|
'Yan fim suna tseren yin aure-aure
A CIKIN 'yan watannin nan tun lokacin da shekarar nan ta shigo, ga alama 'yan fim gasar yin aure suke yi. A duk wata sai Fim ta kawo labari na aure-auren 'yan fim. To a wannan watan, saboda yawansu ba za mu yi cikakkun bayanai kan auren kowane mutum daya ba, amma mun zubo maku su a kwano daya, ku sa gishiri kawai ku ci da dumi-duminsu. Wannan abin sha'awa ne, kuma zai kara kawar da tunanin da wasu ke yi cewa 'yan fim ba su yin aure. Wani abin sha'awar shi ne yadda 'yan fim suke halartar daurin auren abokan aikinsu a garuruwa daban-daban, suna taya su murna. A shafin da ya gabata dai kun ji labarin auren A'isha Musa. To, ga sauran, kuma mun fara ne da manya-manya, wato Sakatare-Janar na Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Abdullahi Maikano Usman:
Babbar kawar amarya, Fatima Iliya, ta dafa amarya Mariya Abubakar Musa a kafada
|
AUREN ABULLAHI MAIKANO USMAN
DA misalin karfe 2:48 na ranar Jumma'a, 19 ga Juli 2002 aka daua auren Abdullahi Maikano usman, Sakatare-Janar na Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, a layin Kyauta Haske da ke unguwar Mando, Kaduna. Shugaban na kamfanin 'Iman Ventures' ya auri kyakkyawar budurwa Mariya Abubakar Musa.
Daurin auren ya samu halartar manyan furodusoshi da fitattun 'yan wasan fim. Sun hada da A.A. Kurawa, Ibrahim Mandawari, Adamu Moh'd Kwabon Masoyi, Ahmad Al-Kanawy, Auwalu Marshal, Magaji Suleman, Tukur Aliyu, Nata'ala Aliyu, Mustapha Yarima, Galin Money, Adamu Bello Ability, M.Z. Faru, Aliyu Abdullahi Gusau, Yakubu Lere, da Ibrahim Sheme. Sauran sun hada da Ashiru Sani Bazanga, Saminu M. Mahmoud, Yusuf Barau, Yahuza A. Ilu, Ya'u Koli, Musa Karama, Aliyu Abdullahi, Dan'azumi Dafe-Dafe, A.S. Muhammad, Salisu Salinga, da sauransu.
An daura auren a kan sadaki N10,000. Bayan an daura, an rankaya zuwa unguwar su angon, wato Kabala Costain, inda aka tanana ciki da abinci. Yanzu Mariya ce ta uku a cikin matan Abdullahi. Allah ya ba da zaman lafiya, amin.
ALIYU DANGIDA MA YA DARJE DA ZAINAB
ALIYU Dangida dan jarida ne wanda kan dauko labaran 'yan fim ana bugawa a mujallar Abuja Newsweek ko kuma a mujallar Fim. An daura aurensa da Zainab Mustapha Aliyu a ranar 27 ga Yuni, 2002 a garin Shuwaki da ke cikin Karamar Hukumar Kunci a Jihar Kano. Aliyu ne wakilin Abuja Newsweek a jihohin Kano da Jigawa, ita kuma amaryar tasa tana zaune a rukunin gidaje na Shagari Quarters a Kano kuma ma'aikaciyar lafiya ce a Karamar Hukumar Kunci. Ta yi karatun aikin kiyon lafiya a School of Health Technology a Kano. Muna taya su murna.
Aliyu Dangida tare da amaryarsa Zainab Mustafa Aliyu
|
AUREN ZAKIRU A GOMBE
A RANAR Jumma'a, 17/6/02 ne shahararren dan wasa kuma darakta, furodusa a Gombe mai suna Jibril Audu Zakariya (Zakiru) ya yi aure. Misalin karfe 3:30 na yamma 'yan fim na Gombe da suka samu halarta suka fara hallara. Sun hada da shugaban biki kuma tauraron fim din Ciki Da Gaskiya, Abubakar Zabo, da Sadiq Dan Nana, furodusan fim din Abokin Gaba, da Sa'adu Lawan, dan wasa kuma tauraron fim din Abokin Gaba, Sani abokin Gambo (CBN), Bashir Ahmed Sasa na (Fatima Binta Investiment Gombe, da dai sauransu.
Ango Zakiru da Amarya Hauwa
|
Washegari an shirya kalankuwa a katafaren filin wasan kwaikwayo din nan na 'Dadin Kowa Club'. 'Yan fim da 'yan kallo sun cika wurin tun kafin karfe 5 na yamma don su washe idonsu. Jaruman fim din Abokin Gaba, Abdulkadir da Hauwa, sun yi wakar , "Muna Rawa Muna Juyawa," aka yi masu liki. Sa'adu Dan Malllam ya yi wakar cikin shirin Allah Gatan Kowa, Lawan Siraka ya yi wakar Sai Bayan Raina. Har ila yau, Sa'adu Lawan da Bose sun fito sun dan taka. Ango da amarya ma sun yi wakar "Soyayya."
An tashi daga gala da karfe 12 na dare lami lafiya. Dan wasa Sani Gambo (CBN) ya ce, "Wannnan galan mun shirya ta ne don mu taya dan'uwanmu murnar bikin aurensa da ya yi. Allah ya ba su zaman lafiya, amin." Kuma ya ce wannan ita ce gala ta farko da aka shirya don auren wani dan fim a Gombe kuma za a ci gaba da yin haka.
AUREN ALIYU ABDULLAHI A GUSAU
A KWANAN baya mun ba ku labarin auren fitaccen dan wasan
nan kuma jami'in Kungiyar Furodusoshi ta Arewa, Aliyu Abdullahi Gusau, da Asiya, wanda aka daura a ran 9 ga Fabrairu, 2002. To, a lokacin ba a tare ba, sai a ran 22 ga Yuni aka yi bikin babban birnin Jihar Zamfara. A lokacin, an yi walima da karatun Alkur'ani.
Aliyu Abdullahi Gusau (a hagu) da Amarya Asiya tare da jarumi Musbahu M. Ahmad
| Mata sun yi nasu taron bikin a gidan Alhaji Abdulkadir Maibulo Gusau, cikinsu kuwa har da matar Gwamna, Hajiya Husaina Ahmed Sani, da kuma Babbar Sakatare ta Ma'aikatar Al'amuran Mata ta jihar, Hajiya Kulu Anka. Shi kuma ango a bangarensa, ya shirya liyafa a 'Gusau Hotel' wadda aka fara da misalin karfe 8 na dare. Daga Kano, 'yan fim da suka halarta sun hada da Ibrahim Mandawari, Musbahu M. Ahmad, Aina'u Ade, Saima Moh'd da Shamsiyya Habibu, sa'annan dga Sakkwato akwai Hauwa'u Yahaya da sauransu. Duk wanda ya ga hidimar da aka yi ya san an kashe kudi sosai, to amma bukata ta biya, domin ango da amarya sun tare, jama'a kuma babu mai kukan tuwo.
BA A BAR MAWAKI ABUBAKAR SANI A BAYA BA
AN daura auren mawakin nan na kamfanin 'Iyan-Tama Multimedia' mai suna Abubakar Sani da Jamila Yusuf a ranar 26 ga Yuli a cikin unguwar Tumfafi, Kano, da misalin karfe 3 na yamma.
Abubakar bai jima sosai da fara waka ba to amma har tauraruwarsa ta fara haske. Shi ne wanda ya rera wakar "Kada Jita" ta cikin Gagarabadau, da wakar "Ya Ki Taho Abar Sona" ta cikin A'isha 2.
Abubakar ne ya rera wakokin cikin finafinai kamar Daren Farko, Ladaf na 1 da 2, da wata waka ta cikin Halak, Dawayya 2 da wasu da yawa da ke kan hanyar fitowa.
Da Fim ta nemi jin yadda aka yi ya hadu da amaryarsa, sai ya ce ai auren zumunci ne, zuri'ar su ce yarinyar. Amma ya bayyana cewa ya kwashe shekaru uku yana nemanta da aure. Batun wakokin da Abubakar ke rarawa kuwa cewa ya yi amaryarsa tana sha'awar kowace waka da ya rera.
An shirya bikin gala a ranar Jumma'a a Gidan Danhausa a ranar daurin auren inda abokan aikinsa su Alee Baba Yakasai suka cashe da kidan fiyano. Allah ya ba da zaman lafiya, amin.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin
|
|