Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 33   Satumba 2002
BUKUKUWA


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 31
Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Bikin kanwar Sani Danja ya tara mutane

Daga SANI MOH'D MAIKATANGA a Kano

DIMBIN ' yan fim ne suka yi wa fitaccen jarumi Sani Musa (Danja) kara suka halarci bikin auren kanwarsa Fatima (Ladidi) Musa wadda ta auri Abubakar Saminu Kura kwanan nan a Kano. Duk wanda ya halarci bikin ya san lallai Sani yana da masoya a cikin 'yan fim, domin kai ka ce bikin na aurensa ne.

An daura auren a a ranar Asabar, 6 ga Yuli, 2002 a unguwar su Sani, wato Tudun Murtala.

Mahalarta sun hada da Ali Nuhu, Ahmad S. Nuhu, Kabiru Maikaba, Tijjani Asase, Jazuli Kazaza, Rufa'i Kudi da Ali Gote. To amma kada mu yi tuya mu manta da albasa, babban abokin Sani, wato shahararren mawakin finafinai Yakubu Muhammad, yana wurin shi ma a matsayin kijin biki.

Jim kadan da daura auren, amarya ta bayyana mana farin cikinta kamar haka: "I am irin very happy in this day, kuma I am irin grateful to God Almighty Allah. Sannan ina godiya ga 'yan'uwana yadda suka tsaya wajen ganin komai ya tafi daidai. Allah ya saka masu da alkhairi, amin." Shi ma Sani ya yi godiya ga jama'ar da suka halarta, yana mai fatan Allah ya maida kowa gida lafiya. Ya bukaci kanwarsa ta bi mijinta sau da kafa kuma ta rike 'yan'uwansa tamkar nata.

Daga wurin daurin auren an dunguma zuwa 'Sani Abacha Youth Centre' inda aka shirya walima. 'Yan'uwa da abokan arziki sun halarci walimar. 'Yan fim a wurin sun hada da Hajara Usman, Kabiru Maikaba, Ummi Nuhu, Jamila Haruna, Rukayya Umar Santa, Maryam Umar Aliyu, Maryam Abubakar, Fati Bappa Fagge, Baba Sheriff, Ahmed M. Sasari, Rabi'u Ibrahim, Tijjani Paris, Suleiman Sa'eed, Sulaiman Gambo Awaisu, Yusuf Khalid, Musbahu M. Ahmad, Baballe Hayatu, da Ali Mai Dawayya.

Kabiru Maikaba ne ya bude taro da addu'a. Daga nan aka ci gaba da furta kalaman taya ango da amarya murna.

An kuma cashe da wakokin fim daban-daban a wurin. Maryam Abubakar (Jan Kunne) da Ale Mai Dawayya sun rera wakar cikin Darasi 2 mai taken "Duk Girmana Yau Sai Kin Sa Na Yi Kas"; Musbahu da Ummi Nuhu suka yi wakar Kansakali; Yakubu da Fati Bappa suka yi wakar "Mun Iya Renonmu Na Mata" ta cikin Rawani, kuma Sani Danja da Rukayya suka yi wakar cikin Jaheed. An yi tande-tande da lashe-lashe.

Wani abu mai jan hankali shi ne cashewar da amarya da ango suka yi lokacin da Yakubu yake wake su kuma jama'a suna ta yi masu liki. Sai wajen karfe 10 da wasu mintina na dare ne aka fara watsewa daga wurin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin