SHUGABAN 'YAN WASA NA GARIN TAFA YA CE:
Mu zage damtse
DON INGANTA HARKAR FIM
Daga NAZEEB SULAYMAN IBRAHEEM a Tafa
SHEKARU 40 da suka shude, cikin garin Doguwa a Karamar Hukumar Doguwa a Jihar Kano, aka haifi gwani-na-gwanaye sarkin wasa na garin Tafa, Jihar Kaduna. E, mun san masu kallon fim ba su taba ganinsa a fim ba, to amma yawancin fitattun 'yan wasan jihohin Kano da Kaduna sun san shi. Su Ibro, Cinnaka, Yautai, Katakore da Danwanzan suna zuwa har Tafa (kan hanyar zuwa Abuja daga Kaduna) don su gan shi, wata sa'a ma su goga tare a fagen wasan dabe inda ya shahara.
Yusuf Musa, wanda aka fi sani da suna Karda (bakon dole!) ya shahara a fagen wasa iri daba-daban: dan fashi, barawo, kwarto, uba, tsoho, dan yaro, saurayi, likita, direba, wanzami, dan tauri, gyartai, magini, lebura mai kudi, dan daudu, talaka... kai duk abin da kake so, Karda ya iya. Sai me? Duk wani dan wasa a Arewa Karda ya riga shi cin ribar wasa, saboda ya samu jama'a da dimbin yawa fiye da wadda aka san shi a fim. Ya yi aure tun shekaru kamar 16 da kudin wasan dabe. Ya gina gida na kashin kansa ta hanyar wasa. Ya je kasashen Afrika ya yi wasan kudi, kuma ya kafa kungiyar wasan kwaikwayo ta kansa na farko shekaru 16 da suka wuce, shekarar da ya yi aure, a sabuwar garin Doguwa mai suna 'Alfijir Dramatic and Cultural Troupe'. Ya kafa kungiyar rawa ta koroso ta Jihar Kaduna da ke Tafa mai suna 'Sardauna Troupe', ya dinka masu kayayyakin rawa masu launi iri-iri.
Tambayoyi a nan su ne: shin wadanne nasarori suka rage wa wannan bawan Allah ya cimmawa a fagen fim? Shin ya taba zagawa a wani bangare a harkar take wasa? Ko ya taba shakka ko shayin wani dan wasa a harkar? Ko kuma ya taba satar wasan wani dan wasa a rayuwarsa? Wadannan tambayoyi ne da kuma wasunsu na yi wa gwanin wasa bakon dole Karda, a filin wasansu da ke Tafa:
Fim: Da ka zauna tare da kungiyar Alfijir shekaru 16 da suka wuce, daga nan fa sai ka doshi ina?
KARDA: Na dawo Kaduna garin gwamna inda na yi wasa da 'Marhaba Drama Club,' da ke Kasuwar Barci,' na kamar shekara hudu, daga nan sai na zo nan Tafa.
A matsayin me ka zo?
KARDA: A matsayin dan wasa kuma daya daga cikin shugabannin sabon kulob din Tafa, watau Sardauna. Ni da Muntaqa (Sarka) da Gwanda da Soko, da Isyaka Mohammed (Madubi) mu ne manyan jami'an kungiyar. Yanzu Sarka ya koma Kaduna can Marhaba yana tare da Dafe-Dafe. A halin yanzu, ni ke shugabancin kungiyar.
Ta ina kuke samun taimako don ci-gaban kungiyar?
KARDA: Daga Allah da jama'a. Da can, kamar shekaru uku da suka wuce, muna samun mafi yawan taimako daga wanda ya dauki nauyin kungiyar a wancan lokacin, wani attajiri mai suna Umar Faruk.
Yanzu ba ya taimakawa ne?
KARDA: E, to har yau dai yana tare da mu a matsayin mai kaunarmu a kullum. To sai dai ya karkata akalar harkokinsa ne zuwa Abuja da Ikko.
A ina ka koyi wasa ne tun farko a rayuwarka? Sa'annan za ka iya tuna wadanda suka fara koyar da kai wasa?
KARDA: Tabbatacce zan iya tuna wadanda suka fara koyar da ni wasa. Da farko dai na fara wasan dabe ne a garin Doguwa, karamar hukumata a Jihar Kano. Wadanda kuwa suka fara koya mani wasa babu kamar Malam Yakubu Liman, wanda a yanzu ma'aikaci ne a Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano; sai Malam Habihu wanda sakatare ne a Cibiyar Nazarin Tarihin Al'adun Gargajiya, watau 'History and Culture Bureau,' ta Jihar Kano a yanzu. To shi Malam Yakubu Liman, shi ne mutum na farko da ya koyar da ni wasa - yadda zan fuskanci kyamara, yadda zan amsa kiran wani daga waje, yadda zan daga murya don 'yan kallo su ji abin da nake fadi... kai, shi wannan bawan Allah kusan shi ne komai nawa na wasa a yau. Ina kara gode masa.
Malam Habibu kuwa shi ne ya sake yi mani tushi kan ilimin wasa a babban dandalin wasa na gwamnati da kuma yadda zan taka wasa don hoton kyamara na bidiyo. Shi ma ina kara gode masa. Wadannan mutane biyu ko a kwanan nan sun zo nan Tafa daya bayan daya don su gan ni su kuma ga ci-gabana a harkar kamar yadda suke jin labarina a wajen jama'a; sun zo sun jinjina mani bisa yadda na dora a kan yadda na faro tun lokacin da suka koyar da ni. Tunda har na samu daukaka, a cewarsu, za su rika aiko mani da takardar gayyatar yin wani wasa ko fim idan halin hakan ya taso.
Ka taba yin fim irin na finafinai yanzu?
KARDA: Na taba yi amma har yanzu ban gan su a kasuwa ba.
Menene dalili?
KARDA: To, mai yiwuwa ko furodusoshin ne ba su shirya fitar da su ba don wasu dalilansu.
Ko ka taba sha'awar wasan wasu?
KARDA: E. Ina sha'awar wasannin Bappa Cinnaka, Katakore, Danwanzan da Yautai.
Me ya sa ka fi sha'awar nasu wasan?
KARDA: Saboda su wadannan 'yan wasa sun iya sauraron mutum a wasa kafin su furta tasu maganr. Suna amfani da basirarsu kwarai wajen sigar wasa. Na sha yin wasannin dabe da su, saboda haka na san wannan. Suna da nitson karanto inda mutum ya nufa a wasa.
A mazan jiya fa, wanene gwarzonka?
KARDA: Kasimu Yero. Wannan mutum Allah ya ba shi basirar iya wasa. Yau ina son a ce na kai Kasimu Yero iya wasa ko ma har in fi shi. Kashimu Yero jangwarzo ne, haziki.
Akwai bambancin finafinan da da na yanzu?
KARDA: Sosai kuwa. Bambanci na farko shi ne mazan jiya sun fi mu da'a a ciki da wajen wasa. Na biyu, hazikan da gwanaye ne masu ilimin wasan fiye da na yanzu. Na uku, mazan jya suna yi ne don sha'awa da neman ci-gaban al'adunmu da addininmu, na yanzu kuma muna yi ne don neman kudi. Na hudu, finafinan yanzu sun samu ci-gaba wajen kayan aiki irin na zamani na fim ba kamar na zamanin mazan jiya ba. Na biyar, 'yan wasan yanzu ba su da hazaka sai rashin kunya da fitsara da girman kai da rashin sanin ilimi na makamar wasa; mazan jiya kuwa akwai karimci da kima da sanin ya-kamata da da'a da ladabi da biyayya ga na-gaba da su. Ya kamata 'yan yanzu su dauki darasi su yi hattara don koyo daga 'yan mazan jiya.
Akwai wata nasaba tsakanin finafinan Hausa, na Indiya da na kudancin Nijeriya?
KARDA: Akwai sosai. Ai babu ma hadi gaskiya. A finafinan Hausa ana gurbata al'adun Hausa matuka. Don a al'adar Hausa babu inda aka taba cewar yarinya da yaro ko budurwa da saurayi su tafi daji suna waka suna tikar rawa. Haram ne a ga mace da namiji hade suna kama hannun junansu, musamman idan haramiyoyin junansu ne, sai dai a ga mace tana nika ko daka tana waka a gida, shi kuma saurayi a nuno shi a daji ko a gida yana faskare, gini, noma, saka, yanta, rini, ko tufka, yana tasa wakar shi kadai. To ka ga a finafinan yau, duk wadannan babu su, sai fitsara da rashin kunya. Saboda haka mun yi haye ne kan al'adun kasashen Indiya da Turai. Su Indiyawa mai yiwuwa al'adarsu ce haka. Turawa ma al'adarsu ce rika mace a fim da rungumemeniya da sumbanta da ire-iren fasidanci. To amma mu ba al'adarmu ba ce. Addinin Musulunci ya yi hani nesa da irin wannan dabi'a.
Ina so in yi amfani da wannan dama don in yi kira ga Hukumar Tace Finafinai ta Kasa da ta hana irin wadannan finafinai fitowa har 'ya'yanmu da mu kanmu mu kalla. Wadannan dabi'u ne na Yahudu da Nasara, abin tir. Ban ki a ce samari su yi rawarsu su kadai ba, zunzurutunsu. Ba ni da ra'ayin a bar waka sai dai a yi ta ta hanyar da ta dace da al'adunmu. Ni ma nan zan iya rera waka in yi rawa bisa tsari da ka'ida tunda ni dan wasa ne. Mu Musulmi ne, kuma Musulunci ya yi hani da cudanyar maza da mata.
Akwai wani furodusa da ya gayyace ka kwanan nan don yin wani fim?
KARDA: Babu, amma ai ka san komai lokaci ne, ina jira. Don idan lokaci ya yi, za a bambance magirbin saran ciyawa da na yakuwa. Komai na Allah ne. Ni ba na zuwa wurin kowa don in yi barar a sa ni a wasa. A'a, ni ba bakon wasa ba ne. Kuma duk wani dan wasa a nan Arewa ya taho mu taka wasa a kasa mu gain.
Yau ka yi shekaru nawa kana wasa?
KARDA: Yau na yi kamar shekara 18 ina wasa.
Ka taba satar wasan wani?
KARDA: Sam sam! Na fi karfin satar wasan wani ko shi wanene a kasar nan.
Kana da aure?
KARDA: E, ina da aure. Mace daya da 'ya'ya hudu.
Shin akwai koma-baya a wasannin yanzu na bidiyo?
KARDA: To, koma-baya dai ita ce ta rashin lalumar 'yan wasa a waje; ina nufin a rika samun sababbin 'yan wasa, don wadanda ake yawanta sanya su 'yan kallo sun fara gajiya da su.
Menene shawararka a kan harkar?
KARDA: Lallai ina da shawara kuwa. Da farko kan 'yan wasa. Su rage girman kai. Dan wasa shi ya san sirrin dan wasa. Duk wanda ya karanta wannan bayanin ya san abin da nake nufi. Na biyu, furodusoshi su rika sanin wadanda za su taka masu wasa. Don wasu suna tattara 'ya'yansu ne da abokansu amma ba wai kwararru ba. Saboda haka, a bincika don inganta harkar. A shiga lungu-lungu, sako-sako a tono hazikan 'yan wasa. Akwai su da yawa, sai an bincika an yi watsi da son rai don ci da kasar nan gaba.
Na uku, kan kamfanonin finafinai. Ina ba da shawarar mu rika la'akari da finafinan Kudu mu dau sahu. Misali, irin harbe-harbe da ake yi a finafinansu. A ina suke samun bindigogin? Yaya ake yi suke harbi har bakin bindigoginsu su rika fidda wuta kamar harbin gaske? Wa ke koyar da su harbin? Yaya suke yi mota ta kama wuta ita kadai? Yaya suke yi a ga motoci sun yi karo gaba da gaba? Yaya suke dana bom ya tashi? Yaya suke yi a soki mutum da takobi a ciki ya fito ta bayansa? Yaya ake yi a ga ciwo ko jini a jikin wanda aka harba? Tambaya a nan ita ce: a ina suke samun bindigogin? Saye suke ko aro gwamnati ke ba su? Idan aro ne, mu ba za mu tambaya a ba mu ba ne? Idan ko ba za a ba mu ba, to menen dalili? Idan kuwa za a ba mu, me zai hana mu karba, jami'an soji ko 'yansanda su koya mana? Idan kuwa saye ake yi to mu ba mu da kudin saye ne? Ko kuma su gwamnati ta fi son su ne fiye da mu?
Saboda haka mu ma mu zake wajen zama teburin shawara don ci-gabanmu. Mu ma mu nemi taimakon gwamnati don mu samu gaggan kayan aiki. Dukkan dabarun nan, kamar fadowa daga bene amma mutum ya tashi garau, ko a tafi duniyar wata da kumbo, mu rika aiwatar da su a finafinai.
Karda, ga shi ka kure malejin iya wasa a nan gida amma mafi yawan masu kallo ba su san ka ba. Ta yaya za ka samu ci-gaba, sa'anannan me kake so zama a fagen fim kafin ka yi murabus?
KARDA: Lokaci ne kawai; idan Allah ya yarda za ku rika ganina a kai a kai nan ba da dadewa ba. Kuma a yau zan so a ce na zama babban furodusa in rika sakin finafinai masu ma'ana da inganci.
Ga wa za ka mika godiyarka kan nasarorin da ka samu a harkar har zuwa yau?
KARDA: Ga Allah (s.w.t.).
Muna yi maka fatan alheri.
KARDA: Na gode maku ni ma. Allah ya kara daukaka ku, amin.
Sababbin Finafinai: RUHI
Sabon Tsari Daga Darakta Hafizu Bello
AN dade ana ce-ce-ku-ce a kan alkiblar da ta dace finafinan Hausa su fuskanta a wannan karni na 21 miladiyya. Wasu na cewa a rika yin finafinai na gargajiya masu nuna rayuwar karkara, domin a ganinsu hakan ne ya dace da al'ada, wasu kuma na fadin a rika yin finafinai a kan rayuwar zamani tsantsa, wadda yawancin masu kallo suka fi ganewa - domin yawancisu a birane suke inda akwai na'urar bidiyo da akwatin talbijin. Wasu ma cewa suke yi a rika yin finafinai masu nuna wata rayuwa shigen almara, wato kamar zuwa duniyar wata.
To, duk dai akwai wadannan finafinan yanzu. Sai dai an lura daraktoci da dama sun ki yarda su sauya salon ba da umurninsu, ciki har da Hafizu Bello, wanda yana daga cikin wadanda ake ji da su a yanzu. An san Hafizu da yin finafinai na soyayya a tsakanin matasa da na zamantakewar iyalai, da kuma na gumurzu.
Ga alama Hafizu ya fara sauyawa, domin sabon fim dinsa mai suna Ruhi, wanda zai fito cikin wannan watan, sabon tsari ne a yadda aka san salon ba da umurni na daraktan. Domin kuwa shi ma ya bi sahun finafinai irin su Salma-Salma Duduf da Lawisa inda aka yi amfani da komfuta wajen lauya nau'in hoton bidiyo don nuna wata irin rayuwa wadda ba mu saba gani a finafinan Hausa ba.
A Ruhi, wata arniya ce, budurwa, mai suna Kindir (Zahara'u Shata), ta kamu da ciwon son wani saurayi wanda suke makaranta daya da shi mai suna Nasihu (Ali Nuhu). Duk da yake akwai yarinyar da Nasihu yake son ya aura, sai Kindir ta hada baki da wata tsohuwar majusiya ko (Hadiza Mohammed), suka karkato zuciyarsa ga Kindir. Ya zuwa lokacin da Nasihu ya juya wa Kindir baya ya auri yarinyar da iyayensa ke son ya aura, ita Kindir ta gaji tsafin tsohuwar nan lokacin da ta mutu. Don haka sai ta koma kan Nasihu don ta yi ramuwa kan abin da ya yi mata na cin amana. Shi kuma ya dogara ga karfin Allah. Don haka an kafa ginshikin tafka gwagwarmaya tsakanin tsafi da ikon Ubangiji kenan.
A fim din, babu waka ko daya, to amma mai kallo zai iya gama kallon bai ma san cewa babu wakar ba saboda yadda labarin zai rike tunaninsa.
An yi amfani da komfuta a wurare da dama don fitar da sakon da ake son a isar, kama tun daga lauya hotuna da fitar da sauti. Wakilin mujallar Fim da ya samu kallon fim din kafin ya fito ya bayyana cewa lallai fim din ya burge shi, kuma babu shakka sabon salo ne daga hazikin daraktan. Babu mamaki ganin yadda labarin yake, domin fitaccen marubucin nan Maje El-Hajeej Hotoro ne ya rubuta shi, wato wanda ya rubuta labaran finafinai irin su Sirrinsu da Juyayi.
Hafizu Bello ya fada wa Fim cewa shi dai ya yi wannan sabon salon ne domin harkar fim gaba daya tana bukatar sabuwar alkibla. "Sannan a duniya ana samun canji. Masu kallon finafinanmu kuma sun kure mu - da ka fara kallon fim, ka san inda zai kare," inji daraktan.
Burinsa a karshe, inji shi, shi ne furodusoshi da daraktoci su sauya yanayin fim dinsu. Ya ce duk da yake akwai bukatar ganin finafinai kala-kala, kada a tsaya a abu daya. "Ka ga Ruhi soyayya ce, amma ta zo da wani abu daban; ba soyayya ce ta a ce 'babana bai so ba' ko wani abu. Akwai bambanci," inji shi.
Ita ma jarumar shirin, Zahara'u Shata, ta fada wa wakilinmu cewa ta ji dadin saka ta da aka yi ta taka wannan rawar, domin za ta yi fice. "Amma ina so kada masu kallonmu su dauka ni arniya ce ko muguwa. Duk shiri ne fa!" inji ta.
A karshe ta ce ta kosa fim din ya fito, kuma ta tabbatar zai karbu ga masu kallo.
To, Allah ya sa.