Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 39   Maris 2003
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Gasar Finafinai:
Aminu Shariff ya kalubalanci Mandawari kan rabon fom na shiga

Daga WAKILINMU a Kano

WATA takaddama ta barke tsakanin wani fitaccen darakta kuma furodusa da shugaban Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Mohammed Mandawari. Furodusan, Malam Aminu Shariff Hassan, ya fito ne karara ya bayyana rashin gamsuwa kan yadda aka raba fom fom na shiga wata gasar finafinan Hausa.

Ita dai wannan gasa, mai suna 'Fimfair Award', wani kamfani ne yake kokarin shirya ta. Kamfanin ya nada wakilai a garuruwan Kano, Kaduna da Jos wadanda a gunsu ne mai son shiga gasar zai iya karbar fom. To, shi Mandawari shi ne aka wakilta a Kano.

Binciken da wannan mujallar ta yi ya nuna cewa mandawari ya raba fom fom din ga mutane da dama, to amma kuma akwai korafin da wasu suka rika yi cewa yana ba da fom din ne ga wasu zababbun 'yan fim kurum wadanda yake so.

Mujallar Fim ta ji cewa cikin wadanda ke kukan sun je gun Mandawari don karbar fom an hana su har da Isa Ja. Wasu sna tunanin cewa tunda abin nan na Arewa ne gaba daya, me ya sa ba a dora wa Kungiyar Furodusoshi ta Arewa nauyi raba fom din ba.

Aminu Shariff, wanda shi ne shugaban 'Ummi Production,' ya daura damarar yaki a madadin masu irin wannan korafin, inda yake nuna cewa ko kadan Mandawari bai yi adalci a wurin raba fom din ba. A karo na farko, furodusa ya tafi jaridu da mujallun Turanci don yin kamfen a kan al'amarin. Ya yi haka ne ta hanyar rubuta takardar kuka wadda ya raba ga masu shirya gasar, wato kamfanonin MTN, Lever Brothers, da bankin Intercity. Ya kuma raba ta a wurare daban-daban, ciki har da ofishin Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Kano da kuma 'yan jarida.

A takardarsa, Aminu ya nuna wa wadanda suka dauki nauyin bayar da kyaututtukan cewa "jama'ar da suka dora wa nauyin raba fom a Kano sun raba abin ne bisa son ransu, ba bisa ka'ida ba." Ya ce mafi yawan fitattun furodusoshi, daraktoci da 'yan wasa duk ba su samu fom din ba duk kuwa da namijin kokarin da suka yi na neman a ba su.

Daraktan ya yi kuka da mandawari kuma ya yi roko ga wadanda za su shirya gasar da cewa a sake sabon lale na raba fom din.

A nasa bangaren, Mandawari ya yi wa Aminu martani a wata takarda ta ya aiko wa mujallar Fim, inda ya nuna cewa sam ba shi da wata masaniya kan shirya bikin bada kyaututuukan a Kano kamar yadda Aminu ya dauka. Ya roki Aminu da ya yi cikakken bayani gamsasshe "don mu sami damar daukar wani mataki kan abin da wuri." Takardar, wadda aka rubuta a ran 25 ga Janairu, ta nuna cewa shi ma Mandawari ya aika da ita wuraren da Aminun ya aka da tasa.

A karin bayanin da Aminu Shariff ya yi wa wakilinmu, ya ce ya je ofishin Mandawari da ke El-Duniya don a ba shi fom na shiga gasar, amma aka hana shi.

Ganin martanin da Mandawari ya yi masa, ya sake daukar alkalami da takarda ya yi wani sabon rubutu ya sa hannu a ranar 7 ga Fabrairu, inda ya nuna wa shugaban furodusoshin cewa bai dace ya maido amsa ba tunda ba shi aka rubuta wa wasikar farkon ba. "Kai aiko maka da kwafe kawai aka yi" - wato cc, irin abin nan da ake ce wa ka-san-na-sani.

Aminu ya yi wa Mandawari dalla-dallar koken da yake yi a kansa, kamar haka:

* gasar finafinai na na tafe za a yi ta a nan Arewa, wadda wasu manyan kamfanoni za su dauki nauyi, kuma kai ne jami'in shirye-shirye; to gaskiya ne ko karya? * Ko ma da wace fuska kake son ka fake dai kai ne ka raba fom fom din; to gaskiya ne ko karya?

* ka raba fom fom din ga wasu furodusoshi, daraktoci da kuma 'yan wasa; a gefe daya kuma kana sane kiri-da-muzu ka ki ka bai wa wasu don wani dalili naka. To gaskiya ne ko karya?

Maganganun da Aminu ya jefa kan Mandawari sun kai har guda shida. A cikin sauran bayanan ne yake nuna wa Mandawari cewa yanzu fa lokaci ne na dimokuradiyya, don haka ya dace ya gina hanyar biya wa jama'a bukatunsu, musamman ta bangaren raba fom na shiga gasa. Ya kuma tunatar da shi cewa ya tuna shi fa shugaba ne da aka dora wa hakkin jama'a.

A karshe ya nuna cea abin da Mandawari ya yi ya saba da abin da ake tunanin mutum mai matsayi, ilimi da kuma wayewa irin tasa zai yi ba. Ya ce ya kamata Mandawari ya rika girmama bukatun da ke cikin zukatan jama'a, musamman a wannan hali na wayewar zamani da duniya ke ciki.

Har lokacin rubuta wannan RAHOTO ba a sami martanin Mandawari ga wannan sabon raddi na Aminu Shariff ba.

Finafinan da Aminu Shariff Hassan ya shirya sun hada da Saki Reshe 1&2, Reshe Ya Juye Da Mujiya, Wake Daya, Sarkakiya, Gumurzu, Hakki Alwashi, Kada Mage, Raina fansa, Balli, da sauransu.

Wannan shi ne kusan karo na farko da 'ya'yan Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Kano suka kalubalanci shugabanninsu kan wani al'amari da bai kwanta masu a rai ba.

A Kaduna ma, wanda aka ba fom din ya raba, furodusa Yakubu Lere, ya yi bakam, ba a san abin da yake ciki ba. Yawancin 'yan fim na jihar sun ce sam ba su ma san wai akwai fom a wurin Lere makamancin wannan ba.

Ita dai wannan gasa, idan har ta tabbata, 'yan fim za su kwashi garabasar kyaututuuka da suka hada da mota, kyamara, talbijin,tarhon GSM, tikitin jirgin sama na zuwa Afrika ta Kudu, kwana otal din Sheraton da ke Abuja, da makudan kudade. An shirya za a yi takarar mukamai har 34 da za a ci kyaututtuka a kansu.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin