Daga AISHA ABBA AHMED
FIM din Qaya ya kunshi labarin wata yarinya Amal wadda ake kashewa a wani daji. Yarinyar dai 'yar wani mutum ce mai arziki kuma Balarabe mai suna Alhaji Abdullahi da kuma babarta Hajiya Bilki. Tana da kanwa Amina, kuma ta kasance tana soyayya da wani yaro da ake kira Yahuza, amma daga dukkan alamu tata soyayyar ta fi tasa karfi.
Bayan mahaifinta ya lura da soyayyarsu sai ya dora Yahuza kan shugabancin kamfaninsa kuma ya daura masa aure da Amal, wato ya taka tudu biyu. Amma akwai alamun cewa Yahuza dai dukiyar mahaifin nata yake kwadayi ba wai sonta yake yi na hakika ba. Saboda haka a lokacin da ta nemi su je kilisa (picnic) sai bai yarda sun je a lokaci guda ba, wato ita sai ta riga shi zuwa kuma ta yi ta jiransa har aka zo aka kashe ta. Kuma a wani sashe na wurin shakatawar da suka je an nuno wata da 'ya'yanta uku 'yanmata da namiji sun je shakatawa a wurin, amma su har da kyamarar daukar hoton bidiyo suka je, kuma namijin shi yake daukar hotunan. Ya saita kyamarar ya bar wurin sai ta goce har ta isa wurin kisan Amal saboda haka kila ta hasko.
Ana haka jami'an tsaro suka shiga bincike saboda shugabansu aboki ne ga Alhaji Abdullahi kuma ya sha alwashin sai ya gano wanda ya yi kisan. Ba tare da wani bata lokaci ba ya dora hakkin binciken a kan wani jam'i, Sufeto Bashir wanda yana zagaye a wajen binciken ya tsinci karan taba a wajen da aka yi kisan, kuma daga baya yake fahimtar cewa irin tabar da Yahuza yake sha ce.
A sakamakon ceton Hajiya Bilki da Amina da Bashir ya yi daga hannun wasu miyagu, ya saba da gidan Alhaji Abdullahi inda kuma akwai alamun soyayya za ta shiga tsakaninsa da Amina, to amma kuma babanta ya riga ya bayyana sha'awarsa ta hada Amina din da Yahuza aure. Ko da mahaifiyar Amina ta tuntube ta da maganar, ba bata lokaci a take ta watsar da zancen tare da yin ikirarin ba zai yiwu ba.
Bayan matsancin binciken da Bashir yake dada yi a kan Yahuza, abin ya kai makura, rannan sai wasu miyagun mutane suka dira a gidan jina-jina. To ko waye ya aiko su kuma? Oho! Sai dai a kashi na biyu na shirin za mu tabbatar.
Shirin ya yi kyau, labarin kuma ya tsaru. To sai dai akwai 'yan matsalolin da ba a rasa ba. Ga wadanda na ci karo da su:
Babu sauti mai kyau (watakila daga wajen rikodin ne a kasuwa).
Kala ta yi yawa a hoton wanda na kalla.
3. A wakokin babu ta gargajiya kuma muryar mawakan ba ta kamaci masu bin wakokin ba.
4. An zuzuta karar duka da ake yi a fim din idan ana buga kofa. Lokacin da Bashir ya je gidan Alhaji Abdullahi ya buga kofa Amina ta bude kofa, to ina kira ga Amina nan gaba.
5. A matsayinsa na sufeto, bai kamata Bashir ya dinga yin tsalle-tsalle ba yana faman wakoki kamar wani dan disko.
6. A al'adance, 'picnic' ba dabi'ar Bahaushe ba ce kamar yadda aka nuna iyalin Hausawa sun je a fim din, kuma ma dai sakon da fim din ke isarwa shi ne illar 'picnic' din.
Duk da haka an yi kokari a shirin. 'Yan wasa sun nuna kwarewa. Haka shi ma darakta ya yi bajinta tare da bayyanar da fasahar da aka san shi da ita. Fim ne da ya dace mutum ya kalla domin ya nishadantu, kuma ya karu da darussan da ya kunsa.
Qarni
Kamfani: S.B. Ventures, Kano
Shiryawa: Sabo Abdulmajid
Darakta: Hafizu Bello
'Yan Wasa: Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Hussaini Sule Koki, Aminu Ahlan, Aminu HUdu, Binta Musa Kaduna, Fati Abubakar, d.s.
Daga AISHA ABBA AHMED
WATA al'umma ce ta wani zamani wadanda ke bautar ungulu, suna zaune a tsakanin wasu duwatsu a daji. A cikinsu akwai wani yaro wanda lokacin da shekarunsa suka kai kamar 13 sai gunkinsu Mardu ya shaida wa babban limaminsu cewa in suka bar wannan yaro ya girma zai kawo musu sabon addini. Aka yi ta shawarwari kuma aka yarda a kan cewa mahaifiyar yaron (Ali Nuhu) ta yanka shi ta kuma kawo jininsa a bai wa Mardu. A take aka hada ta da wani majiyin karfi domin ta yanka yaron a gabansa. Da yake a gaban yaro aka yi magana sai ya ranta a na kare. Da gajiya ta debe shi sai ya fadi sumamme. Wata mace cikin shudayen kaya ta bayyana ta kuma dora hannunta a kansa, suka bace.
Bayan shekaru sai wani halitta ya addabi wata al'ummar daban, amma wadannan Musulmai ne kuma da harshen Hausa suke magana, ba kamar masu bautar Mardu ba masu yin magana da wani harshen maguzanci (Bulungudu). Ita wannan halitta yakan kashe 'yanmata ne masu kamar shekaru 20, kuma yanayin kisan duk iri daya ne. Nan fa hankalin jami'an tsaro ya tashi domin an kasa gane kan al'amarin. Wani jami'i da ya kware a kan irin wannan bincike (Nura Hussaini) ya shiga aiki, inda ya je wajen wani furofesa (Zulkiflu Muhammad) domin ya taimaka masa. Furofesan ya tambaye shi wasu abubuwa shi kuma ya amsa masa, a nan kuma ya ba shi bayanin wannan halitta kaf.
Jami'i da abokan aikinsa suka bazama neman wannan halitta a wani surkukin wuri, suka kuma yi sa'ar ganinsa. Amma sun sha wahala, domin lokacin da jami'in ya yi yunkurin kama shi, shi kuma ya doke shi ya zube kasa. Yana dawowa hayyacinsa sai ya bi halittar da gudu kuma suka hadu a waje. Cikin irin binciken da jami'in ya yi har da na sanin cewa halittar nan ba ya son ruwa, aka kuma ci sa'a ya nufi wurin da wani rafi yake ba tare da ya sani ba. Jami'in ya yi wuf ya sha gabansa ya rika debo ruwa yana watsa masa a fuska, har ya ci lagonsa ya fadi wanwar.
Aka tafi da wannan halitta kuma jami'an suka shiga bincike ta hanyar amfani da na'urori na zamani domin a karanta kwakwalwarsa da tunaninsa. Ta haka ne suka gano yadda matar da ta tsince shi ta ya yi masa wasiyya da shan jinin 'yanmatan da ba su wuce shekara 20 ba, duk ranar 14 zuwa 15 ga kowane wata kamar yadda yake yi. Da suka gama binciken sai suka mika mutumin ga likitoci inda suka cire masa wasu abubuwa da suka yi tsiro a jikinsa ya kuma koma mutum ras.
Bayan ya dan zauna a cikin mutane ya kuma karbi Musulunci, sai jami'an suka yanke shawarar cewa za su ba shi taswira domin ya kama hanyar garinsu. Ya kama hanya har ya isa wurin da maguzawan suke a daidai lokacin da suke ta wakoki da shagulgulan bautarsu, suna kuma gama waka shi kuma ya kira sunan Allah da karfi har duk hankalin maguzawan ya dawo kansa, nan kuma suka san bako ya zo musu.
Shugabannin suka zaunar da shi suka shiga yi musa tambayoyi har suka gano cewa shi ne yaron da aka yi umurnin yankawa; amma me ya dawo da shi bayan an yanka shi? To zaune dai ba ta kare ba, sai aka shiga shawarar ko a kore shi daga garin. Haka dai ya ci gaba da zama a masaukin da aka ba shi tare kuma da bayyana addininsa a fili, kuma har ya fara yada shi. Ya yi nasarar jan hankalin wata yarinya (Fati Abubakar) har ta fara bijire wa bautar Mardu. Matasan garin suka yi kungiya suka nufi inda yake kuma suka nuna masa bacin ransu a bisa yada addininsa da yake yi, shi kuma ya hakikance a kan cewa addinin gaskiya ya zo kuma dole su yarda domin babu yadda za su yi. To ko zai yi nasara ko ba zai yi ba sai mun ga kashi na 2.
Lallai Qarni ya ci sunansa, kuma ya yi ba-zata. Hafizu Bello ya dada canza akalar shirinsa zuwa wata siga da ba a saba gani b. Babban yunkurin fim din shi ne ya bayyana akida ta addini daban tare da yada manufofinsu.
Fim din ya kwatanta ci-gaba da aka samu ta hanyar kimiyya, wato ta irin na'urorin da aka yi amfani da su wadanda yawanci ake gani a finafinan Amerika. Wani abin burgewar shi ne irin kwalliya da siddabarun da aka yi wa Ali Nuhu; dubi yadda aka maida shi mana. Hoto ya fito kuma magana ta dauku sosai. Yin amfani da wani 'yare' (Bulungudu, wanda a hakikanin gaskiya babu shi a doron kasa), tsantsar hikima ce. Marubucin wakar fim din, Abubakar Sani, ya nuna cewa shi ma kanwar lasa ba ne a fagen tsara waka da rera ta. Ya bai wa mutane mamaki.
Akwai 'yan kurakuran da ba za a rasa ba a fim din. Na farko dai idan an matso da hoton halittar dodon kusa (closeup) ana gane cewa kwalliya ce aka yi masa; da an bar hoton a dan nesa da ya fi. Na biyu, ya kamata a yi hira da malamai, ta yaya za a ce za a saka mutum a cikin komfuta? Na uku, ya kamata a ce su Hussaini Sule sun kara tsufa a lokacin da Ali ya girma ya dawo, to amma sai muka ga ba bambanci sosai. Na hudu, wai Ali wane irin da ne da ya ga mahaifiyarsa a haukace bayan dawowarsa, kuma ya tuno ta amma ya share ta bai kula da ita ba? Na biyar, da an nuna cewa daya daga cikin 'yanmatan da dodon ya kashe ta yi kokarin guduwa; abin nufi shi ne ba a nuna kowace ta yi yunkurin ceton kanta ba. Na shida, yanayin mutane da bautarsu, da ma yanayin wakarsu da shigarsu ta fi kama da mabiya addinin Buddha. Na bakwai, fim din ma bai kwashi shekarun da za a kira shi Qarni ba domin akowane karni ana nufin shekaru 100 ne. Na takwas me zai sa Ali ya rika ihu yana faman fada a kan sai an karbi addininsa? Ai ba haka ake jan ra'ayin mutum zuwa Musulunciba.
To mun ga Qarni da aka dade ana jira, sai mun hadu da almuru.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin