Darakta ne yake da hakkin daukar 'yan wasa ba Furodusa ba
Wakilinmu ALIYU ABDULAHI GORA II ya sadu da sabon Furodusa mai tashe a Kaduna, Muhammad Awwal Inuwa, suka tattauna a kan yadda aikin ba da umurni yake da matsalolinsa.
IDAN ana maganar masu ba da umarni a finafinai mazauna Kaduna, to dole a sako Malam Muhammad Inuwa Auwal a ciki. Ba kuwa yawan finafinan da ya yi ya sa haka ba, a'a sai da kwarewar da ya nuna a kadan din da ya yi, musamman a fim din Hikayah.
Muhammad Inuwa Awwal
|
Auwal haifaffen Unguwar Kanawa ne a garin Kaduna. Iyayensa mutanen Kano ne. A Kaduna ya yi karatunsa na Muhammadiya da na boko, "har zuwa daidai gwargwadon abin da na samu daga karatun," inji shi.
Bayan karatu, Auwal ya ce ya yi "sana'a kala-kala," har dai ta kai ga ya komo ga shirya finafinan Hausa. "A halin yanzu, babbar dai sana'ar da muka sa a gaba ita ce shirya fim, muna darektin kuma muna shirya fim namu na kanmu a lokaci daya," inji daraktan.
Fim ta tambaye shi sana'ar da yake yi kafin ya shigo harkar fim. Inuwa ya amsa, "Kafin in shigo harkar fim, sana'ata ita ce muna shigowa da kaya daga Kotono, kamar su rediyo, TV, bidiyo, da dai sauransu. Muna kuma aikin daukar biki a bidiyo. Daga nan sai na samu kaina ina da ra'ayin shiga harkar shirya finafinan Hausa, na kuma shigo."
Inuwa ba yana nufin shirin fim ya fi waccan sana'ar da ya baro ba. "Wato shirin fim kamar sha'awa ne. Na taso tun ina karami ina mu'amala da wani sutudiyo, wato na Jama'atu Nasril Islam, wanda kawuna shi ne ainihin wanda yake kula da wurin. To tun ina karami na taso muna aiki da kyamara wajen daukar bukukuwa; kafin dai video camera ta yi yawa a gari, mun dade muna aiki da ita. Har yanzu ina da sha'awar irin wadannan ayyukan. To ka ga wannan al'amari ne wanda yake tafiya hannun da hannu da shirye-shiryen finafinan Hausa. Sai ya kasance sai na ji ina da ra'ayin shirin fim. Sai 'yan shekarun nan da yake finafinan Hausa sun fara karbuwa, kuma da ma can abin da nake so kenan a rayuwata. Sai ya kasance na shiga sana'ar."
Da ya shiga sana'ar, ya fara ne da zama furodusa na fara, ya shirya fim din nan mai suna Sara Da Sassaka. Malam Tijjani, wani wanda aka fi sani da T.J., wanda kuma yake zaune ne a unguwar Rigasa a Kaduna, shi ne ya ba da umarni a fim din. Duk da haka, a cewar Inuwa, "To amma ni ma na yi karambani na yi darektin wani bangare na fim din!" Bayan haka kuma yana nan har ya kasance ya gane yadda ake aikin ba da umarnin ma. "Ina iya darektin fim da kaina a yanzu." Shirin farko da ya ba da umarni da kansa baki dya shi ne Hikayah, inda ya nuna matukar kwarewa har wasu da suka ga wasu bangarori na fim din suke mamakin hazakar da aka nuna wajen shirya shi.
Inuwa ya kara da cewa tunda fa shi yanzu ya gane bakin zaren, a yanzu "zai yi wuya in dauko darakta, in dai ba ta kama dole ba. Saboda ko na dauko, aikinshi ba zai gamsar da ni ba."
Finafinan da ya yi ba su shiga kasuwa ba tukuna. Amma nan da dan lokaci kadan z a fara ganinsu. Inuwa ya bugi kirji ya ce, "Duk wanda ya kalle su, zai so ya san wanene daraktan."
Kada ka dauka Hikayah kadai Inuwa ya yi. Akwai wasu. ka ga dai akwai Hattara, wanda har an gama hada hotunansa. Sai kuma wani mai suna Huduba, wanda ake kan aikinsa a yanzu. "A halin yanzu ma akwai rubutattun fim a hannuna da dama wadanda ni zan yi aikinsu."
Akwai wata matsala da ta zame wa 'yan Kaduna alakakai. Wannan ko ita ce yadda yawancin furodusoshin garin na Gwamna suke tsallake daraktoci irin su Inuwa su je Kano su dauko darakta. Shin me zai ce a kan wannan? Inuwa: "Wato ni ina ganin ba wai sun raina mana ba ne. Yawancin furodusoshi, ka san ganin cewa mutane sun dade suna kallon finafinan Hausa wadanda suka fito daga Kano, to sai daraktocin Kano suka fi na Kaduna suna. To ganin haka sai furodusoshin na Kaduna suke ganin idan ba daga Kano suka dauko darakta ba, fim din ba zai yi kasuwa ba. To amma duk abin ba haka yake ba, a nan Kaduna muna da kwararrun daraktoci wadanda suka karanci abin, amma ba a kiransu."
Idan an lura, Inuwa dai ya hada abu biyu: furodusa ne kuma darekta. To shin wanne ne ya fi muhimmanci a wurinsa? Sai ya amsa: "Gaskiya daraktin fim ya fi zama mafi muhimmanci a wurina. Ka san in ba darakta, ba fim, komai kudin furodusa."
Wata matsala da daraktocinmu ke fuskanta ita ce yadda ake samun gardandami a tsakanin furodusa da darakta a kan wanda ya kamata ya dauki 'yan wasa a fim. Shin ya Inuwa yake ganin abin?
Inuwa: "To, yawanci a gaskiya mutane sukan sa son rai a wajen daukar 'yan wasa. Abin da ba na yi kenan. Ni ina ganin duk inda dan wasa ya dace a fim, to a sa shi a wajen, ba wani maganar 'yan'uwantaka ko abokantaka. Kuma darakta shi ke da hakkin daukar dan wasa, ba furodusa ba. Sai dai in ba gaskiya ake so ba."
Maganar wannan shi ne sai daraktoci su kafa kungiya inda za su rika tattauna al'amuran da suka shafe su. A Kano, akwai kungiyar daraktoci. To, mujallar Fim ta samu labarin cewa a Kaduna ana kokarin a kafa, har an yi tarurruka a kan hakan. Allah ya nuna mana.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin