AMINU Shehu Mirror yana daga cikin fitattun 'yan wasa daga Jihar Kaduna. Haifaffen Zariya kuma mazaunin birnin, ya yi fice ne tun daga fitowarsa a fim din da ya shirya da kansa mai suna Asali, wanda ya sa ake kiransa Aminu Asali. Ya fito a wasu finafinan da dama wadanda ya ce bai ma san adadinsu ba. Bugu da kari, Aminu furodusa ne wanda ya shirya finafinai guda hudu: Ibro Kansila Alhaji Malam Ibro, Tijara da kuma Asali. Akwai kuma wani da yake yi a yanzu mai suna Tattali.
Can kwanan baya, lokacin da shirin Asali 2 ya fito kasuwa, Aminu ya tayar da muhawara a tsakanin masu kallo game da wata rawar cashewa wadda ya sa a fim din, wato inda aka nuno Hadiza Kabara tana wata irin takawa tare da ambaton kalamai na batsa. Shin me ya sa Aminu ya shirya wannan rawar? Neman kasuwa ne ko kuma burgewa kurum? A cikin hirar da suka yi da wakilinmu ALIYU ABDULLAHI GORA II a Zariya, wannan wanzamin dan wasan ya kare kansa tare kuma da bayyana mana ko shi wanene. Bismilla:
FIM: Malam Aminu za mu so jin arnihin cikakken sunanka, tare da takaitaccen tarihinka.
AMINU: Assalamu alaikum. Ni dai ainihin sunana cikakke shi ne Aminu Shehu, amma an fi sanina da A.S. Mirror. Kuma an haife ni ne a unguwar Kusfa da ke cikin birnin Zariya. Sannan na yi karatun firamare dina a L.E.A. Kofar Gayan da ke Kusfa. Sannan kuma na yi karatun sakandare a 'Alhudahuda College,' Zaria. Sannan kuma na yi karatun Islamiyya a wajen Malam Sani ta nuna a Kusfa.
Wacce sana'a kake yi kafin ka shigo harkar fim?
AMINU: Kafin in shigo harkar fim, sana'ar da nake yi ita ce ta wanzanci. Don kakannin kakan Sarki Aliyu, zuwa Ibrahim, duk dai ainihin kakan kakanmu shi ne Makaman Aska na birnin Zariya, ni kuma tun ina da shekara goma na fara aski, kana har na iya kaciya da cire beli da sauransu. Kuma har a yanzu a cikinta nake. duk da nake harkar fim, ban saki wannan sana'a ba.
Yanzu ka kai shekara nawa da haihuwa?
AMINU: Shekaruna ashirin da biyar da haihuwa.
A wace shekara ka shigo harkar fim?
AMINU: Na shigo industiri a shekarar 1997. Amma ban fara fitowa a fim ba sai a 1999.
Wane bangare ka dauka lokacin da ka shigo industiri?
AMINU : Kafin dai in fara a matsayin dan wasa, sai da na iya rike kyamara, kana na fara fita a fim, sannan na zama furodusa, kuma nan gaba kadan ina sa ran zan zama darakta.
Me ya sa ake kiranka 'Mirror'?
AMINU: Ba a Turance na fara samun wannan suna ba. Wata kakata ce take kirana da 'Madubin Zamani'. To a haka sunan ya bi ni. Sai na juya shi zuwa Turaci, shi ne ake kirana haka.
Finafinai nawa ka fito a cikinsu ?
AMINU: suna da yawa, a gaskiya bazan iya gaya maka adadinsu ba.
Ka taba yin aure?
AMINU: A gaskiya ban yi aure ba, amma ina da niyya, kuma nan ba da dadewa ba in Allah ya so.
Menene ra'ayinka dangane da korafin da wasu ke yi cewa rawar da Hadiza Kabara ta yi a fim dinka Asali 2 ba ta dace ba?
AMINU: Ka san shi fim din Hausa ba al'adunmu ne kawai muke amfani da su ba. Mun aro wasu al'adu na ma kasasahen waje. Kuma shi ake yi, yake burge jama'a. To ni alhamdu lillahi,duk wanda ya yi magana, da alamar abin ya burge shi ne har ya fito ya yi magana a kai.
Kai a naka bangaren kana ganin wannan rawar ba ta saba wa Musulunci da al'adar Bahaushe ba?
AMINU : To ni dai gaskiya a nawa tunani ba ta saba ma addini ba; kuma in har ba ta saba wa addini ba, don ta saba wa al'ada bai kama a ce an samu wani ce-ce-ku-ce daga jama'a ba.
Wace irin tarbiyyar kake ganin irin wannan rawa za ta koya wa 'yan kallo?
AMINU: To ita dai wannan rawa ana yi ne saboda nishadi. To saboda haka in ko aka ce babu nishadi to sai dai in a cire rawar ma gaba daya, shi ne kawai mafita.
Me ya sa ka zabi a Hadiza ta yi rawa da kayan sojoji a fim din?
AMINU : Na ga za ta dace hakan ne, kuma za a samu abin da ake so.
Da ma a matsayin soja ta fito a shirin?
AMINU: Ba a matsayin soja ta fito ba, saboda dai a burge masu kallo ne sannan kuma a samu canji na irin kayan da aka saba gani a fim.
Wane irin shiri ka yi na tarbar kalubalen 'yan kallo a kan rawar?
AMINU : Gaskiya a shirye nake duk wanda ya zo da wata magana da ta shafi wannan rawa zan ba shi amsa. Ni dai na san bai saba wa addini ba, ita ma Musulma ce, da ta san ya saba wa addini da ba za ta yi ba.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin