WAI an kashe Macijiya an sare kanta ne? Idan ba haka ba, yaya muka dai jin duriyarta?"
Wannan tana daga cikin tambayoyin masu kallon fim da suka waiwayi mujallar Fim game da 'yar wasan nan mai suna A'isha Dauda, wato jarumar shirin Macijiya wadda aljana ce da ta kuntata wa rayuwar Sani Musa Danja bayan ya kashe mata 'ya a fim din. To, A'isha dai, ko kuma mu ce Macijiya kamar yadda wasu ke kiranta, tana nan da ranta, kuma ba ta bar fagen shirin fim ba. To yaya aka yi aka daina ganinta? Wannan tambayar ta sa wakilinmu SANI MOHAMMED MAIKATANGA ya binciko inda take, ya wurga mata tambayar. Amsar da ta ba shi ita ce aure za ta yi, shi ya sa ta daina yin fim.
Shin wai ma, wacece Macijiya?
"Da farko dai sunana A'isha Dauda kuma mahaifina Bafillatani ne. Asalinmu 'yan Adamawa ne. Babata ita ma yare ce, 'yar kabilar Margi." A haka 'yar wasan ta fara ba mu tarihinta. Ta ce an haife ta ne a cikin garin Kano. "A takaice, mun kai shekara talatin a inda muke zaune muna zaman lafiya, wato a unguwar Zangon Dakata. A can na taso, nai makarantar firamare dina a 'ECWA Primary School.' Sannan sakandare dina a Baba Alhamdu. Sai daga baya ne na yi sha'awar shiga harkar fim."
A cikin 1999 ne ta shiga harkar. Dalilinta shi ne ta ga ana fadakarwa ne, kuma "duk abin da ake fadakarwa wata rana zai iya zama gaske." Idan ka ji yadda A'isha Dauda ta shiga harkar fim sai abin ya ba ka mamaki. A cewarta, ita dai ba ta dalilin kowa ta shiga ba. Wai wata rana ne ta zo za ta wuce kan hanya kusa da dandalin matasa na Fagge, wurin da ake kira 'Welfare,' wanda matattarar 'yan fim ce, sai ta ga taro. Sai ta ce, "Me ake yi a nan?" Sai aka ce 'yan wasan kwaikwayo ne suka taru. Kawai sai ta kunna kai cikin zagayayyen gidan. "Da na shiga ina gani sai abin ya ban sha'awa; shi ne na shiga wannan kungiyar (wasan kwaikwayo ta) Janzaki," inji ta.
Tun da farko dai da sa'a yarinyar ta shiga harkar, domin har ta yi finafinai sun kai goma; wasu ma ba su fito ba har yanzu. Daga cikin wadanda ita ce jarumarsu akwai: Mukhtar, Macijiya, Kantafi da Matausaya.
An tambaye ta wane darasi take jin ta koya a harka fim? Sai ta amsa: "Iya zama da jama'a." To, tunda ta koyi wannan darasin, ko wani rashin jituwa ya taba hada ta rigima da wani? A'isha ta ce ba wanda ta taba yin rigima da shi. "Duk muna mutunci da su," inji ta.
To mu koma babbar tambaya. Me ya sa tun daga fim dinta na Macijiya, wanda 'Iyke Moore Investment' suka shirya, aka daina jin duriyarta a fagen shirin fim?
Ga amsar A'isha: "Aure zan yi kuma wanda zan aura ya ce in ina cikin harkar fim ba zan maida hankali wajen aurenmu ba, shi ya sa daga Macijiya na daina."
Masoyin na A'isha dai wani dan wasa mai suna Abubakar.
To wai da gaske dai ta daina fim kenan? Sai 'yar wasan ta kada baki ta ce: "Tunda ba a gama shirin auren ba, ko yanzu duk wanda ya yi kirana zan jein yi masa fim."
Af! To, ina masu son su sa A'isha a fim din su? Kun ji fa, har yanzu a kasuwa take!
Ko za ta dan tuno mana da wasu abubuwan da suka wakana a lokacin da suka je daukar shirin Macijiya. Misali, yaya ta ji da aka fara?
Aisha: "Gaskiya da na ga an fito da macizai (sai) na ji masifar tsoro."
A cewarta, da fari ma ba ita ce aka tsara za ta fito a yarinyar fim din ba. "Allah ne ya sa da muka je interview, bayan an yi mana interview (sai) aka ce ni na haye."
Wani abu da mai karatu bai sani ba game da Macijiya shi ne a yanzu haka ita 'yar rawar koroso ce a kungiyar wasannin gargajiya mai suna 'Tarauni Cultural Promotion and Dance.' To shi saurayinta bai yi magana kan wannan ba sai wasan kwaikwayo? 'Yar wasan ta ba mu amsa da kanta da ta ce, "Gaskiya tun kafin in fara harkar fim nake yin wannan, kuma mutane suna cewa ma wai na koma koroso na bar fim. Ba haka ba ne; sha'awa ce ta sa ni nake yi (koroson) saboda ba na iya zama a gida. Shi ya sa nake fitowa in yamma ta yi in zo in yi, in gaisa da abokan arziki sai in koma gida. Kuma (saurayina) bai san ina yi ba. Kuma ba rawa kawai nake yi ba har dirama ina yi."
Yaya take ganin ci-gaba a harkar fim kuma mecece shawararta ga 'yan fim masu yawan fadace-fadace?
A'isha tana da ra'ayi game da 'yan fim: "Gaskiya suna yin kokari wajen ciyar da harkar nan gaba. Allah ya taimaka. Sannan su kuma masu fada, su rika kai zuciya nesa, domin wata ran mu ne wata ran ba mu ne ba. Don Allah a hada kai!"
To A'isha Macijiya, Allah dai ya sa su yi aiki da wannan shawara da kika ba su. Fakat.
Komawa babban shafinmu  Komawa saman wannan shafin