MUNA daf da buga mujallar wannan watan muka samu labarin kyaututtukan gwarzayen finafinan Indiya na bana guda biyu - wato ZEE CINE AWARDS da kuma MANIKCHAND FILMFARE AWARDS na bana.
Fim din nan mai suna Devdas ne ya yi zarra a dukkan bukukuwan bada kyaututtukan.
An yi bikin ZEE CINE AWARDS a otal din alfarma na 'Tulip Star Hotel' da ke Juhu. An cashe da wakoki da raye-raye daga fitattun jarumai irin su Aishwarya Rai, Shamita Shetty da Esha Deol, yayin da Arbaaz Khan da matarsa Maliaka Arora-Khan suka kasance masu gabatarwa. Alkalan gasar sun kunshi tsofaffin 'yan fim wadanda suka yi tashe a baya, irin su Feroz Khan da Rakhee.
Da ma kowa ya zaci cewa Devdas ne fim din da zai lashe kusan dukkan manyan kyaututtuka. Sun kuwa hada da (a Turance) Best Actor (Jarumin Jarumai Maza), Best Actress (Jarumar Jarumai Mata) da Best Director (Daraktan Daraktoci). Abu mafi ban mamaki a gasar shi ne da Madhuri Dixit ta kasa lashe gasar Best Supporting Actress (Mataimakiyar jarumar Jarumai Mata) da rawar da ta taka da sunan Chandramukhi a shirin Devdas. Maimakon haka sai aka zabi Sushmita Sen saboda wasan da ta yi a fim din Filhaal. Wannan ya tayar da ka-ce-na-ce, koda yake dimbin magoya baya sun ce lallai Madhuri ce ya dace ta ci matsayin.
Wani abin tarihi da aka yi a gasar ta Zee Cine Awards 2003 ita ce da aka ba mutum biyu kyautar 'Best Female Playback Singers' (gwarzayen mawaka mata), wato aka ba Kavita Subramaniam da Shreya Gosai saboda kokarinsu a wakar 'Dola Re Dola' ta cikin Devdas. Haka kuma an ba Nadeem-Shravan (Raaz) da A.R. Rehman (Saathiya) kyautar 'Best Music' (gwarzayen makada), suka doke Ismail Darbar da kidansa na wakokin cikin Devdas.
Duk da yake Devdas ne ya cinye yawancin kyaututtuka, su ma finafinan The Legend Of Bhagat Singh da Saathiya sun ci wadansu kyatututtukan. A kasan shafin nan za a ga jerin wadanda suka yi nasara a gasar.
A gasar 'Manikchand Filmfare Awards 2003' ma fim din Devdas ne ya zama zakaran zakaru. Wannan gasa ta bana ita ce ta 48 da aka yi tun lokacin da aka fara yin ta. An yi bikin ba da kyaututtukanta a daren ranar Jumma'a, 21 ga Farbariru, 2003 a birnin Mumbai, hedikwatar shirin fim na kasar Indiya. Sanjay Leela Bhansali ne daraktan wannan fim din wanda ya ci zunzurutun kudi har da Rs 50-crore.
Devdas yana ba da labarin wata soyayya da wani mashayi yake yi da wata yarinya. Fim din ya ci kyaututtuka har 11, wadanda suka hada da 'Best Film' (gwarzon fim), 'Director' (darakta Sanjay Leela Bhansali), 'Best Actor' (Jarumin Jarumai Maza, Shah Rukh Khan), 'Best Actress' (Aishwarya Rai) da 'Best Actress in a Supporting Role' (Madhuri Dixit).
"Kowa yana tambayata abin da ya sa na kashe kudi tsababa haka a kan labarin wani mashayi, to amma sai ga shi ya doke masu hankalin," cewar darakta Bhansali.
Da aka ce shi ya ci matsayin Jarumin Jarumai, sai da Shah Rukh ya yi kamar zai yi kuka. A jawabinsa ya ce wannan kyauta da ya ci a cikin shekararsa ta 11 da shiga harkar fim tana da muhimmanci musamman tunda zai dauki wani dogon hutu saboda a yi masa tiyata a gadon bayansa kwanan nan. "Ina fatan zan ci gaba da dawowa ina lashe gasanni," inji shi.
Ita ma Aishwarya Rai ta ce a duk tsawon wannan daren, za ta dinga gode wa duk wani wanda ya taimaka mata har ta samu kyautar.
Devdas ne har ila yau ya ci kyautar 'Best Choreography', wato tsara rawa, wadda aka ba gwanin koyar da rawa Saroj Khan, da 'Best Female Playback', wato gwarzayen zabiyoyi (Kavita Krishnamurthy da Shreya Ghoshal).
Fim din kuma ya ci kyautar 'Sony scene of the year', da wasu kyaututtukan wadanda suka shafi nagartar aiki a tsarin shirya fim da fasaharsa..
Fim din Saathiya ya biyo bayan Devdas, ya ci kyautar 'Best Music' (A R Rahman), wakoki (Gulzar), 'Best Screenplay' (Mani Ratnam) da mawaki namiji (Sonu Nigam). Gulzar (Saathiya) da Jaideep Sahni (Company) su biyu aka ba kyautar 'Best Dialogue', sa'annan aka ba Jaideep Sahni kyautar 'Best Story' da fim din Company.
Rani Mukherjee da Manisha Koirala ne aka ba kyautar 'Critic's Award for Best Actress' (wato kyautar manazarta); ita Rani saboda wasanta na cikin Saathiya, ita kuma Manisha saboda wasanta na cikin Company.
An ba Ajay Devgan kyaututtuka biyu na 'Critics' Best Actor' saboda fitowarsa a matsayin bos a shirin Company da kuma dan tawaye mai neman kwatar 'yancin kai a shirin The Legend of Bhagat Singh. Shi ne kuma ya ci gasar 'Best Actor in a Villainous Role' (wato bos) saboda wasansa cikin fim din Deewangee. Kyautar 'Critics' Award for Best Film' kuma fim din nan na Raj Kumar Santoshi mai suna The Legend of Bhagat Singh ne ya ci ta. Rahman aka ba kyautar 'Best Background Score' saboda kidansa na fim din.
Paresh Rawal ya ci kyautar gwarzon cali-cali ('Best Actor in a Comic Role') da wasansa cikin (Awara Paagal Deewana). An ba Vivek Oberoi, wanda masu gabatarwa suka kira da sunan 'The man of the moment', kyautar 'Best Male Debutant' (sabon jarumi) da 'Best Actor in a Supporting Role' (shirin Company). Esha Deol ta ci kyautar gwarzuwar sabuwar jaruma ('Best Female Debutante'), to amma saboda ta makara, ba ta karbi kyautarta da hannunta ba.
Hasali ma dai 'yan wasa da dama ba su karbi kyautarsu da hannunsu ba. Sun hada da Ajay Devgan, Paresh Rawal da Madhuri Dixit.
Shi wannan biki na 48 na 'Manikchand Filmfare Awards 2002' an yi shi ne a dakin taro na Bandra-Kurla da ke filin MMRDA a daren ranar Jumma'a a matsayin girmamawa ga sana'ar fim ta Indiya. A wurin an yi la'akari da bunkasar da masu shirya fim din Indiya a kasashen waje ke yi. An yi haka ne ta hanyar taka rawa da waka a dakin taro, wadanda Rahul Khanna da Neha Dubey suka yi lokacin da aka jefo kida daga fim din Monsoon Wedding, wanda a kasar waje aka shirya shi.
Wasu kyaututtuka biyu da gwamnatocin kasashen Birtaniya da Siwizalan suka bayar sun nuna tasirin finafinan Indiya a kasashen ketare. Two special awards by the British and Swiss governments further acknowledged the impact of Indian films overseas. Mataimakin jakaden Birtaniya a Indiya, wato Howard Parkinson, ya karrama Yash Johar, furodusan Kuch Kuch Hota Hai da Kabhie Khushi Kabhi Gham. Mista Parkinson ya ce akwai mutum milyan 1 da dubu dari uku 'yan kasar Birtaniya wadanda asalinsu Indiyoyi ne, wadanda kuma suke matukar son finafinan Indiya. Shi ko Shah Rukh Khan, gwamnatin Siwizalan ce ta turo masa da kyautar musamman saboda yadda finafinansa suke yawan nuno tsaunukan kankara na kasarta, inda akan nuno shi yana cashewa da rawa da soyayya har aka dauka tsaunukan su ne aljannar masoya; jarumar nan Geraldine Chaplin, diyar shahararren aktan nan Charlie Chaplin, ita ta mika wa Shah Rukh kyautar.
Wata zabiya 'yar birnin Mumbai, wato Shreya Ghoshal, wadda daddadar muryarta ce jaruma Aishwarya Rai ke bi a shirin Devdas, ita aka ba kyautar 'R D Burman Prize for the Best Upcoming Talent in Music.'
An bai wa 'Jumping Jack' Jeetendra da Rekha kyaututtukan 'Lifetime Achievement Awards'.
Gwanin tsara kwalliya (Art director) mai suna Nitin Desai wanda ya kirkiri dandamalin shirya fim mai ban mamaki, kamar yadda ya kirkiri dakin rawa (nightclub) tare da kawata shi da ruwa mai zubowa daga samaniya da kwayayen wutar disko, don wakar Yana Gupta ta 'Babuji zara dheere chalo' da tartasin wutar da ke tashi a waka da rawar da Aishwarya ta yi mai suna 'Dola re', shi ma ya ci kyauta.
Kai, abin dai sai wanda ya gani. A cikin rugundumin wannan biki, industiri din ta dakata ta tuno da wadanda suka kwanta dama a shekarar da ta gabata, irin su jagorori Harivanshrai Bachchan, Dina Pathak, Anand Bakshi, Bhagwan Dada, Naseem Bano da Kaifi Azmi.
An ci gaba da cashewa har gari ya waye. Aikin da Shah Rukh Khan ya yi na mai gabatarwa ('master of ceremonies') a karo na farko a rayuwarsa ta sa kowa yana ta murmushi yayin da Shah Rukh din yake ta ba mutane dariya da barkwancin da ya rika yi tare da Saif Ali Khan.
An kawata dakin taron dai da kwayayen lantarki har 16,000 a karkashin jagorancin daraktan tsara dandamali Nitin Desai.
Wani karin bayani game da fim din Devdas shi ne, shi ne shirin da kasar Indiya ta shigar a matsayin fim dinta a gasar finafinai ta duniya (Oscars) wadda akan yi a Amerika. Amma fim din bai kai mataimakin karshe na zabe ba ('nomination'). Wannan ya ba jarumi Shah Rukh Khan da furodusan shirin, Bharat Shah, haushi, har suka ce to ai ba karshen sinimar Indiya kenan ba. Sun so a ce shirin ya ci kyautar 'Oscar Foreign Film' a gasar wadda za a bayyana sakamakonta a karshen wannan watan. An yi fim din na Devdas daga wani littafin hikaya da marubuci dan Indiya mai suna Sarat Chandra Chatterjee ya wallafa. Lokacin yin fim din an samu matsaloli da dama. Jami'an tsaro sun kama furodusa Bharat Shah, ma'aikata biyu sun mutu a wani hadarin lokeshin sa'annan darakta Bhansali ya bata da kusan kowane mutum lokacin daukar shirin. Duk da haka, fim din ya ja hankalin jama'a a bikin finafinai na duniya da aka yi a Cannes cikin Faransa, ya lashe gasar ZEE Awards a Mumbai, ga shi kuma ya yi zarra a gasar 'Filfare Awards.' Yanzu ba abin da masu fim din da 'yan wasan cikinsa ke yi sai murmushi kamar kurma ya yi amarya.
Jerin zakarun ZEE CINE AWARDS 2003
BEST FILM: Devdas
BEST DIRECTOR: Sanjay Leela Bhansali (Devdas)
BEST STORY: Jaideep Sahni (Company)
BEST ACTOR: Shah Rukh Khan (Devdas)
BEST ACTRESS: Aishwarya Rai (Devdas)
BEST ACTOR IN A SUPPORTING ROLE: Vivek Oberoi (Company)
BEST ACTRESS IN A SUPPORTING ROLE: Sushmita Sen (Filhaal)
BEST ACTOR IN A NEGATIVE ROLE: Ajay Devgan (Deewangee)
BEST ACTOR IN COMIC ROLE: Paresh Rawal (Awara Paagal Deewana)
BEST MALE DEBUT: Vivek Oberoi (Company)
BEST FEMALE DEBUT: Malini Sharma (Raaz)
BEST MUSIC: Nadeem Shravan (Raaz) and A R Rahman (Saathiya)
BEST LYRICIST: Gulzar (Saathiya)
BEST MALE PLAYBACK: Sonu Nigam (waka mai sunan fim din, wato Saathiya)
BEST FEMALE PLAYBACK: Shreya Ghosal and Kavita Subramaniam (Dola re dola; Devdas)
BEST BACKGROUND SCORE: A R Rahman (The Legend of Bhagat Singh)
BEST CINEMATOGRAPHER: Binod Pradhan (Devdas)
BEST CHOREOGRAPHER: Saroj Khan (Maar dala, Devdas)
BEST SOUND: Robert Taylor (Saathiya)
BEST EDITING: A V Mayekar (The Legend of Bhagat Singh)
BEST SCREENPLAY: Mahesh Bhatt (Raaz)
BEST DIALOGUE: Piyush Mishra, Ranjeet Kapoor, Rajkumar Santoshi (The Legend of Bhagat Singh)
BEST ACTION: Amin Ghani (The Legend of Bhagat Singh)
BEST ART DIRECTOR: Nitish Roy (23 ga Maris, 1931 Shaheed)
BEST COSTUME: Neeta Lulla, Abu-Sandeep, Reza Shariffi (Devdas)
LIFETIME ACHIEVEMENT AWARD: Hema Malini
QUEEN OF HEARTS: Preity Zinta
TRUE INDIAN ACTRESS: Aishwarya Rai
DYNAMIC DUO: Dino Morea, Bipasha Basu
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin