NA yi murna matuka da gaske da ganin makalar Ali Nuhu mai taken "Iya Ruwa Fidda Kai" kuma wacce ta fito a shafi na 24 a mujallar Fim ta Fabairu 2003. Ba don komai ba sai saboda jaruntar da Ali ya nuna wajen fitar da ra'ayinsa na dalilan da suka sa ya shiga harkar fim, da kuma nuna fahimtarsa game da manufar ita kanta harkar gaba daya a rayuwar kabilar Hausawan zamani. Duk wanda ya karanta wannan makala tasa, kuma ya tuna da hirar da aka yi da shi a Fim ta Maris 2000, zai san lallai Ali bai yi nisa daga inda ya fara ba. Makalar kuma ta nuna cewa Ali a shirye yake da ya yi tanbaba da jama'a a kan ra'ayinsa. To madalla.
Sai dai, kash! Sai kuma ga shi Ali Nuhu ya fitar da wadansu ra'ayoyin da babu kyakkyawar hujja. Idan mutum ya fitar da ra'ayin kansa game da duk wani abu, ba za a ga aibunsa ba domin ai ra'ayi ba gaba ba ne. Amma fitar da ra'ayi da kuma yanke hukunci a kan abubuwan da babu kyakkyawar madogara zai zama rashin adalci ga wadanda ake yanke wa hukuncin. A nan zan fitar da wurare uku a inda shi kansa Ali ya ce yana kalubalantar mutane da su. Na farko, ya ce: "..manyan finafinai da suka fi yin kasuwa duk na soyayya ne…in da a ce soyayya ta gundire su (masu sayen finafinan Hausa) da ba a yi rububinsu ba..."
Ya kawo wannan ne domin ya karyata-ko kuma ya kalubalanci-masu cewa finafinan Hausa na soyayya ne kawai. Dole a ja da shi a kan wannan. Idan aka duba finafinan Hausa, za a ga kashi 95 daga cikin 100 duk na soyayya ne. Wannan babu tanbaba. Labaransu-jigonsu- duk daya ne: ko mata biyu na son saurayi daya, ko kuma maza biyu na son mace daya. Wannan jigo ya yi kasuwar da ya fada a farko-farkon bunkasar finafinan Hausa, ba don komai ba sai saboda fitar da kaimin da ke zuciyar matasa. Wannan ta faru ga rububin da aka dinga yi wa littattafan kagaggun labaran Hausa da akan kira Labaran Soyayya. Ko finafinan da Ali Nuhu ya kawo a misalai, ba na kwana-kwanan nan ba ne, kamar Ki Yarda Da Ni, Sangaya, da Daskin Da Ridi. A lokacin da wadanda suka shigo harkar fim suka ga kasuwar, misali, Ki Yarda Da Ni, kafin ka ce kwabo duk an raja'a a kan wannan jigon. Shi ya sa a yanzu, a tsakiyar shekarar 2002 har zuwa farkon 2003, aka gaji da jin labarin soyayya-kuma aka daina sayen finafinan, kasuwar ta cunkushe (wanda shi ne dalilin da ya sa ya rubuta makalar tasa-neman mafita). Jigogin da ya fada na cewa ana yi, kamar su "adventure" da "comedy", su ne suka cika gurbin 5% din da ya rage a dukkan jigogin finafinan Hausa.
Na biyu, ya kalubanci ilimin Mass Comm (ilimin sadarwa)-daga masu koyar da shi, har masu koya-kuma babu kwakkwarar hujja-a inda ya ce: "…wani lokaci shi ya sa nake kalubalantar furofesoshi da doktas dinmu da suke sukar finafinanmu, musamman masu tunkaho da cewa su ne malaman Mass Comm (wato ilimin sadarwa) wanda har suke daukar finafinanmu suna bai wa dalibai domin su yi mana bincike, har suna zaginmu… su daliban in ka ajiye masu kamera ba su san yadda za su yi aiki da ita ba…"
Allah Sarki! Wannan ya nuna fahimtar Ali game da nazarin ilmin sadarwa, watau Mass Communications, ta tsaya ne kawai ga iya rike kamera. Akwai fannoni da yawa, amma ba ni ne zan yi masa jawabi a kansu ba. Ya kuma nuna cewa tunda ba za su iya rike kamera ba, to jahilai ne-saboda dai ai duk mai ilimi zai iya aiki da shi, in kuma ya kasa, to da shi da jahili wanda bai san abin ba duk daya ne-kuma duk mai karanta Mass Comm babu abin da ya sani-domin kwakwalwarsa ba za ta iya rike darasin rike kamera ba. Ba shi da wata kwakkwarar hujja ta yanke wannan hukuncin, domin bai kawo misalan daliban Mass Comm, kuma daga wace jami'ar ba, da ya ba su kamera ya ce su yi aiki da ita suka nuna masa ba su iya aiki da ita ba. Kuma shi ba malami ba ne a bangaren Mass Comm na kowace jami'a, saboda haka ba shi da hujjar nuna cewa duk daliban Mass Comm dakikai ne, ba su san komai ba.
Nazari kuma a kan finafinansu (ban sani ba ko fushi yake yi an yi nazari a kan finafinan FKD, ko kuma duk finafinan Hausa na bidiyo) ai ya zama dole-ko ya so ko ya ki, domin ana nazarin domin ganin yadda finafinai suka shafi al'adun jama'a. Ba ma wai a nan Nijeriya ba, duk inda ka san ana finafinai a duniya, to ana nazarinsu - daga nazarin labaransu, zuwa tsarinsu, da tsara su. Sannan sai nazari a kan yadda suka shafi al'adar rayuwar dan'adam. Hasali ma dai akwai masu yin digiri daga na farko har na uku a kan nazarin finafinai. Shi kansa Ali, a lokacin da yake dalibi a Jami'ar Jos, ai ya yi nazarin littattafan wadansu, inda ya yarda da wadansu, ya ce bai yarda da wadansu ba a cikin kundin digirinsa. Saboda haka nazari nau'i ne na fadada ilimi, da mamaki a ce Ali Nuhu ya kalubalanci wannan, saboda ta nazari ne za a samu ci-gaba, a nuna mai kyau da mummuna, sannan da kuma yadda za a gyara. Amma da yake Ali kudi ya sa gaba a harkar finafinan ba daukaka ilimi ko yada al'ada ba, shi ya sa yake fushi da nazarin finafinan da ake yi-kada a zuba masu yashi a cikin kwakinsu.
Abin takaici, a yanzu a duniya babu wanda ya fi Dokta Brian Larkin, daga wata jami'a a Amerika, kwarancewa a nazarin finafinan Hausa, da kuma danganta su da Indiyanci. Har ma abin ya zama abin haushi yadda yake yawan nuna cewa duk wani fim din Hausa na bidiyo da ka gani yanzu, to an wanke shi ne daga Indiya. Wannan ba daidai ba ne-akwai finafinan basira da yawa-amma duniya ba ta san da haka ba, domin ire-iren Ali Nuhu su ne masu son su yada wa duniya cewa Hausawa ba su da basirar kirkiro labarai, sai dai kawai su wanke labaran bautar gumakan Indiya. Ga kadan daga cikin nazarin da Dokta Larkin ya yi a kan finafinan su Ali Nuhu, kuma wadanda aka buga a shahararrun mujallun nazari na duniya:
§ Why Indian films travel: African videos, Bollywood and global media. Interdisciplinary Research Group Africa (IDOGA), The social and religious life of media in Africa. 'Filmzaal', Film-Plateau, Paddenhoek 3, 9000 Ghent, The Netherlands, 2002.
§ Muslim audiences in Kano and Korhogo: Love stories and Indian films, Africa: The Journal of the International African Institute Volume 67 No 3 1997.
§ Indian Films and Nigerian Lovers: Media and the Creation of Parallel Modernities. Africa. 67(3): 406-440. 1977.
§ Mediating the Sacred: Electronic Preaching and the Transformation of Muslim Identity in Northern Nigeria.
§ African Video Films Under the Sign of Neoliberalism.
§ Media Worlds: Anthropology on New Terrain. Faye Ginsburg, Lila Abu-Lughod, Brian Larkin eds. Berkeley: University of California Press, 2002.
§ Hausa Dramas and the Rise of Video Culture in Nigeria. In: Jonathan Haynes (ed.), Nigerian Video Film. Ohio: Ohio University Press, 2000.
§ Introduction, Media and the Design for Modern Living. Brian Larkin (ed.)
Special Issue, Visual Anthropology Review 14 (2), 1999.
§ Theaters of the Profane: Cinema and Colonial Urbanization. Special Issue 'Media and the Design for Modern Living'. Brian Larkin (ed.) Visual Anthropology Review 14(2): 46-62. 1999.
§ Cinema Theaters and Moral Space in Northern Nigeria.ISIM Newsletter 3. July 1999:13, 1999.
§ Colonialism and the Built Space of Cinema in Nigeria. In, City Flicks: Metropolitan Life and Modern Indian Cinema. Preben Sepstrup ed. Occasional Paper no. 22, International Development Studies, Roskilde University, 2002.
§ "Indian Films and Nigerian Lovers: Media and the Creation of Parallel Modernities." In, The Anthropology of Globalization. A Reader. Jonathan Xavier Inda and Renato Rosaldo eds. Oxford: Blackwell Books, 2002
Sai Ali Nuhu ya ci gaba da cin zarafin malaman Mass Comm, inda ya nuna su ma, kamar dalibansu, jahilai ne ba su san komai ba, inda ya ce: "…yanzu za ka ga dokta ko furofesa ba abin da bai sani ba (game da shirin fim) a makaranta, amma in aka ajiye masa kamera bai san yadda zai dauki wannan kamerar ba. Saboda haka, kalubale gare su: duk wani da yake tunanin muna yi ba daidai ba, ya zo shi ya gwada mu gani, ai akwai wadanda a da sun fara. To suna ina? Ai sun gudu!"
An ce dai muhimmancin ilimi, a yi amfani da shi. Idan mutum yana da ilimi, ya kasa amfani da shi, to ya zama jahili. A nan Ali Nuhu ya nuna jahilcin duk malaman Mass Comm na duniya (domin bai yi iyaka a kan malaman da yake kalubalanta ba), domin, kamar yadda ya ce, ga shi dai suna da ilimin, amma su ma sun kasa yin amfani da shi, domin ko kamera ba za su iya rikewa ba. Anya kuwa an yi adalci a nan?-domin tsananin dagawa ka ce duk wani malami na Mass Comm a duniya jahili ne saboda, a hukuncinka, bai zai iya rike kamera ba? Ya ko san yadda ake tsara manhajar ilimin Mass Comm, a inda dole sai an kai dalibai sun yi aiki zahiri (practical) a cikin horon nasu-amma a ce duk ba su iya rike kamera ba? Ko kamera ita ce misalin tsantsar jahilinci su a wajen Ali Nuhu, domin ita ce tabbas dole sai da ita za a yi fim?
Kuma bai gaya mana malaman da suka fara finafinai suka kasa ba. Idan dai ya fadi wannan maganar domin ya ci zarafin wani malami da na sani, to bai yi adalci ba, domin shi wannan malamin ya saka Ali a cikin fim din da Ali Nuhun yake cewa daga shi malamin bai kara yin wani ba-watau ya ga wuya ya gudu kenan.
Na uku, sai maganar wanke finafinan Indiya, a inda Ali Nuhu ya ce, "Haka kuma mutane suna nuna cewa kamfaninmu na FKD mun ta'allaka ne kan finafinan Indiya kawai, wai ba za mu kirkiri na kanmu ba. Wannan ai maganar banza ce tunda fim nawa aka yi wadanda kirkira aka yi amma ba su yi kasuwar wadanda Indiya ne muka juya ba? Ka ga kamar Kudira da Sabani duk kirkirarsu aka yi, amma ai ba su yi kasuwar Mujadala, So da Zubaida ba…Mu dai muna nan kan bakanmu na juya finafinan Indiya…." (an kara tisi a wani baitin).
Wannan ya fito ya nuna wa duniya cewa Ali Nuhu-mai zagin dalibai da malamansu da nuna cewa jahilai ne-ya shiga harkar finafinai ne kawai domin ya yi kudi, amma ba domin ya inganta al'adun Hausawa ba. Har ma zage-zage yake yi (duk wanda kuke hira da shi ka ce da shi "wannan maganar banza ce", to tamkar ka zage shi ne-in dai Hausawan Fulani da na sani ne) a kan ana son ya nuna basirar kansa, ba ya saci basirar wadansu ba: kuma su ne suke kokarin yaki da barayin zaune-sai ga shi sun fi kowa satar basir wadansu. Ya ce in ya nuna basirarsa, to ba zai yi riba ba, saboda da haka, bari ya saci basirar wadansu. Allah Ya saukake!
Abin da Ali ya kasa fahimta shi ne, duk fim din da Indiya suka yi, sun yi shi ne a kan doron bautar allolinsu-kowane irin fim ne, ba wai sai mai suna Hare Rama Hare Krishna ba-duk gaba dayansu. Su Indiyoyin da kansu suka fadi haka a wurare da yawa-littattafai da mujallun tarihin sinimominsu (wanda na tabbata Ali duk ya karance su, domin ba ka fara sace basirar wani ba tare da ka san salsalar basirar ba), da kuma gidajen yanar intanet. A lokacin da Ali yake Majalisar Finafinan Hausa a Yahoo! Groups, mun aiko wa da 'yan majalisar wadannan bayanan. Amma ko karanta su bai yi ba. Saboda haka duk fim din Indiya da aka wanke zuwa Hausa, ana wankowa ne tare da daudar bauta wa gumaka. Kai tsaya ma! Ai su kansu 'yan Indiya din, su ma satar basirar finafinan Amerika da Turai suke yi; domin da yawa daga cikin finafinansu su ma wankin finafinan Hollywood din ne. Misalan finafinan Hollywood da Indiyawa suka wanke sun hada da Beverly Hills Cop (suka mayar Jalwa), Die Hard (Baazi), For A Few Dollars More (Sholay), Lethal Weapon (Farz), Face/Off (Jung), Romancing the Stone (Hifaazat), The Godfather (Satta bazar). To ai ka ga abin ya zama batan-bakatantan kenan, sata ta saci sata!
Ali Nuhu ya ce ai akwai rawa da waka a al'adun Hausawa. Kwarai, akwai-amma wadanne iri? Ba dai irin wadanda ake wankowa a finafinan Indiya ba. Ai akwai na gargajiya yadda za a iya amfani da kayan kidan zamani, in dai wai lallai sai an fitar da zamanin yanzu, sannan a aiwatar da shi. An yi haka a fim din Kogin Bagaja, inda kusan duk raya-rayen na kashi 1 na fim din, daga wake-waken gargajiya ne, duk da cewa kidan a zamanance aka yi shi. Wannan ai fitar da basira ne na wanda ya yi wannan ingantattacen fim din. Me ya sa Ali ba zai iya irin wannan ba? A'a, saboda naira kawai. Ya nuna haka a hirar da aka yi da shi a Fim ta Maris 2000 a shafi na 15. Ga yadda hirar ta kasance:
"Fim: Ko kana ganin yin raye-raye da wake-wake a fina-finan Hausa bai dace ba?
"Ali: A gaskiya ba abin da zan ce a kan wannan magana sai dai na ce a yafe mu, amma rawa da waka yanzu muka fara. Dalilin da ya sa na fadi haka kuwa ba komai ba ne illa wadannan abubuwa (rawa da waka) da ake yi suna daga cikin abubuwan da suke sayar da wadannan finafinai. Na san mutum zai ce ba al'adarmu ce ba, ara muka yi… kuma tunda a cikin 'yan kallo akwai wadanda suke da sha'awar wannan abu, to babu yadda muka iya, dole ne mu rinka yi. Sai dai kawai abu daya da za a ba mu shawara, shi ne a dinga kokari ana cusa al'ada ciki; idan ka fadi haka ni ma na amince.."
Sai dai kuma ga shi bai dauki shawararsa ba; abin ma sai dada dagulewa ya dinga yi, domin kusan duk lokacin da wani fim din Indiya ya burge shi, kafin ka ce kwabo, ya wanke shi-ba tare da ya san salsalarsa ba. Wannan ba yada al'adun Hausawa ba ne-ko da yake ban san irin rukunin Hausawan da yake nufi ba, domin akwai Hausawa na ainihi, watau Maguzawa, sannan kuma akwai Hausawan Fulani. Maguzawa ba Musulmi ba ne, saboda haka idan ana wankin finafinan Indiya domin su ne, to babu laifi-bautar gumaka sai ta hadu da kafirci kenan (ko da yake su kansu Maguzawan yanzu suna ta rungumar Musulunci, Alhamdulillah). To amma Hausawan Fulani tsantsa, wadanda suka fi kowacce al'umma yawa a nan kasar, Musulmi ne, saboda haka in dai domin su ake wankin finafinan Indiya domin a nishadantar da su, to ana cutarsu, domin kullum sai an yarfa masu daudar mishirikanci-sai kuma dada lalata adabinsu da ake yi.
A makalarsa, Ali ya nemi ya ci zarafin wani malamiwanda ya zama babban furodusa a wani fim din da shi Ali Nuhun ya fito, inda yake cewa ai an fara, amma "sun gudu!" Wannan fim din babu rawa babu wakar Indiya, kuma ya nuna zahirin rayuwar Hausawa matasa a zamanin yanzu. Lokacin da aka nuna shi a sinima, har tafi aka yi, domin ya nuna basira ingantacciya. Idan Ali ya fitar da fim kwaya daya tal wanda ya kamanci rabin-rabin rabin wannan a basira da ma'ana, to lallai zai fara zama hadadden dan wasa mai ma'ana, ba baragada ba.
Ba a ce kada a yi rawa da waka ba, in ta kama dole. Amma akwai na gargajiya, wadanda muka gada kaka da kakanni. Yadda Indiyawa suke tunkaho da nasu, haka mu ma dole mu yi tunkaho da namu. Babu yadda za a yi ka ga Indiyawa sun kwafi wani labari ko fim na Hausawa. Don me mu za mu kwafi nasu? Wannan ba yada al'ada ba ne, gurguntar da ita ne. Kuma na yi maka imanin cewa a duk lokacin da aka nuna wani daga finafinanmu ga Indiyawa, to dariya za su yi mana. A yanzu haka, saboda irin masu ra'ayi na Ali Nuhu, duniya ta dauka Hausawa ba su da basirar yin fim, har ma su Dokta Brian Larkin (a Amerika) da Furofesa Graham Furniss (a London) suna nuna cewa finafinan 'yan kudu (Nigerian Films) sun fi na Hausawa inganci-saboda su Hausawa 'yan wankin daudar Indiya ne kawai. An yi wa Hausawa adalci kuwa?
Taken makalar da Ali Nuhu shi ne Iya Ruwa Fid Da Kai (wanda a Turanci za a iya fassarawa da By any means necessary). Zan rufe wannan martanin da wani karin maganar: Kowa ya daka rawar wani, zai rasa turmin daka tasa (Don't be a loser).
Allah Masani.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin