Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 39   Maris 2003
Bukukuwa


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
FADI SONKA
Wasiku
NEMAN MAFITA
DUNIYAR FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
Sauran Labarai
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM MAI FITOWA!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
FADI SONKAr sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da tunanin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: Wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, ta da jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Ta yada kwallon mangwaro

Daga ABDULLAHI NASIR (ABILITY) a Zariya o

A'ISHA Ibrahim da Aisha Musa, dukkansu 'yan wasa ne daga Jihar Kaduna, kuma duk sun yi aure a cikin 2002. To sai ga wata A'ishar, watau A'isatu Abdullahi, ta kasance 'yar wasa ta farko daga Jihar Kaduna da ta yi aure a cikin shekara ta 2003. An daura aurenta da mijinta na da a ran 18 ga Janairu, 2003, a Zariya. Shin wacece A'ishatu Abdullahi?

An haife ta a Zariya a 1980. Ta yi karatun firamare da na sakandare duk a Zariya. Ta shiga harkar fim a cikin 2000 lokacin da ta shiga fim din Kaddara na Lerawa Films, Kaduna. Sauran fina-finan da ta fito cikinsu sun hada da Muwafaka inda suka fito tare da Galin Money a matsayin jaruman fim din, sai kuma Zagon Kasa inda ta fito a likita. Har ila yau a Kano ta fito a Sakiya, Ta'asa, Gayya, da kuma Haka Kawai.

Wanda bai san ta ba zai zaci A'isha 'yar Kano ce, saboda duk yawancin harkokinta na fim a Kano ne ta yi su domin a lokacin da take fim ta koma can da zama; koyaushe in ka je Kano za ka rika ganinta a wurin da yawancin a 'yan wasa da furodusoshi ke zuwa, kuma a wurin ne ake aikin editin. Wannan wurin kuwa shi ne "Kwality Audio-Visual' wanda yake 'Zoo Road'. Hasali ma dai ce mata ake 'A'ishar Zariyar'.

Wani abin kunya da ban mamaki shi ne rashin halartar 'yan fim wajen daurin aure A'isha. Tun wajen karfe 1 na rana wakilinmu ya je wajen har zuwa lokacin daurin auren har watsewar jama'a ba wanda ya zo daga Kano ko Kaduna; kai, hatta kawayenta 'yan fim wadanda aka fi ganinsu tare duk ba wadda ta je.

Bayan daurin auren, amarya A'isha ta ja wakilimmu har cikin gidansu a inda ya zanta da ita kamar haka:

Fim: Malama A'ishatu, salamu alaikum.

A'ISHATU: Wa alaikumus salam.

Ki gaya mana tarihin haduwarku da angonki da kuma shi wanene.

A'ISHATU: Sunanshi Garba Ibrahim Datti. Yana zaune a Tudun Wadan Zariya, amma yana aikin dansanda ne a State C.I.D., Kaduna. Kuma mun yi aure da shi a 1999, sai muka rabu.

Af, ashe da ma kun taba yin aure ne!

A'ISHATU: E mun taba yi, amma iyakarmu wata tara zuwa goma sai muka rabu.

Da haihuwa?

A'ISHATU: A'a.

To A'ishatu ga shi kin koma dakin mijinki, ko kina da shawarar da za ki ba 'yan wasa, musamman 'yan 'uwanki mata wadanda ba su yi aure ba?

A'ISHATU: E, shawarar da zan ba sauran mata 'yan fim shi ne, don Allah su yi kokari su yi aure, tare da fatan Allah ya zaba masu nagari.

Ga sauran 'yan wasa da furodusoshi fa?

A'ISHATU: Ina rokonsu da su yi mani addu'a, da fatan za mu zauna lafiya.

Ban ga 'yan wasa daga Kano da Kaduna a wannan biki ba. Ko ba a aika masu ba ne?

A'ISHATU: Ba wanda ban aika mashi ba, sai dai da alama yawanci sai ka je da kanka sannan suke zuwa.

Watau kin aika ne, ba da kanki kika je ba?

A'ISHATU: E.

Daga karshe, ko kina da wani kira da za ki yi?

A'ISHATU: E kiran da zan yi shi ne, da 'yan wasa, daraktoci, furodusoshi da dukkan sauran mutane, wanda na yi masa laifi, to ina rokonsu da su yafe min.

To mun gode, da fatan Allah ya bada zaman lafiya.

A'ISHATU: Amin.

Fati Mai idon Gwal ma ta yi aure

''Kalli idonta! ... kamar idon gwal!'

FITACCIYAR 'yar wasan nan da ke Zariya cikin Jihar Kaduna mai suna Fatima Aliyu (wadda aka fi sani da Fati Mai Idon Gwal) ta bi sahun 'yan wasa mata da suka yi aure a cikin 'yan watannin nan. An daura mata aure da wani mutum mai suna Malam Abdullahi Alhassan a Layin Jibga a Tudun Wadar Zariya a ranar Laraba, 26 ga Fabrairu, 2003.

Fati, jarumar sabon fim din nan mai suna Janhuru wanda kamfanin 'Jari Films' da ke Zariya ya shirya, ita ce yarinyar da ta yi wakar nan ta "Lallabari" ta cikin shirin Halak na furodusa Ahmed M. Sarari (Dakta) a Kano. Ta fito a wasu finafinan da yawa, kamar su Kishi, Zagon Kasa (wadanda ba su fito ba) da kuma Fatahi, Zafin So, Fa'iza, In So, Daren Farko 2 da sauransu wadanda ba su fito ba.

Daurin auren ya burge jama'a, domin 'yan fim da sauran 'yan'uwa da abokan arziki da dama daga Kano, Zariya da Kaduna sun halarta. Tun a ranar jajibirin daurin auren kamfanin Jari ya shirya wata kwarya-kwaryar walima (gala) a 'Kuta Hotel' Zariya don taya amaryar murna, a karkashin shugaban Jari kuma amininta Alhaji Nata'ala Aliyu. Fati dai tana da dimbin farin jini. Shi ma ango Abdullahi, wanda aka ce ya dade yana soyayya da Fati, ya shirya walima don nuna farin cikinsa a ranar da aka daura masa aure da amaryar tasa "mai idon zinari."

Kwanaki kadan kafin a daura mata aure, Fati ta ziyarci ofishin Fim inda ta bayyana farin ciki kan wannan abin alheri da ya same ta, wato aurenta na fari. Ta kuma yi wa takwarorinta 'yan fim mata nasiha da cewa: "Kowace ta yi kokari ta sami miji. Aure shi ne mutuncin 'ya mace."

Ga sauran 'yan fim baki daya kuma ta ce ba wani abu sai godiya. "Na sami daukaka ga jama'a yaro da babba, musamman sanadiyyar fim din Halak."

Wakilinmu ya tambaye ta ma'anar "Idon Gwal" da ake kiranta da shi. Shin don tana da idanu dara-dara ne ko kuwa da yumbun zinari aka yi mata idanun? Fati ta amsa: "Tun ina karama, idan zan je makaranta ('Bako Zuntu Primary School') sai yara su rika cewa, 'Kalli idonta, kalli idonta!' To da na waigo sai wani ya ce, 'Wannan ido kamar idon gwal!'... Ba na son wannan suna amma tilas na dake, na hakura."

Da ta waiwaya baya kan ko tana da wani abin nadama game da shirin fim, sai Fati Aliyu ta ce, "Na sha samun matsala da 'yan matan fim na mayar da ni saniyar ware don sun ga na samu daukaka-musamman a Kano da Zariya." Amma ta yi bayani da cewa, "Kada 'yan Kano su dauka da su nake; da Rukayya Dawayya nake!"

To Fati yanzu babu sauran wariya tunda kin samu mai sonki na gaskiya. Allah ya ba ku zaman lafiya, amin.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin