Free Web Hosting Provider - Web Hosting - E-commerce - High Speed Internet - Free Web Page
Search the Web

Jagorar mujallun Hausa
FITOWA TA 31   Yuli 2002
FITATTUN TAURARI


BABBAN SHAFI
RA'AYI
Zuwa Ga Masu Karatu
Wasiku
Balaraba Muhammad (1983-2002) 
Rahoton Musamman
Rahoto
Malam Zurke
Ra'ayin Mujallar Fim
Bukukuwa
Sauran Labarai
Fitattun Taurari
Dangane Da Mu
Muhawara a Zauren YAHOO!GROUPS

Wannan wani zaure ne da aka kirkira a dandalin sadarwa na zamani, wato intanet.
An gina zauren ne a kan tsarin 'Groups' na babbar masana'antar sadarwa ta intanet da ke Amerika din nan mai suna Yahoo!
A wannan zauren namu mutane suna tattaunawa ne musamman a kan finafinan bidiyo na Hausa wadanda ake yayin su yanzu.

JE KA TA NAN


Inda za ka samu tsaffin mujallun Fim
 
Je ka Bangon Fim ta 30
Bangon FIM ta 29
Bangon FIM ta 28
Bangon FIM ta 27
Tallar sabon fim din da ya fito!

NORTHERN STAR FILMS

KE GABATAR DA

GAGARABADAU Fostar fim din kenan

Shiryawa: MUJALLAR Fim

Darakta HAFIZU BELLO

Wasa: Sadiya Abdu Rano, Musbahu M. Ahmad, Sani Moda, Aliyu A. Gora, Hindatu Bashir, Isa Ja, A'isha Ibrahim, Mika'il Hassan 'Gidigo,' Baban Mulika, Shu'aibu 'Kumurci', Ashiru Bazanga, Saratu Gidado, Shehu Kano, Galin Money, d.s.

Labari/Tsarawa: Iro mamman;

Daukar Hoton Bidiyo: Yahaya Skito

BABU IRINSA!

Wasu matafiya ne Allah ya hada su tafiya a tsohuwar motar Direba Moda. Kowanensu yana da ra'ayin yadda ya kamata motar ta rika tafiya: wasu na kukan ana bata lokaci, wasu na cewa a rage gudu...

Can a kan hanya, yaran Gagarabadau (su Kumurci) sun tare hanya suna fashi...

Labari ne na soyayya, ban dariya, tada jijiyar wuya, da ban tsoro...

Idan har ka kalli fim din ba ka yi dariya ko ka ji taraddadin sharrin basawan Gagarabadau ba, to za mu biya ka kudinka! Ka tuntube mu ta e-mail dinmu don ka samu naka

 


Wasan kwaikwayo shiryawa ne - Umaru Bosso Minna

Daga NAZEEB SULAYMAN IBRAHIM a Minna

ALHAJI Umaru Bosso yana daga cikin manya kuma tsofaffin 'yan wasan kwaikwayo na Hausa. Sai dai ga alama, da yake ba a Kaduna ko Kano yake zaune ba, ba kowa ba ne ya san hakan. An haife shi shekaru 45 da suka wuce a unguwar Biri, cikin garin Minna, hedikwatar Jihar Neja.

Alhaji Umaru, wanda shi ne shugaban kungiyar wasan kwaikwayo ta 'Sabo-Da-kaza' da ke Minna, ya yi shekaru kamar 18 yana wasan kwaikwayo na dabe da kuma na gidajen rediyo. Ya faro ne da wasannin rediyo kai tsaye, sa'annan ya koma ga na dabe, sai kuma na talbijin. Daga cikin wasannin rediyo da ya yi, sun hada da wani fitaccen wasa mai suna "Magana Jari" (amma ba na littattafan marigayi Dr. Abubakar Imam ba), wanda wani furodusa na wancan lokacin mai suna Sa'idu Jibrin ya rika shiryawa. Daga nan sai wasan furodusa Mr. Dele Angulu mai suna "Kowa Ya Ki Ji" wanda ke tsokaci kan shaye-shayen muggan kwayoyi. A daidai wannan lokacin ne sabon janar manajan gidan talbijin na tarayya (NTA) da ke Minna, Alhaji Bello Sule, ya kirkiro wani sabon wasa mai suna "Suntumi". Duk wadannan, an yi su ne tsakanin 1994 zuwa 2000.

Alhaji Umaru Bosso yana da mace daya da 'ya'ya uku, Mohammed Kamal, Hamza da Habiba. Na tambaye shi ko zai amince 'ya'yansa su shiga harkar wasan kwaikwayo, musamman na bidiyo da ake yayi yanzu? Shugaban kungiyar ya kada baki ya ce, "Kwarai, kwarai. Ai sana'a ce da jahili ba ya yi sai mai ilimi. Dalili kuwa, duk mai harkar wasan kwaikwayo, Allah ya yi shi da hazaka da amfani da basirarsa. Saboda haka, wasan kwaikwayo yinsa karin basira ne da ilimin zaman duniya ga mai yinsa. Sa'annan duk mai yin wasan kwaikwayo yana shiryarwa ne kan tafarki mai kyau."

Da aka tambaye shi wasannin rediyo da talbijin da ya fi so, sai ya ce, "Hakika na rediyo na fi so, 'Kada Mai Gani Ya Taka Makaho', na talbijin kuma na fi son wasan 'Suntumi'."

Tsohon dan diramar ya yi wasannin bidiyo da dama amma guda daya ya fito kasuwa. Wasan shi ne wani mai suna Ta Haihu wanda ya fito a farkon wannan shekara kumar kungiyarsa ta 'Sabo-Da-Kaza' ta shirya. Shin ko Alhaji zai iya tuna wasu daga cikin abokan wasansa ma talbijin ko bidiyo/ sai ya ce yakan tuno kamar su Sani Sada, Abdullahi King, Balaraba Musa, Ja'afaru Danjuma Bakori da Kabiru Sa'idu.

Ta fuskar ci-gaban harkar fim din bidiyo, cewa ya yi, "Tun muna ji, har muka zo muna gani, ta fuskar kayan aiki kamar su kyamarar daukar hoto irin ta gida mai saukin kudi kamar M7, M10, M3500 zuwa ga manyan kyamarori irin su Betacam mai tsada ta miliyoyin nairori. Ta wannan fanni, an samu ci-gaba sosai. Hanya ta biyu kuwa ita ce ta fannin wakoki don nishadantarwa irin na finafinan Indiya wadanda da can ke debe mana kewa, yau na Hausa sun kore na Indiya warwas saboda kishin Hausa."

Alhaji Umaru ya ci gaba da cewa shi ya fi son ya zama babban mai ba da shawara ta fannin finafinai a arewacin Nijeriya, sa'annan ya yi nuni da irin tinkahon da yake yi da jiharsa ta Neja. A cewarsa, "Jihata ta Neja, na tabbatar za ta iya gogawa da kowace jiha a Arewa in dai ta harkar finafinai ne masu inganci da ma'ana da kuma fannin taka wasan shi kansa."

Na tunzuro shugaba Umaru Bosso inda na ce jiharsa ba ta da manyan furodusoshi masu rijista da uwar kungiyar furodusoshin arewa (AFPAN). Sai ya yi farat ya ce, "Idan ba ka san da su ba, to yau zan gaya maka cewar akwai guda biyu, daya a garin Suleja, daya a Minna. Babban abin bakin cikinmu a yau shi ne babu manyan furodusoshi da yawa a jiharmu, amma a halin yanzu, matasaN furodusoshi sun fara yunkurowa."

Umaru Bosso ya ba da shawarar cewar yana rokon furodusoshi da kamfanonin finafinai a nan Arewa su yi ta hakuri da juna. "Mu taru mu hada kai don kai ga gaci kamar sauran manyan kasashen duniya da tuni suka ci gaba kamar su Amerika, Japan, Indiya, Koriya, Sin, Faranshi, da sauransu."

A karshe ya kuma gode wa mujallar Fim saboda a cewarsa ta ba 'yan dirama na Jihar Neja damar fadin albarkacin bakinsu su ma. Ya ce ya dade yana karanta mujallar amma sau tari sai labaran 'yan fim na Kano, Zariya, da Kaduna kawai yake gani a ciki. Ya ce wannan wata dama ce ga 'yan Neja da su ba da tasu gudunmuwar don dukkan 'yan arewa su san da zamansu.

Komawa babban shafinmu           Komawa saman wannan shafin