Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 45   Disamba 2003


BABBAN SHAFI
GASKIYA DAYA CE
HIRA DA DARAKTOCI
Wasiku
NEMAN MAFITA
SHARHI KAN FINAFINAI
RAHOTO
Malam Zurke
RA'YIN FIM
Bukukuwa
ADABI
SABUWAR FUSKA
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka

Bangon FIM TA 45. Danna nan ka gani!
Bangon FIM TA 44. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 43. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 42. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 41. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 40. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 39. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 35. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 34. Danna nan ka gani!

Bangon Fim ta 33. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 32. Danna nan ka gani!
Bangon Fim ta 31. Dannan nan ka gani!
Bangon Fim ta 30. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 29. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 28. Danna nan ka gani!
Bangon FIM ta 27. Danna nan ka gani!
SABON FIM YA FITO!!
Daga Mujallar FIM

KAR KA BARI A BA KA LABARI!!
Akwai shahararrun 'yan wasa a ciki!!
Sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

KASH! Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

'Yan wasa: Farida Jalal, A.A. Shariff (Momo), Kasimu Yero, Bashir Nayaya, Abubakar Yusuf Ladan, Hajara Usman, Sani Idris Moda, Sani Garba S.K, da Rashida Bello.

Darakta: Aminu A. Shariff

BABU IRINSA!

 


In kana son mu aika maka duk lokacin da muka canza shafin nan
    
   Za mu rike sirri  

by ChangeDetection

Manyan darussa daga littafin Ruwan Raina

Daga IBRAHIM SHEME

SUNAN LITTAFI: Ruwan Raina

MARUBUCIYA: Amina Abdulmalik

WALLAFAWA: Farid Ventures, Abuja

SHEKARA: 2000 (ya fito a 2001)

SHAFUKA: 243

WANNAN littafi yana daga cikin manyan littattafan hikaya da aka wallafa da Hausa a cikin 'yan shekarun nan. Idan ka dubi yawan shafukansa da sarkakiyar jigonsa da kuma dab'insa, za ka iya kwatanta shi da duk wani littafin hikaya da aka taba wallafawa da Hausa. Za mu iya kwatanta shi da manyan littattafai irin su Karshen Alewa Kasa na Bature T. Gagare, da kuma ma wadansu wadanda suka fito kwanan nan, irin su Ci Talatarka… na Sakina A. Aminu da littafin Balaraba Ramat Yakubu din nan, wato Ina Sonsa Haka. A lura cewa shi wannan littafi Ruwan Raina, tare da sauran biyun nan na mata da na ambata a sama, sun shigo da wani sabon salo a adabin Hausa wanda ya bambanta da wadanda muka sani a baya, kuma abin mamaki mata ne suke jagorantar sabon salon.

Manazartan adabi sun yi amanna da cewa a yawancin lokuta idan mace ta yi rubutun hikaya, to in ka bincika za ka taras labarin gaske ne ta rubuta, kuma labarin ya shafe ta kai tsaye. Ita marubuciyar Ruwan Raina, ba ta boye wannan ba, domin ko a bangon littafin hoton mijinta ne aka buga, kuma ta ce wannan labarin ba almara ba ce. Saboda haka tunda dai an gabatar da littafin a matsayin hikaya, sai mu dauka irin dabarar nan ce ta gwamutsa kagawa da gaskiya a cikin labari aka yi. Ita marubuciyar ta fi kowa sanin yawan karin da ta yi a cikin zahirin gaskiyar labarin, in har ta yi karin. Shi kuwa manazarci, aikinsa ne ya dubi littafin a yadda yake, ba tare da ya yi wani waje yana wani bincike na daban ba. Saboda haka mu a nan abin da kawai za mu yi kenan wajen nazarin wannan littafi.

Ruwan Raina dai labari ne na wasu ma'aurata guda biyu, matasa, wato Amina da mijinta mai suna Abdulmalik wanda yake tsananin kaunarta. An faro labarin daga lokacin da suka hadu suka fara matsananciyar soyayyarsu. Shi Abdulmalik ya dawo daga Amerika kenan inda ya gama karatun nazarin lafiyar dabbobi, ya fara aikin gwamnati, sannan kuma a bisa shawarar mahaifinsa yana neman yarinyar da ta dace ya aura. Sai ya gamu da Amina, wadda 'yar makarantar sakandare ce mai yawan alkunya, kuma aka daura musu aure bayan ya cika dukkan sharuddan al'ada da na addini na yin aure.

To daga nan fa suka fara wata irin rayuwar aure wadda kowa yake cewa ba a san irinta ba. Misali, an nuna cewa angon bai san amaryarsa a daren farko ba kamar yadda ake yi a ko'ina a duniya, sai bayan wata da watanni. Wai shi nan yana ta kiwonta ne saboda ta shirya wa wannan muhimmin daren ta fuskar jikinta da tunaninta. To halayensa da suka biyo baya, sun ma fi wannan zama wadansu irin halaye. Mutum ne wanda son matarsa ya rufe masa ido, ba ya son ko kuda ya taba ta, kuma a kowane lokaci yana son ya ji fatar jikinta a jikinsa; ko nan da can ba ya so su rabu, sai ka ce karamin yaro. Duk motsawa kadan sai ya sumbace ta, kuma yakan sa faifan kade-kaden Turawa su yi ta rawa a falo, sa'annan ya dinga shaida mata irin son da yake yi mata, abin ma har ya gundure ka. Akwai dabi'a da ya tsira kuma ya kafe a kanta, wato dabi'ar yin barcin rana tare da matarsa a kullum. Yakan yi kokarin ilimintar da ita a kan al'amuran rayuwa iri-iri, kama tun daga kan aikinsa na sha'anin dabbobi har zuwa yadda ciki ke shigar mace da yadda da yake girma a cikin ciki. Wasu abubuwan da yakan koya mata, a al'adance mace takan koye su ne daga wurin mata 'yan'uwanta ko iyaye, amma shi gogan naka ya nace a kan lallai shi da kansa ne zai koya mata.

Ita kuwa Amina, ta kasance yarinya mai tsananin jin kunya, don sun share watanni ko hada ido ko yin zance sosai da shi ba ta iya yi. In ba domin Abdulmalik mutum ne maras boye tunaninsa ba, kuma wanda ba ya yin kasa a gwiwa wajen gudanar da al'amuransa, to da cin karfin ran Amina har ta sauya zai yi matukar wuya. Saboda rashin kawaicinsa, hatta holewar da ya dan taba a Amerika sai da ya fayyace mata, to amma ya tabbatar da cewa yanzu ya tuba. A cikin mayen soyayyarsa yakan nuna irin ni'imar da Allah ya yi wa Amina a matsayinta na 'ya mace. Za a ga haka a shafi na 149 zuwa na 159 musamman inda shi da abokinsa Abbas suke tattauna wannan al'amarin tare da yin amfani da kalmomi cikin hikima irin su 'maliya' da sauransu. Irin wannan bayyana komai din ya tabbatar da cewa shi dai Abdulmalik ya bambanta kwarai da sauran mazaje. To amma ba wanda zai ce Abdulmalik ba ya son matarsa; babu wani wuri da aka nuna cewa soyayyar karya ko ta fatar baki yake yi mata. A gaskiya shi miji ne wanda mata da yawa za su so su samu irinsa saboda sadaukarwarsa.

Abdulmalik yana son haihuwa. Shi ya sa da Amina ta yi bari ya yi kamar zai zautu. Da ta sake samun ciki kuma sai ya rika tattalinta kamar kwai, duk dai don kada cikin ya kuma zubewa. Ta wannan hanyar za mu fahimci cewa shi mutum ne mai tausayi da kyautata wa jama'a, daga kan matarsa har zuwa iyaye da 'yan'uwa da kuma masu yi masa aikatau a gida. Akwai wani lokaci da wani yaronsa ya ji wa wani biri da ya kamo a daji rauni, abin ya bata wa Abdulmalik rai sosai domin shi A.M. (kamar yadda Amina kan kira shi) mutum ne wanda ba ya son a zalunci kowace irin halitta.

Shin wace irin soyayya ce wannan? Ita kanta Amina Abdulmalik takan tambayi kanta haka. A shafi na 199, ta rubuta cewa, "Idan da za a iya cewa soyayya ta yi yawa to a bisa gaskiya sai a ce wannan soyayya ta su Abdulmalik ta yi yawa. Idan mutum ba ya gani da idanunsa ba da wuya ya gaskata."

To, kwatsam, bayan an yi watanni sha hudu da yin auren nan mai rikirkitacciyar kauna, sai Abdulmalik ya yi wani mugun hadarin mota a kan hanyarsa ta dawowa daga Kano inda ya je wani bikin aure, kansa ya tsage, ya mutu. Batun bakin ciki wurin Amina ba a cewa komai. Gaba daya ta kidime ta kasa karbar kaddara don ci gaba da rayuwarta ba tare da Abdulmalik ba. To kuma tana cikin taskun bakin ciki sai ta fuskanci sababbin matsaloli. A garin sai mutane suka camfa ta a kan wai ita ce sanadiyyar rasuwarsa, domin wai tana da "farar kafa" - wai yana rayuwarsa cikin ci-gaba ya auro ta amma a karshe ga shi ya mutu yana yaronsa. Ga mari ga tsinka jika, sai kuma aka hada ta auren dole da wani dattijo wanda ya yi jika da ita, wanda ba ta kauna fiye da mutuwa kanta. Abin da ya biyo baya shi ne sai mijin ya shiga azabtar da ita don ya fashe haushin gabar da ta nuna masa. Har dukanta ya rika yi, kuma yana yi mata allura da magani mai sa barci don ya samu kwanciya da ita. Saboda ita dai ta kasa mantawa da Abdulmalik, ga shi iyayenta sun ki yarje mata ta karo karatu, sa'annan ga bakar wahala a hannun mijinta na biyu, duk abu ya taru ya cabe mata har ya kusa sa ta yin hauka. Kai, ai Amina har dan haukan ma ta taba, rayuwarta kuma ta gurbace.

A babi na 14 marubuciyar ta yi kokarin kammala labarin tare da yin sharhi kan mugun yanayin rayuwar Amina da kuma yadda al'ummarmu ta dauki mata ba a bakin komai ba. Ta nuna cewa Amina dai ta wahala ne saboda kaddarar rayuwarta da kuma al'adu. A babin da ya gabaci wannan ta bayyana mana cewa juna biyu da Amina ta samu a gidan Abdulmalik dab da zai rasu, shi ma ya zube. Wannan abin bakin ciki ne a gare ta domin kenan babu wani tabbataccen abin tuno A.M. dinta a rayuwarta. A babin karshe, marubuciyar ta kawo wasu hujjoji da ta ce sun ba ta damar "fayyace komai" dangane da rayuwar aurensu da Abdulmalik, wanda har ya hada da batsa. Ta kawo ayoyi da hadisai da ta ce sun ba ta wannan damar. Haka kuma ta yi bayanai kan gaskiyar labarinta, don kada wasu su dauka duk zuki-ta-malle ce kawai ta shirya. Ta rubuta a shafi na 234, "Kada wanda ya yanke hukunci a kan Amina sai idan ya tabbata ya ratsa daidai irin halin da ta ratso ko kwatankwacinsa to sannan za ya iya yin hukunci."

Akwai wata waka ta juyayi har shafi tara mai taken, "Don Soyayya" a karshen littafin wadda ta yi daidai a matsayin kammaluwar littafin. Wakar ta nuna zurfin kaunar da Amina ke ji game da mijinta (na farkon) a lokacin yana raye amma ta kasa bayyana masa saboda tsananin kunya irin ta al'ada. Ita wakar ba ta da kafiya amma duk da haka tana cike da fasaha da bayyanar da dimbin bege, kuma ta alamta cewa wannan hadi na Amina da Abdulmalik hadi ne wanda ba zai yanke ba har abadin abadin.

To amma fa wannan labari na Ruwan Raina ya bar gibi a wurare da yawa, bai amsa wasu tambayoyi ba. Misali, a babin karshe ta bayyana cewa wulakancin da mijinta na biyu ya rika yi mata (wato allurar sa barci don ya tara da ita) ya sa ta sami ciki, to amma ba ta gaya mana ko ta sami haihuwar wannan cikin ba ko kuma idan dan yana da rai. Shin ko Amina ta samu kubuta daga kangin aurenta na biyu? An nuna cewa al'amuran sun auku ne a zamanin farkon shekarun 1970; duk da yake ba a ba da kwanan wata a littafin ba, amma mutum zai iya gane haka daga bayanin cewa Janar Gowon ne ke mulki a lokacin, sa'annan kuma a shekarar da Abdulmalik ya rasu shugaban kasar Habasha din nan Haille Selasse (marigayi) ya kawo ziyara nan kasar. To amma kuma sai muka ga an bige da ambaton wasu abubuwa na kwanan nan, kamar rikicin zaben Abiola da labarin mika mulkin da Janar Abdulsalami Abubakar ya yi ga Cif Obasanjo duk a labarin. To me ya auku ga Amina daga misalin 1973 (an kirkiro Naira da Kwabo!) lokacin da kila zahirin taskun Amina ya faru, zuwa yanzu? Shin ta karo ilimin kamar yadda take da buri? Shin yaushe ta rubuta littafin? Abin mamaki, ba a nuna mana ko akwai wani kokari da surukan Amina (na bangaren Abdulmalik) suka yi wajen agaza mata ba wajen gyara rayuwarta; shin ko sun manta da ita ne, ta je ta fuskanci taskunta ita kadai, tare da camfa ta?

Babu wanda zai karanta wannan littafi dai ba tare da ya koyi wasu muhimman darussa na rayuwa ba. Saboda an gina labarin ne a kan wani ginshiki na kyakkyawar tarbiyya, wadda aka debo daga al'adu da addini, sai mai karatu ya ji tausayin ukubar da Amina ta shiga; sai mu ji kamar mu ma abin ya shafe mu kai tsaye. Rasuwar Abdulmalik ba zato ba tsammani wani darasi ne da ke nuna cewa dukkan mai rai mamaci ne; sa'annan da Amina ta yi ta-maza ta je cikin makabarta din nan ta zauna a gefen kabarin Abdulmalik tana ganin ana kawo gawarwaki ana rufewa, dole mu farka mu fahimci cewa mu mutane ba a bakin komai muke ba, domin rayuwa gajeruwar lokaci ce maras dadi.

A matsayin aikin adabi, littafin nan ba karamin hobbasa ba ne, musamman da yake da Hausa aka rubuta shi (don yawancin Hausawa 'yan boko sun fi son yin rubutu da Turanci a yau). Kalmomin da aka yi amfani da su tare da sauran nau'o'in nahawu sun dace, sai dai kamata ya yi a ce an ba wani edita ya gyara littafin sosai kafin a buga shi. Wani abin lura kuma shi ne shi kansa sunan littafin bai dace ya zama haka ba duk da yake sunan ya dace da jigonsa, dalili shi ne akwai wani littafi mai irin wannan sunan wanda ya riga fitowa tun shekaru kadan da suka gabata; wannan ko shi ne littafin hikaya wanda marubucin nan na Kano mai suna Mohammed Lawan Panshekara ya rubuta.

Duk da yake Amina Abdulmalik ta fito da Ruwan Raina ne saboda wani abu da ya faru a gare ta, zai kyautu a ce ta yi amfani da wannan baiwa da Allah ya ba ta ta ci gaba da rubutun adabi na Hausa. Akwai matsaloli barkatai wadanda za ta iya yin rubutu a kansu, musamman ma wadanda suka shafi mata da yadda ake amfani da al'ada ana cutar mata a kasar nan. Kada ta yi watsi da wannan dama da take da ita, musammam a wannan lokacin da kasar Hausa take kishirwar marubuta masu tsantsar fasaha irin tata.

A karshe, dole mai karatu ya tambaya: wacece ita kanta Amina Abdulmalik da ta rubuta littafin? Shi wannan littafi wanda aka sadaukar ga matar Sardauna wadda aka halaka, wato Hafsatu, bai yi mana wani bayani ba game da marubuciyar. (Hajiya Amina dai 'yar asalin Jihar Katsina ce, kuma a yanzu tana zaune a Abuja). Mutane za su fi gaskata labarin in da sun san ko wacece ita. A nan ina taya Amina addu'ar Allah ya jikan Abdulmalik, kuma ina addu'ar Allah ya ba Amina Abdulmalik sa'a a wannan fage na rubutun adabi. Sauran kuma mu ga fim din Ruwan Raina wanda tun tuni ta fara fafutikar ganin an yi shi.

Fassarar sharhin da na yi a jaridar 'Weekly Trust' ta ran 12 ga Disamba, 2001.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin