Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 34   Oktoba 2002
RA'AYI BA GABA BANE


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
HIRAR MUSAMMAN
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
RA'AYIN MUJALLAR FIM
Ra'ayi Ba Gaba Bane
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Rayuwa ce jigon wasa

Daga ADAMU G. YUSUFARI

ANA bukatar kwararrun marubuta ko daraktoci ko 'yan wasa domin tsara labari mai ma'ana wajen shirya wasan kwaikwayo. Ta haka ne za a da wata muhimmiyar rawa da ake son su taka. Wasan kwaikwayo ko kuma labarin shirya finafinai suna da asali ne daga rayuwar dan'adam.

A zahiri, shi marubuci yana amfani da basirar da Allah (s.w.t.) ya yi masa, kawai wajen nuna yadda rayuwa take a rubuce da kuma yin nuni da ire-iren halayyar rayuwa ta hanyar kwaikwayonta. Duk kalmomin da man'oirn basira da ake amfani da su wajen fahimta, ko nazari, kan fasahar wasan kwaikwayo da man can sananne ne a rayuwar jama'a. Domin fahimtar ire-iren wadannan sassa daban-daban din rubutattu ko kagaggun labarai akwai wasu kalmomi kamar su mugunta, ko abin dariya, ko barkwanci, ko bacin rai, alheri, soyayya ko rashin mutunci.

Dukkan wadannan hikima ta nazari ko fasahar wasan kwaikwayo da man can abubuwan da ke faruwa a rayuwar jama'a ko kuma ana iya hango kanshin faruwarsu a nan gaba, wannan shi ne ya sa za ka ga rayuwar jama'a cike da abin mamaki, ko abin tausayi ko abin haushi, ko abin sha'awa, ko abin dariya. A gaskiya ma dai dabi'u da halayyar jama'a su ne ginshikin dalilanmu na yi masu kushe ko yabo.

Dole ne a gano halayen mutum a duniyar nan in har yana raye. Wasu halayen dan'adan suna da dangantaka da asalin mutum. Alal misali, yanayin gida ko iyalin mutum, ko jinsi, ko ilimi, ko arziki, ko addini, ko kuma matsayin mutun a cikin al'umma. Wannan ne ya sa za ka iya ganin mutum ko jama'a na jituwa ko rashin fahimta a tsakanin al'umma.

To wannan kadai ma ginshikin wasan kwaikwayo ne. Kuma ta haka ne za ka iya ganin mutum mai abin alfahari ko abin tsana ga abokan huldarsa. Kowa da ka sani a rayuwarsa, gwanin kansa ne ko gwanar kanta ce. Kuma abokan zama su ne 'yan kallo -kamar 'yan kallon finafinai ko wasan kwaikwayo a gidan sinima, ko gidan bidiyo ko a talbijin, ko kuwa masu karanta littatafan wasan kwaikwayo.

Duk abin da ya yi (ko yake yi) jama'a na kallonsa tare da yin sharhi. Kamar masu yin sharhi a kan ruuce-rubucen adabi, suna yin Allah-wadai ko sa albarka. Kuma a haka ne jama'a ke gyara rayuwarsu. Shi ne ya sa daga baya za ka iya ganin mutum yana da dimbin masoya, abokai ko kuma masu yi masa batanci a idon duniya.

Duk abin da mutum ya yi, dole ne a samu wani abin da za a danganta wannan dabi'ar da ita. Alal misali, idan ka yi dariya, to menene dalilinka na yin dariya? Idan Allah ya yi maka arziki kuma kana taimaka wa masu karamin karfi, mutane na sha'awar su ji dalilinka na yin kirki? Ko kuwa kai shugaba ne mai adali, me ya sa haka?

Wasu kuwa rayuwarsu abin tausayi ce. Wani lokacin sukan yi kamar su kashe kansu da kansu, amma suna gudun magana cewa ai masu matacciyar zuciya ce kawai ko marasa imani ne kawai za su iya kashe kansu.

Komai mutum ya yi a duniyar nan, to, yana yi wa kansa shaida ne. Alal misali, idan mutane biyu suna yin doki-in-doka a kan titi, jama'a za su taru ne suna kallonsu domin tantance gwani a tsakanin mafadatan. Kuma a haka ne, 'yan kallo za su tantance gwaninsu da kuma wanda ba su so a zuciyarsu. To wannan shi ne dirama, an samu gwani da mai barkwanci.

Wasu kalmomi daga cikin fasahar adabi ko rubutun dirama na yin kokarin nuna cewa ai wasu irin dabi'un a cikin basirar aikinsu take. Alal misali, kamar a ce: "Shiga ta farko, kashi na daya", da sauransu. Daraktan shiri na yin amfani da ire-iren wadannan jimloli ne wajen horar da 'yan wasa ko yi wa mai karatu jagora. Ko kuma kokari ko kwarewar jarumai wajen jarraba gwanintarsu ko yin nuni da wata dabi'a domin fahimtar da 'yan kallo ko mai karatu. Duk wadannan dabaru ana samunsu a cikin rayuwar jama'a ta yau da kullum.

Alal misali, akwai wani tsohon wasan kwaikwayo da Wole Soyinka ya rubuta da Turanci mai suna "The Lion and the Jewel. A cikin wannan diramar akwai wani fakirin mutum, malamin makaranta ne mai zunzurutun Turanci a bakinsa. Sunansa Lakunle. Saboda rashin abin duniya ya rasa samun auren yarinyar da yake so mai suna Sidi. To a nan, marubucin yana yin nuni ne da cewa malaman makaranta yawancinsu ba su da isasshen abin duniya a cikin al'umma.

Bugu da kari, akwai wani wasan kwaikwayo da na taba gani (amma ban rike sunansa ba) inda Bashir Bala Ciroki ya taka rawar 'yan sanda. Ciroki ya fito ne a matsayin azzalumi, kuma mai son abin duniya. Saboda haka, a matsayina na mai kare doka, sai na ga yana karbar cin hanci sannan kuma yana sharhi cikin izgili da cewa ai watansu uku ba a biya su albashi ba. To a gaskiya wannan yana faruwa ko ba a cikin shirin dirama ba, wato rashin biyan albashin 'yansanda ko ma'aikatan gwamnati da kuma 'yar dabi'ar karbar hanci domin cin abinci da biyan bukatun yau da kullum.

Wannan haka ne, in har za ka zuba wa al'ummomi idanu, ka yi kokarin gano zamantakewar jama'a to ba lallai ba ne wai sai ka karanta adabin wasan kwaikwayo ko kallon fayafayansu. La Allah, za ka yi hakan ne domin debe kewa ko nishadi. Rayuwa da kanta ita ce dirama.

Daga nan fa, mai nazari zai iya ganin cewa duk wani nau'i ko taskar rayuwa su ne ginshikin labari. Misali, idan al'umma na cikin bacin rai ko murna; ko tana cike da jama'a masu imani ko marasa imani, duk suna yin nuni ne da halayyar al'ummar kamar yadda marubuta suke yin nazari da sharhi a kan rayuwa.

Ta harakar mulki kuwa, idan al'umma na bukatar mulkin soja ne, ko dimokuradiyya, ko amfani da kundin tsarin mulki wajen gudanarwa da zartarwa, duk suna da alaka da rayuwa da zamantakewar jama'a.

Daga karshe, mutum zai iya ganin abubuwa da dama dangane da rayuwa kamar su bacin rai, abota, soyayya, kiyayya, arziki, talauci, har ma zuwa su dariya ko kuma suna yin horo ne ga al'umma saboda jama'a su yi hattara da koyon darussan rayuwa.

Jama'a da dama na yin yabo ko godiya ga marubutan wasan kwaikwayo da jarumai domin yadda suke yi wa al'amuran rayuwa sharhi da kuma kokarinsu na yi wa al'umma gargadi da tunatarwa.

Idan aka yi la'akari da cewa rayuwa ce jigon wasan kwaikwayo, ba wai ana nufin cewa shikenan babu bukatar karanta littattafan adabi ko kallon finafinai ba. A'a, su da man can suna tuni ne ko koyarwa ga al'umma. Abubuwa da dama a rayuwa da ba su yi tasirin da suka yi a yanzu ba. In ba don marubuta ba, wasu tsofaffin al'adu ma da sun bace kwata-kwata.

Ko da ma addini ne, a kan iya kwaikwayon wani al'amari domin tunatarwa da koyarwa. Alal misali, akwai finafinan addini da suke bada tarihin Musulunci ko annabawa ko sahabban Manzon Alah (s.a.w.).

Wadannan dalilan sun zama kalubale ga marubuta, da jarumai, da daraktoci, da furodusoshi da cewa dole ne su yi himma wajen cin moriyar basirarsu domin faimtar da al'umma da nuna wa duniya abin da ya kamata.

Malam Adamu G. Yusufari ne Jami'in Yada Labarai na Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), P.M.B. 1040, Damaturu, Jihar Yobe.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin