DA farko ina taya 'yan'uwana 'yan fim da sauran al'ummar Musulmi bakin cikin rashin da muka yi na maigida, dan'uwa, mai kishin zuciya, mai kuma son ci-gaba, wato Tijjani Ibraheem. Allah ya ji kansa, ya sa ya huta, amin summa amin. Su kuma iyalansa Allah ya ba su hakurin rashin da suka yi. Allah ya yaye masa duhun kabari, ya sa karshen wahalar kenan, ya yaye masa kurakuransa shi da dukkan 'yan'uwa Musulmi, amin!
Bayan haka, a farkon maganata nake cewa ya zama wajibi harkar fim ta samu ci-baya. Duk yawan addu'a ko daukar mataki na kowace irin hanya ba zai hana ma harkar finafinai mutuwa ba. Domin masu yin harkar ne suka kashe ta.
Zamanka mai ilimi, komai neman ilimi, zai yi matukar kara maka kwarin gwiwa wajen gudanar da harkokinka na rayuwa. Duk lokacin da ka sami kanka marar neman ilmi kuma mai ganin ya iya ba tare da cikakkiyar shaidar iyawa ba, a cikin kowane lokaci za ka samu ci-baya cikin kowadanne harkokinka na rayuwa.
Wannan dan misalin ya yi daidai da halin da masu shirya finafinai suke ciki. Ainihin masu yin fim mafi yawancinsu ba su da cikakken ilimi, kuma sun kasa nemansa. Masana ilmin dan'adam sun gano cewa kowane ilmi ana fin wanda ya je makaranta ya karance shi, bayan ilmin aikin likita.
Farkon shekarar 1996 da fim ya fara yawa a cikin jihohinmu forudusa nawa darakta nawa muke da su? A cikin wan-nan harka, in ba za kumanta ba har du'a'i ake yi kan fim in an kalli kashi na farko, domin kashi na biyu ya fito cikin lokaci, saboda tsabar gamsuwa da aka yi da kashi na farkon. Wannan kadai ya isa ku yanke wa kanku hukuncin cewa harkarku ta fara samun matsala sahihiya. Lokacin da na sami bayani a kan kungiyoyin da kuka shirya, ta furodusoshi daban ta daraktoci daban, sai na kara jin dadi, ina ganin harkar fim ta samu ci-gaba. Ashe ba haka abin yake ba. Ci-gaba ne irin na mai gina rijiya A cikin wani hasashe da nake yi, ina ganin kamar wadannan kungiyoyi ba za su amince wa wani ya zama furodusa ko darakta ba sai tare da ya cika wasu sharudda, wanda ashe ba haka abin yake ba. Ban taba zama cikin mamaki ba in aka ce mini yau Jihar Kano tana da furodusoshin da yawansa ya kai 250 zuwa 300; ko daraktoci kawai na san za a sami sama da 200 da kari.
A nan arewacin Nijeriya jihohi 19 muke da su har da Abuja. ASHIRIN kenan. Na tabbata abu ne mai matukar wuya a ce ga wata jiha wadda Hausawan cikinta ba su yi kokarin shirya fim na Hausa ba. Da wadanda suka iya da waydanda ba su iya ba, duk kasuwa guda za a hadu. Mai karatu, tambaya gare ka: wane lokacin ne za a bambanta direba da fasinja?
Wannan harka tana jaririya amma tsakanin furodushi da daraktoci da yawansu ya kai 1,000 da kari ke jagorancinta wanda ya zama wajibi a sami matsala.
Wani abin tambaya shi ne, shin Bahaushe kowanne Larabci yake ji? Da yawa na san akwai Yarabawa da Inyamurai, masu yin fim na Hausa har ma da wasu kabilu wadanda ba su da wata nasaba da kabilar Larabawa. Amma sai ka ga sun yi fim da sunan Larabci. Abu mafi daure kai wanda yake tare da ni yawancin finafinan shekara ta 2002 duk sunansu Larabci ne. A matsayinka Bahaushe (darakta ko furudusa) kuma kana takama da harshen na Hausa, me zai kai ka yin fim da sunan Larabci kuma ba Larabci ake yi cikinsa ba?
Ina biye da kai tare da hujjata. Masana ilimin dan'adam sun sha bayanai a kan cewa harshe ba ya bunkasa sai tare da yana aron wasu kalmomi daga wani yare daban. To, in muka duba furodusoshin Kano da na Kaduna su kadai ne Hausawa, ko su kadai ne masu aro kalma, in suka fadi sunan fim (furodusoshin Kano da na Kaduna) Hausawan Sakkawato da na Kebbi da Zamfara har ma da Nijar ba za su fayyace ainihin sunansa da kalmar Hausa ba. Yau muna wajan shekara dubu da kari da kafuwa amma a ce sai yanzu ake aron kalma - yana yiwuwa kuwa?
A ganina, duk wadannan suna daga cikin abin da ya sa aka rage kallon finafinan Hausa. Misali, ka je kasuwa sayen kaset ka kasa karanta haruffan da aka rubuta a jikin kwalin kaset, to me zai kai ka sayensa? Abin da ya sa ni fadar wasu furodusoshi hade da daraktoci ba su da ilimi (ina nufin ilimi na Hausa) shi ne, a nahawun rubutun Hausa na san babu harafin 'Q', E, na kuma san akwai k.b.d. Mai karatu, me ke akwai cikin wadannan finafinai da ake kira na Hausa? Bukulu, Qauli, Thakun Sa'ah, Khusufi, Jaheed, Aqiba, Isa'ah, Huznee, Dhalal, Noor, Kudirah, Yakanah.
In muka dubi wadannan da kaifin basira, a ina za mu aje su bare ma wasu ararrun kalmomi wadanda ba su ci kasar Hausa ba, kamar haka: Manuba, Zilla, Garari, Kansakali, Kacibus, Kafiya, Yarfe, Sammatsi, Narjis, Sunduki, Izaya, Shauki, Badali. A cewar wani malamin jami'a, ba Hausa ba ne, in kuwa har ana zaton Larabci ne, to ba ingantacce ba ne (Gargaliya ce). Har wa yau, wasu sunaye mamaki suka ba ni a ce Bahaushe ya rasa sunan da zai sa ma kaset sai irin su Zunubi, Siradi, Ruhi, Tawili, Ilhama, Ibtila'i, Siratsi.
Daga karshe furodusa/darakta ba na yi wannan don suka ko batawa ba, na yi ne domin jin ana ta ce-ce-ku-ce a kan mutuwar kasuwar finafinan Hausa. Idan kuwa da hali domin Allah sai a gyara, domin ganin hakarmu ta cimma ruwa.
Wata tunatarwa ta karshe, Allah ya jikan rai Tijjani Ibraheem wane mai kallo ko mai rubuto na mujalla da jaridu ya rubuta ya ki sa yaransa a fim, to don Allah a cire sa rai.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin