Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 31   Yuli 2002
BUKUKUWA


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


DAN BOKO SAI 'YAR BOKO

Ahlan ya kasa samari 42 ya auri A'isha, ita kuma ta kasa 'yanmata ba adadi

Ahlan da A'isha
Daga hagu, Ahmed S. Nuhu, Ango Ahlan, Amarya A'isha da Baballe

SAU da yawa idan ta yi wani juyi sai a ga cewa Ahlan (wanda cikakken sunansa shi ne Shariff Aminu Abdu) ya fi kowane dan wasa zuwa ofishin mujallar Fim da ke Kano. Ba a san dalili ba sai wannan lokacin na aurensa ne muka gano cewa ashe ba ziyara jarumin na shirin Laila yake kawo mana ba - a'a, hanya ce kan biyo da shi idan ya je zance gidan budarwarsa, rabin ransa, wadda kuma Allah ya kaddara aka daura masu aure a ranar Asabar, 15 ga Yuni, 2002. Gidan su kyakkyawar amaryarsa, A'isha Mansur Kankarofi, ba ya da nisa da ofishinmu.

An daura auren masoyan biyu da misalin karfe 11:00 na safe a unguwar Yakasai kusa da masallacin Jalli. Kai da ganin yawan jama'ar da suka je wurin ka san Ahlan mutum ne mai jama'a. Haka su ma abokan harkarsa 'yan fim sun cika wurin makil. Darakta Tijjani Ibrahim, Yakubu Muhammad, Sani Musa Danja, Ahmed S. Nuhu, Baballe Hayatu, Nura Imam, Tijjani Faris... kai, da sauransu masu dimbin yawa sun halarta.

Ango Ahlan ya shaida wa wakilinmu cewa ya fara haduwa da A'isha ne wata rana ya je gidan hoto na El-Jamil da ke kan 'Court Road.' A lokacin ba ta san yana harkar fim ba saboda finafinansa ba su fara fitowa sosai ba. Mun tambaye shi yadda sukan karke da ita idan ya je zance, domin kuwa, kamar yadda muka ta`a ba ku labari a wata fitowa ta Fim can a watannin baya, shi mutum ne mai yawan jefa Turanci idan yana magana. Ahlan ya amsa, "Ina jefa mata Turanci amma da yake ita ma 'yar boko ce, sai ta hakura har ta saba."

Amaryar ta gama karatum sakandare a makarantar 'yanmata ta Gyadi-Gyadi, yanzu kuma daliba ce 'yar aji daya a Kwalejin Ilimi (COE) ta Kumbotso, Kano.

Ba a banza akan ga Ahlan kullum a kan hanyar gidan su A'isha ba. A cewarsa, ya yi takara ne da kimanin mutum dai dai har 42. To amma ita din ma, ta yi yakida ''yanmatansa wadanda ya ce "ban ma san iyakar adadinsu ba," kafin ta kasa su ya aure ta.

Lokacin da wakilin wannan mujallar ya je domin su gana, ya samu amaryar cike da murmushi da alamun nuna kunya. Ta bayyana cewa ta yi ta fama da Ahlan idan suna tadi yana jefa Turanci abinsa. "Da dai na so in hana shi, amma da na ga ya zame masa jiki sai na hakura," ta fada tare da dariya, sannan ta kara da cewa, "To sai ga shi ni ma har na saba, kuma ga shi ni ma ina karuwa."

Akwai wani fim mai suna Raina wanda bai fito ba kuma Ahlan ne jarumin fim din. A cikin Raina ya fito da sigarsa, wato irin ta American boy. A'isha ta ce duk da ta san ba haka yake ba, ba ta so rawar da ya taka a fim din ba.

"Matsalar shi ne duk wanda ya kalli fim din zai dauka cewa home boy ne typical," inji ta. Ta kara da fadin, "Ni dai bai burge ni ba!"

Anya kuwa Aisha ba ta son kowane irin wasa da angonta ya yi a cikin finafinai? Cewa ta yi ta fi son abin da ya yi a Sharadi. "Amma ba na son role dinsa na cikin Zunubi da kuma Raina".

A kan batun fim dai, ita dai A'isha so take Ahlan "ya daina fim domin 'yanmata sun dame shi, ni kuma ina mutuwar sonsa".

An kuma tambaye ta batun karatu, sai ta ce tana yin kwas din nan mai suna Home Management, wato Tattalin Gida a hausance.

Yanzu dai sai mu ce Allah ya ba da zaman lafiya. Dan Shi kansa angon dalibi ne a Jami'ar Bayero dan aji biyu, a fannin Ilimi. Haka kuma ma'aikaci ne a wani kamfanin mai suna 'Kwiwa Petroleum.'

A baya bayannan ya yi finafinai da yawa da suka hada da Juyi, Maqabuli, Sulhu, Kutungwila, Sharadi, Raina, Zunubi, Shakuwa, Yaqini 2, Tubali, Salo, Hazzi, Na'am da sauransu.

Tunda mun gano cewa Ahlan kan kawo mana ziyara a ofishin Fim ne dalilin-wadalilatan, shin ko zai ci gaba da ziyartar tunda ya aure makwabciyarmu? Za mu tabbatar nan da watanni biyu tukuna idan A'ishar ta tare a gidansa.

Sakkwatawa sun taya Sadiq Bello Jariri murnar zama cikakken mutum
Daga BASHIR ABUSABE a Sokoto

A RANAR Asabar, 4 ga Mayu, 2002 da karfe 3:30 na rana aka daura auren Jami'in Yada Labarai na (P.R.O.) na Kungiyar Furodusoshi ta Jihar Sakwato, Malam Sadiq Bello Jariri da Malama Zainab a cikin garin Sakkwato. Daurin auren ya samu halartar kusan duk wani dan fim da ke birnin na Shehu. Mahalartan sun hada da shugaban kungiyar furodusoshin jihar (SOFMA), Malam M.Z. Faru, da mataimakinsa Ahmed S. Danjummai, Lawali Tukur Faru, Buhari Master, Nura Sauki, Kabir Assada (wanda shi ne babban abokin ango), shahararren marubucin nan Yusuf Dingyadi, da dai duk wani da ake jin ya kai ya kawo a harkar fim a jihar.

Sadiq, wanda shi ne shugaban 'Algerian Video Link,' mutum ne mai matukar sha'awar harkar finafinan Hausa. 'Yan fim na Sokoto suna ganinsa a matsayin mutum mai da gaskiya da rikon amana. Saboda irin akidarsa ne ma ya sa, a kwanakin baya lokacin da aka cire shugabannin SOFMA aka sake sababbi ba a taba kujerarsa ba, sai ma karin girma da aka yi masa inda yanzun yake rike da mukaman PRO kuma Sakataren Kudi na kungiyar. Haka zalika, Jariri ne janar-sakatare na kungiyar masu saida kayan hannu (Belgium) na Sokoto. Wannan inji wasu yaa nuni da irin kwazon jami'in na SOFMA.

Fim dinsa na farko da zai ji yana nan kan hanya. "Da ma aurena ne ya dan sa mani burki, amma yanzun tunda an gama za mu dawo ma harkar gadan-gadan," inji shi. To, Allah ya ba da zaman lafiya, amin.

Guguwar aure a fagen shirin fim ba ta bar Babannan da Ammaratu ba

GASKIYA an dade ba a ga angon da ya burge 'yan fim ba kamar Abdullahi Ahmed Chiroma, wanda aka fi sani da suna Babannan. Dalili, mafi yawan anguna sukan kidime idan jama'a suka baibaye su. Hakan na faruwa kuwa lokacin da kowa ke kokarin ya gaisa da ango don dai ya san ya je daurin aurensa. Amma Babannan ya ba da mamaki.

Ranar da aka daura masa aure da amaryarsa Ammaratu Isma'ila Mohammed a unguwar Sharada Phase 1 a Kano, a ranar 9 ga Yuni, 2002, jama'a da yawan gaske sun cika wurin. 'Yan fim, 'yan'uwansa, abokai da kuma abokan arziki sun yi dafifi, kowa ango yake so ya gani. Gogan naka ya tsaida hankalinsa wuri daya bai yarda ya fada cikin cajin kai ba.

Duk wanda ya je gaishe shi, a natse zai tsaya ya amsa. Idan abokinsa ne kuwa, har barkwanci Babannan kan yi masa. Yana hada ido da wakilinmu sai ce masa ya yi, "Yauwa! Zo in nuna maka wasu 'yan fim ga su can a zaune". Ya nuna su Barista Lawan na kamfanin 'Binta Investment.'

Babannan dan wasa ne. Ya fito a finafinai kuma an fi saninsa da zama a kantin saida kaset na 'Hajin Fafa Ventures' da ke Gidan Atiku a Sabon Titi, Kano. A yanzu kuma yana karatu ne a babbar kwalejin ilimi ta gwamnatin tarayya ('Federal College of Education') ta Kano.

'Yan fim da yawa sun je. Kadan daga cikinsu akwai Barista Lawan, Ibrahim Danko mai buga kida a kamfanin 'Lenscope Media,'darakta Salisu Mu'azu, sarkin rawa Shu'aibu Idris Lilisco, furodusan fim din Lawisa, Aminu Bala, da sauransu.

Bayan daurin auren, an yi wani wasan kwallon kafa na sada zumunci tsakanin 'yan unguwar Sharada da kuma 'yan fim. Wannan bai rasa nasaba da sha'awar shi amgon ga wasan bal.

Muna addu'ar Allah ya ba da zaman lafiya, amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin