malam Sa'idu Suleiman ya bayyana sai aka yanke shawarar kafa wata cibiya wadda za ta tattaro kan Musulmi a tafiyar da sha'anin ilimi yadda zai tafi da sigar Musuluci. Wannan ne ya sa cibiyar ta yi nazarin gano wadanda suka fi kusa ga jama'a su ne 'yan wasan fim da kuma marubuta.

Shi kuwa babban bako kuma shugaban cibiyar na kasa, Dakta Bashir Shehu Galadanci, ya nuna jin dadinsa ganin yadda aka yi nasarar gabatar da takardar jawabi. A cikin takaitaccen jawabin da ya yi, Dakta Galadanci ya bayyana cewa babban ofishin kungiyar na duniya yana kasar Amerika.

Wannan cibiya kuma ba ta da wata alaka da wata gwamnati ko kungiya. Mafi yawan masu ba da taimako don gudanar da ayyukanta su ne wasu Musulmin kasar Amerika don kawai kishin da suke da shi na kokarin rage gibin nisan da aka yi wa Musulmi ta fannonin ilimi, inji Galadanci.

A nasa jawabin, shugaban taron, Alhaji Abdulkareem Mohammed, wanda shi ne mawallafin mujallar Duniyar Fim, ya roki masu harkar fina-finan Hausa da su shiga su taimaka don ganin wannan alkibla da aka fuskanta ta sami nasara.

Bayan mai jawabi ya gama, jama'a da dama sun yi tambayoyi da kuma bada shawara ga ita wannan cibiya. Abdulkareem da Mandawari sun yi nuni da cewa malamai daga nesa suke kallon harkar fim, ba su bincike sai dai saurin kawo suka. Wannan ne ya sa Abdulkareem ya nemi malamai su rika kawo suka mai ma'ana.

Kafin a sa Mandawari ya rufe taro da addu'a sai da Galadanci ya gode wa jama'ar da suka halarci wurin. An kuma raba wani littafi mai suna Islamization of Knowledge wanda Malam Sa'idu Suleiman ya rubuta da kuma wata mujalla mai sun Al-Irshad duk kyauta.

Abin da ya fi daukar hankalin mutane da dama a wurin taron dai shi ne taken ita takardar da aka gabatar, wato "Musulntar da fannonin ilimi," har wasu na cewa ba a yi wa takardar taken da ya dace ba. Kamar yadda wani ya yi korafi, "Idan an ce a musuluntar da abu, to ashe da ma can ba Musulmin ba ne. Wannan babban kuskure ne."

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin