Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 39   Maris 2003
BABBAN LABARI


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Finafinaina 12 da na fi so

A CIKIN 'yan shekarun da ake ta harkar fim, an yi 'yan wasa da yawa da suka zo suka wuce. Wasu sun samu cin nasara, yayin da wasu suka kasa fuskantar kalubalen da ke gabansu. SANI DANJA, daya daga cikin fitattun 'yan wasan kwaikwayo na wannan zamanin, ya yi mana bayani a kan manyan finafinansa guda goma sha biyu, wadanda yake ganin sun taimaka masa gaya wajen samun daukakar da yake da ita a fagen shirin fim. Kamar yadda fitaccen dan wasan wanda kuma darakta ne kuma mawaki ya yi bayani a wata tattaunawa da aka yi da shi.

Sani da shahararren mawakin finafinai Yakubu Muhammad ne suke mallakar kamfanin 'Two Effects Empire,' daya daga cikin manyan kamfanonin shirya fim a Kano. Ga bayanan nasa.

1. JAHEED:

Abin da ya sa na fara fadar fim din Jaheed shi ne saboda fim ne wanda akwai wa'azi a cikinsa, akwai fadakarwa. Kuma fim din ya kara min sanayya da jama'a da yawa. Ni ne darakta kuma ni ne furodusa.

2. MADUBI:

Fim din Madubi Yakubu ne furodusa, ni ne darakta. Abin da ya sa na ke sonsa shi ne domin yana daya daga cikin finafinan da suka fito da ni, wanda har yau har gobe wasu ma idan za su yi kwatancena, da "Sani na Madubi" suke yi.

3. AYAAH:

Shirin Ayaah shi ne labari na farko da na rubuta kuma a dalilin labarin ne har na ga ni ma ya da ce in yi acting, sai na yi.

4. HALIN KISHIYA:

Wannan fim yana daga daga cikin finafinai da mutane suka fara gane cewa ni cikakken akto ne.

5. MACIJIYA:

Shi ma Macijiya zan iya cewa jama'a sun yi amfani da shi wajen auna rawata, bajintata da kuma iya wasana.

6. TANGARAN:

Tangaran fim ne da ya kunshi mutane da yawa. Ni da Yakubu muka rubuta labarin. Labarai ne kamar guda goma, sai muka sunkake shi ya koma daya. Har yau, har gobe muna samun yabo saboda Tangarau.

7. MANAKISA: Gaskiya ina son fim din Manakisa saboda shi ne fim din da na fara taka rawa sosai a cikinsa.

8. KWARYA TA BI KWARYA:

Wannan kuma shi ne fim wanda na fara gwagwarmaya da 'yan wasa a wurin shirya shi. Na sami matsaloli a wurin daukar shirin.

9. NAZEER:

Ba zan taba mantawa da wannan fim mai suna Nazeer ba. A garin Jos muka je aka shirya shi. Dallili son da nake wa fim din kuwa shin ne gari ne gaba dayansa muke musuluntarwa.

10. TSUMAGIYA:

Bin karbuwar da fim din son fim din saboda duk gidan sinima din da aka nuna shi, sai an sake maimaitawa.

11. KASKA:

Ina son fim din Kaska. Shi ne labarin da na shirya na yi darakta amma ban fito sosai a ciki ba.

12. JANKUNNE:

Fim din Jan Kunne duk daga baya na yi shi bayan ma na yi sauran da na lissafa a baya. Amma fa jama'a su sani cewa gaba dai gaba dai yake a jerin finafinan da na fi so. Yau zan bayyana abin da ban taba fada a jarida ba: Jan Kunne shi ne fim din da ya jawo min arziki kowane iri; arziki ta hanyar fim da daukaka a duniya ba ma a duniyar finafinan Hausa kadai ba. An kai Jan Kunne hukumar kasar Amerika sun kalla. An sa Jan Kunne a gidan talbijin na kasa NTA har sau uku an kalla a kasar nan. Sa'annan wani abin alfahari kuma dalilinsa wani wakilin jaridar The Wall Strreet Journal ta Amerika ya zo nan Kano musamman don ya yi hira da ni da Yakubu. Kuma muka yi hirar aka buga a jaridar ta ranar 20 ga Disamba, 2002.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin