Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 28   Afrilu 2002


BABBAN SHAFI
Mu Leka Mu Gani
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 1
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 2
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 3
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 4
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 5
Balaraba Muhammad (1983-2002) na 6
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Hajjin Bana
Sauran Labarai
Ra'ayi Ba Gaba ne
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN

 
If you had a new browser, you would be able to view this java applet. Akwai:  


Balaraba a cikin mujallun Hausa

A IYA tsawon rayuwarta, Balaraba Mohammed, kamar sauran 'yan wasa wadanda suka fahimci amfanin isar da sako ta hanyoyi na zaman, ta yi kyakkyawar hulda da manema labarai, musamman ma mujallun da ke ba da labaran harkar fim. Tana haba-haba da 'yan jarida, kuma ba ta taba bata rai kan wani labari da aka buga a kanta ba. Su kuma 'yan jaridar, sun nuna fahimta da kauna ga wannan yarinya mai fasali wadda kyakkyawar fuskarta riba ce ga mujallun da suka buga hotunanta.

A kidayar da muka yi, mujallu uku ne suka taba buga hoton Balaraba a bangonsu. Su ne: Nishadi, Fim, da Garkuwa. Kuma gaba daya sau takwas ne hotunan nata suka fito a bangon mujallun. A cewar Babban Editan mujallar Fim, Malam Ibrahim Sheme, "Buga labaranta a mujallu ya taimaka mata wajen yin fice da kuma samun karbuwa a wurin jama'a."

Mujallar da ta fara fito da Balaraba dai ita ce Nishadi. Ita marigayiyar, tana da kyakkyawar hulda da editan mujallar, Malam Bala Makosa Zariya. Hasali ma dai Bala din ne ya saka ta a harkar fim, lokacin da ya dauko ta daga Kaduna ya kai ta Kano har ta fito a wani fim mai suna Maryam, wanda Alhaji Danzariya, dan'uwan shi Bala, ya shirya. Nishadi fitowa ta 4, wadda ta fito a cikin Janairu 2001, ta buga hoton Balaraba a bangonta, kuma wannan ne karo na farko da aka ba da labarinta a mujalla. Taken labarinta a bangon shi ne, "Ba Na Zo Korar Wata Ba Ce, Inji Balaraba Moh'd." A daidai wannan lokacin, tauraruwar Balaraba ta soma haske, har ana ganin in su Fati Mohammed da Maijidda da Abida ba su yi da gaske ba, to fa Balaraba za ta "kore" su. Har akwai wata sara a lokacin, wato "A-Kori-Wance." A cikin hirar da Nishadi ta buga, Balaraba ta bayyana yadda ta fara shiga fagen fim, ta kuma yi bayani kan tsohon zancen nan na cewa 'yar wasa wance budurwar wane ce.

Babu mujallar da ta ci gaba da fito da Balaraba kamar Fim. Wata rana a cikin watan Afrilu 2001 ne wani wakilin Fim din, Kallamu Shu'aibu, ya sami mawallafin mujallar, Ibrahim Sheme, ya ce masa, "Ibrahim, akwai wata kyakkyawar yarinya da ta shigo Industry, wadda nake ganin lallai za a dama da ita. Ka san ''yan fim maza da sun ga kyakkyawar yarinya sun dinga rububinta kenan." Ibrahim ya tambaye shi sunanta. Kallamu ya ce, "Balaraba Mohammed."

Ibrahim ya ga hirar da Nishadi suka buga kimanin wata hudu da suka gabata, kuma hirar ba ta burge shi ba saboda guntuwa ce; sa'annan ya yi zaton an buga hirar ne don kurum a taimaka wa Balaraba furodusoshi su san ta, wato a tallata ta. Duk da haka, da yake Kallamu yana da hangen nesa a kan 'yan wasa masu alamar yin farin jini, sai Ibrahim ya ce masa, "Je ka yo mana hira da ita mu gani."

Kallamu ya je ya yiwo hirar ya kawo tare da hotunan yarinyar. Ibrahim ya yi tunanin ya buga ta a matsayin yarinyar bangon mujallar, to amma sai ya yi la'akari da abubuwa uku. Na farko, a daidai lokacin rade-radin auren Fati da Sani Mai Iska ta yi kamari, don haka ya dace Fim ta waiwayi su Fati a kan maganar. Na biyu, wasu 'yan Kaduna suna damun Ibrahim a kan cewa mujallar ba ta fito da 'yan garinsu sosai kamar yadda take fito da 'yan Kano. Har ya je ya yi hira da jaruma A'isha Ibrahim (Saliha) da nufin sanya ta yarinyar bangon mujallar ta watan Afrilu, ga shi bai buga hirar ba saboda an yi rikicin Wasila (sawun giwa ya take na rakumi). Abu na uku shi ne, har ya zuwa lokacin babu mai kallon da ya san wata yarinya wai ita Balaraba domin babu fim din ta ko daya da ya fito.

Duk da haka, Ibrahim Sheme ya ce me zai hana ya "jefi tsuntsu uku da dutse daya"? Saboda haka sai ya ce a buga labarin Fati za ta auri Sani, da na hirar A'isha, da kuma na Balaraba din, duk a bangon Fim ta wata mai zuwa, wato Mayu. Haka kuwa aka yi. Da yake Fim ta zarce kowace mujalla wajen yawan kwafen da ake bugawa da shiga sako-sako na Nijeriya, za a iya cewa wannan labarin ne ya fi kowane fara gabatar da Balaraba ga masu kallo. Kanun labarin a bangon mujallar shi ne, "Balaraba Ta Fara Rage Tashen Wasu." A ciki kuma aka rubuta, "Balaraba Ta Shigo Da Kafar Dama." (Akwai hirar a cikin wannan mujallar, duba ka gani).

A watan na Agusta mujallar Garkuwa ta fara sa Balaraba a bangonta, amma ba ita kadai ba, an sannya ta ne tare da Fati, Hadiza Kabara, Aina'u, da Abida. Sun yi labari mai taken "Bankwana Da Fati: Wa Za Ta Gaje Ta?" A labarin, an nuna cewa yanayin jikin Balaraba ba zai ba ta sukunin maye gurbin Fati ba, duk da yake ta fito a matsayin budurwa a cikin Maryam, Furuci, da Zainab. Mujallar ta ce, "Karshe dai Balaraba za ta kare tamkar irin su Hindatu Bashir da Hauwa Ali Dodo…"

A Nishadi da ta fito cikin Oktoba 2001, an sake sa hoton Balaraba a bango, tare da kanun labari kamar haka: "Auren Balaraba, Abida, Da Wasila Ya Kusa?" An yi hira da Balaraba a mujallar, inda ta tabbatar da cewa suna soyayya da wani dan wasa, amma dai ba a fadi kowane ne ba. "Lokacin da wakilin namu ya nemi sanin wanda Balarabar za su yi aure tare, sai ta ki ta bayyana sunansa," inji mujallar. Wannan dai shi ne karo na farko da wata mujalla ta ruwaito cewa Balaraba za ta yi aure, koda yake mutane dama, ciki har da wakilan mujallar Fim, sun zaci cewa wani dan wasa ne daban, ba Kumurci ba. Soyayyar Balaraba da Kumurci daga baya ta bullo. Bala Makosa, dan jaridar da ya fi kusaci da marigayiyar, ya fadi a cikin mujallar ta Nishadi cewa "babban abin da ke daure masa kai shi ne yadda dan wasan da ke barazanar auren Balarabar, kuma ya yi alkawarin auren wata yarinya a garin Kaduna, yanzu kuma ya yi alkawarin auren Balaraba. Ya ci gaba da fatan Allah ya sa ba yaudara ba ne."

Ita mujallar Fim, ba ta bi sawun wannan shaci-fadin ba kan auren Balaraba. Labarin da ta tsinta bayan wannan shi ne wanda Balaraba ta fito a bangon mujallar a dalilin rikicin nan da aka yi inda wasu mutane suka zo daga Katsina suka ce wai Balaraba 'yar su ce da ta bace tana karama, sai yanzu suka gano ta. Labarin ya fito a bangon Fim ta watan Agusta 2001 inda Fim ta sa kanunsa kamar haka: "Su Waye Iyayen Balaraba? Rikici A Kan Su Wa Suka Haife Ta." Da yake labari ne da ya shafi haihuwa da asali, hatta mahifiyar Balaraba sai da muka tattauna da ita, da kuma wani wan Balaraba mai suna Abubakar, da ita kanta marigayiya. A mujallar kuma an ba da wani labari na wasu mutane 'yan Kano-Jidda wadanda suka so su yaudari yarinyar su saka a karuwanci a Saudiyya.

Daga nan mujallar Fim ba ta kara ba da labarin Balaraba ba sai a fitowarmu ta Oktoba 2001 a cikin labarin bikin ba da kyautukkua ga gwarzayen 'yan fim na shekarar 2001.

Daga nan sai labarin aurenta da Shu'aibu Lawan, wanda ya fito a Fim ta Janairu 2001. Wannan shi ne labari na farko da ya bayyana wanda Balaraba za ta aura. Mun sami labarin daga abokan Kumurci da kuma wasu 'yan gidan su Balaraba din. Tun da fari, a Garkuwa ta Disamba 2001 an yi wani sharhi inda marubucin, Kabir Assada, ya yi shaci-fadin wai Ali Nuhu ne zai auri Balaraba - saboda irin soyayyar da suka nuna a cikin fim din Tasiri 1!

Fim ta biyo wannan labarin da wani a cikin fitowarta ta watan jiya, inda aka sake buga ta tare da Shu'aibu. Wannan dai shi ne labarin da ya fito da batun auren karara, duk duniya ta san za a yi auren, kuma ya taimaka wajen samun dimbin mahalarta daurin auren a Kaduna. Haka kuma ya sa lokacin da Allah ya dauki ran Balaraba mutane daga sassa daban-daban na kasar nan suka rika bugo waya a ofisoshin mujallar Fim suna son su ji tabbacia kan labarin rasuwarta.

Abin bakin ciki da ban tausayi shi ne a wannan watan kuma ga Balarabar a bangon mujalla, a cikin wannan bakin labarin da muke rubutawa tare da kwalla a idanuwanmu.

BALARABA TA MUJALLAR FIM CE!

A ganinmu, marigayiya Balaraba tana da kyakkyawar hulda da mujallar Fim. Ita ce 'yar wasa mace ta farko da ta fara zuwa jaje a ofishin mujallar nan da ke Kano lokacin da wani furodusa ya kai wa Malam Ashafa Murnai hari a ofishin. Baya ga wannan, za a iya kuma cewa idan ka cire Saratu Gidado da Fatima Ahmed, babu wata 'yar wasa da ta taba takawa ta je ta yi godiya a ofis din bayan an buga labarinta sai fa Balaraba. Ranar da mujallar Fim da aka ba da labarin aurensu ta fito, wato 7 ga Maris, 2002, Balaraba da Kumurci sun garzaya ofishinmu na Kano domin su sayi mujalla kuma su yi godiya. Sun dawo washegari da safe bayan daren da suka je ba su sami kowa ba. A cikin ofis din, masoyan biyu sun yi ta yi wa juna barkwanci.

"Ashafs, mun zo godiya." Haka Ashafa ya tuna Balaraba ta furta lokacin da ta dira kafarta cikin ofis din. Ita kadai ce 'yar wasa ko dan wasan da ke kiransa da wannan sunan. Bayan sun yi godiya sun sayi mujalla sai suka kwashi Ashafa a mota suka rankaya suka yi gaba.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin