Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 35   Nuwamba 2002
Bukukuwa


BABBAN SHAFI
MU LEKA MU GANI
TALLA
Wasiku
KU TAMBAYE SU
Duniyar Finafinai
Rahoto
Malam Zurke
Rayuwarmu
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka
Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da MU LEKA MU GANIn yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Mawaki Sadi Sidi Sharifai ya auri Suwaiba

DAGA SANI MAIKATANGA a Kano

GUGUWAR yin aure da take kadawa a fagen shirin fim ba ta bar shahararren mawakin finafinai din nan Sadi Sidi Abdullahi Sharifai ba, domin shi ma an daura masa aure a safiyar ranar Asabar, 26 ga Oktoba, 2002. Ya auri 'yar'uwarsa Suwaiba Abubakar a gidan babanta Alhaji Abubakar Yusuf Sadauki da ke Lokon Makera a unguwar Diso cikin birnin Kano.

Komai ya yi
Furodusa Tijjani Paris (a dam) ya daga Ango Sadi wurin daurin auren

Dimbin 'yan fim sun halarci daurin auren, kamar su Ishaq Sidi Ishaq, Salisu Mu'azu, Misbahu M. Ahmad, Sani Danja, Yakubu Muhammad, Tijjani Paris, Shu'aibu Idris Lilisco, Abubakar Sani, Idris Danzariya, Ahmad Dandirimi, Bala Anas, Ahmad M. Sarari, Aminu Shariff, Nasiru Dararrrafe, da sauransu.

Da yamma, an shirya walima a dakin karatu na 'Theatre One' da ke cikin Jami'ar Bayero. Da karfe hudu aka ce za a fara, amma ba a fara din ba sai bayan karfe 8 lokacin da angon da amaryar suka iso wurin. Mawakan finafinai maza da mata sun yi kara don taya dan'uwansu murna, inda suka cika zauren walimar. A wurin har da baki daga nesa; misali wasu 'yanmata, Hussaina Emmanuel da Hauwa Ibrahim, sun ce daga Gombe suka zo Kano sai suka tsinci labarin auren na Sadi, shi ne suka tsaya domin su ba idonsu abincinsa.

Bayan gabatar da ma'auratan, an ba jama'a damar su tofa albarkacin bakinsu a kan auren.

Wani abin burgewa hi ne wakokin da shahararriyar zabiyar nan Jamila A. Sadi ta rera wa ma'auratan. Jamila dai budurwar angon ce wadda Suwaiba ta kasa. Wakar "Ina Sonka Na Yaba da Halinka" ta cikin Cika Aiki, ta rera ta a wurin musamman saboda angon. Hauwa Ali Dodo ma ta rera wakar "Carmandudu."

Sauran mawaka ma sun gwada fasaharsu.

Da yake an tabo gonar angon, shi ma ya mike ya rera wata waka da ya shirya domin abokan aikinsa da ba su yi aure ba, irin su Misbahu wanda shi ma yake kan hanyar auren Rukayya Dawayya. Taken wakar shi ne: "Ni Sadi A Yau Na Yi Aure, A Yau Ba Ni Ba Kwanan Soro." Masoya sun yi wa angon da amaryar ruwan naira.

Wani abu da aka yi a wannan daren shi ne nadin sarautar Garkuwan Sadi Sidi Sharifai, aka nada Aminu Mai Dawayya wanda mawaki ne da ya gwanance wajen kwaikwayon wakokin da Sadi ya rera, kamar wakokin shirin Ibro Awilo.

Washegari bikin ya ci gaba inda aka yi kalankuwa (gala) a gidan sinima na Goron Dutse. Abu dai tubarkalla. Mu ma a mujallar Fim muna taya Sadi da Suwaiba murnar wannan auren. Allah ya ba su zaman lafiya da zuri'a dayyiba, amin.

Bikin tarewar Ahlan da A'isha ya burge jama'a

DAGA WAKILINMU

Komai ya yi
Ango da Amarya: Ahlan da A'isha

A RANAR 26 ga Oktoba, 2002 aka yi bikin tarewar dan wasa Ahlan Shariff Ahlan da amaryarsa A'isha, wadanda muka ba ku labarin aurensu a fitowarmu ta watan ..... na bana.

An yi bikin tarewar a 'Meena Heart Restaurant' da ke harabar Gidauniyar Jihar Kano a kan titin Gadon Kaya a Kano da daddare.

Bikin ya samu halartar dimbin fitattun 'yan fim irin su Ali da Ahmad S. Nuhu, Baballe Hayatu, Sulaiman Gambo Awaisu, Ibrahim Mandawari, Shehu Hassan Kano, Mika'il ibn Hassan (Gidigo), Aminu Kwai-A-Baka, Mohammed Garba Kabara, Rukayya Dawayya, Maryam Mashahama, Hadiza Kabara, Ummi Nuhu, Zahara'u Shata, Rabi'u Ibrahim, Jamila Haruna, da sauransu.

Karfe 4 aka yi niyyar fara bikin, amma sai karfe 8:30 aka fara duk da yake an rubuta a katin gayyata cewa, "No African Time," wato ban da makara.

Yawancin abin da aka yi a wurin shi ne rawa da waka, inda akan sako wakar wani fim a rikoda sai a kira 'yan wasa su bi wakar suna yi tare da yin rawa.

'Yan'uwan amarya da na ango sun hallara su ma, tare kuma da mutane 'yan kallo wadanda wasu daga cikinsu sun so su tada hargitsi a wurin inda ta kai an yi sa-in-sa da wasunsu da Mandawari da Rabi'u mai kamfanin 'HRB Enterprises.' Duk da haka an yi bikin lafiya aka kuma tashi lafiya. Allah ya bada zaman lafiya, amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin